TAKAITACCEN TARIHIN KABIRU USMAN FAGGE


An haifi Kabiru Usman Fagge ne a kano, kamar shekaru sittin da suka gabata, wato ran 12 ga watan Satumban shekarar 1946.
A shekarar 1956 ya shiga makarantar Firamare ta Fagge a kano, kuma a shekarar 1969 ya kamala karatun midil a Kuka Siniya, sannan ya wuce zuwa Kolejin Horas da Malamai ta Bichi inda ya shekara uku sannan ya kammala a Kolejin horas da malamai ta Kano, KTC a shekarar 1970, ya sami akardar shaidar koyarwa mai daraja ta biyu (Grade2).
Daga shekarar 1971-74 ya koyar a makarantar Firamare ta Tudun wadar birnin Kano, sannan ya koma karo karatu a Jami'ar Bayero, lokacin tana KarKashin (ABU). Bayan ya sami Digirinsa na farko a fannin Musulunci da tarihi, sai ya kama aiki a kamfanin wallafa Jaridun New Nigeria da Gaskiya Ta fi Kwabo.
Kabiru Usman Fagge, na daga cikin ma'aikatan farko da marigayi Audu Bako ya gayyato domin
bude gidan Telbijin na Kano-Bompoi a shekarar 1976. A shekarar 1986 NTA-Kano ta bada aronsa domin ayyukan wayar da kan Alhazai a hukumar Alhazan Nigeria (NPB) dake Ikko. sannan a shekarar 1989, Kabiru Usman Fagge ya kama aiki a gidan Rediyon Muryar murka(VOA) inda har yanzu yake aiki. Kabiru Usman fagge nada aure da 'ya'ya bakwai. Za'a iya aikawa Kabiru Usman Fagge da wasiia ta afagge@voahausa.com