Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma ya zuwan
addinin islama da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya labari
ya sha bambam.Ginshikokin al'adun hausawa na da mutukar zaranta,
kwarewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin
noma ita ce babbar sana'ar hausawa inda hausawa ke ma sana'ar
noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai
yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau
harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba
a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara
wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin
yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi
ne mafi girma da kuma mafi sanai'yar harshe a nahiyar Afirka,
harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci
kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa
al'adar cudeni-na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau
da kullum ga miliyoyin jama'a da ba hausawa bane a nahiyar Afirka.