Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Aruli Da Kida Da Wakokin Hausawa  


  Kida da waka na nuna halin rayuwar jama'ar da su makadan da mawakan ike tare dasu. Bambanci tsakanin waka da wake wato rubutacciyar waka ko kuma kamar yadda masana ke kiranta da sunan ARULI shine kida. Kayan kidan kansu suna nuna al'adun mutane. Hikimar dake kunshe cikin ARULI wake kan nuna himma da karawa mutane kuzari da kaimi wajen kara mmma kan abubuwan da suke gudanarwa. Wadansu waken kuwa wa'azi suke yi ga jama'a don bin tafarki wanda ya dace. Misali wakar marigayi Sa'adu Zungur wadda yayi kan bidi'a inda yake cewa:

Ka daura niyya a kan waka kana addu'a,
A'uzu Billah daga Shaidani a kan bidi'a.
San nan kawo Basmala bisa kan rikon sunna,
kabiya da yin Hamdala ita ce uwar sa'a.

Matsayin wake a kasar Hausa ya fara habaka ne a farkon karni na goma sha tara lokacin da Shehu Usmanu Dan Fodivo da kaninsa Abdullahi tare da dansa Muhammadu Bello suka himmatu wajen rubuce-rubuce don wayar da kan mabiyansu a jihadin da suke yi. Irin wakokin da suka yi suna nan a rubuce cikin littafm nan mai suna "Infaqul-Maisur". Wakokin kuma sune wadanda suka jibanci wa'azi, neman ilmi, ayyukan mulki da shari'a. Daya daga cikin irin wadannan wake akwai wadda tafi shahara wadda Abdullahi ya rubuta mai suna "wakar gode Allah" don nuna godiyarsa ga Allah madaukakin sarki da ya basu sa'ar yin hijira. Wadannan rubuce-rubuce sun yi sune cikin ajami. Daga baya, daya daga cikin 'ya'yan Shehu Usmanu Dan Fodiyo mai suna Isa ya yi kokarin fassara ayyukan Shehu daga larabci ko fillanci zuwa Hausa musamman ma wakokinsa na wa'azi, Tauhidi da Fiqhu.

Cikin karni na ashirin wato bayan Turawan mulkin mallaka sun mamaye kasar Hausa kuma karatun boko ya fara karbuwa sai aka rubuta wake da boko. A wancan lokacin, Sheikh Na'ibi Sulaiman Wall wanda a yanzu Alkalin kotun daukaka kara ta musulunci ne a Kano da kuma marigayi Ma'azu Hadeja wanda a wancan lokacin Malamin makaranta ne sun shahara wajen rubuta wakoki da Hausar boko, kuma sun fi maida hankali kan ilmi da addini. A bangaren wakokin da suka danganci mulki da siyasa kuwa, shahararrun marubuta da Hausar boko sun hada da marigayi Sa'adu Zungur, Mudi Sipikin, Akilu Aliyu da marigayi Malam Aminu Kano. Wani fannin ma bayan ilmi, siyasa da harkokin mulki sun rubuta wakoki da dama kan yakin basasar kasashen Hausa da yakin duniya na daya da na biyu. Haka kuma marigayi Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi ya rubuta waka kan ziyara mai tarihi da ya kai kasar Kano cikin 1914. Daga cikin mawakan Hausar boko na wannan zamani akwai Abubakar Ladan Zariya wanda ya shahara a wakarsa ta Africa da kuma wakar siyasa. Akwai kuma Awwalu Isa wanda yayi rawar gani a wakokin siyasar jumhuriyya ta biyu. Marigayi Yusuf Kantu ba kashin jefarwa bane a fannin wakokin Hausa.

A duk lokacin da aka yi magana kan al'ada cikin wannan littafin ana magana ne kan abubuwa biyu. Na farko dai akwai al'ada wadda addini bai yarda da ita ba. Idan ance addini a wannan littafin ana magana ne kan addinin Musulunci. Daga cikin al'adun da musulunci bai yarda da su ba akwai wadda ta shafi bautar wanin Allah wadda Maguzawa ke yi ta hanyar bori. 'Yan zamani kuma na hada bidi'a a harkokin aure, yin radin suna da jana'iza. Amma kuma akwai wadansu al'adunmu na gargajiya masu kyau da musulunci ya yarda da su. Irin wadannan al'adu na gargajiya kuwa sune irin na rayuwar yau da kullun kamar wadanda suka danganci cin abinci da hannu bayan an wanke hannun, yin aski don a rage gashi idan yayi yawa, sanya tufafi wadanda zasu rufe al'aurar mutun da ziyarar 'yan uwa. Wadannan basu saba ka'idojin addinin musulunci ba. Addinin musulunci kuwa shine addinin da bahaushe ya karba hannu bibbiyu. Don haka ashe wajibi ne ga hausawa su kara himmatuwa wajen ganin matasa sun yi watsi da al'adun nasara wadanda yanzu ke neman zame mana kadangaren bakin tulu.

Idan an lura za'a ga matasan mu sun watsar da aradunmu na gargajiya musamman wadanda suka danganci kida da waka sun rungumi na turawa, suna zaton yin haka shine burgewa. Ya kamata a rika tunawa da karin maganar nan ta hausawa dake cewa "kowa ya bar gida-gida ya barshi". Ba wai lallai bane mu dogara da kidan kotso, kalangu, Algaita da sauransu ba, muna iya inganta wadannan kayan kade-kaden da muke dasu na gargajiya don su dace da zamani ta yadda matasa zasu yi sha'awa. Ana iya sirkawa da kayan kida irin na zamani kamar yadda mawaka da makadan "yarabawa" keyi. Haka kuma idan aka dubi yadda makadan bakaken fatar America suka shahara a filin wakar zamani za'a ga cewa sun sami damar yin hakan ne ta hanyar sirka kayan kidan da kakanninsu wadanda aka kai America da sunan bayi suka tafi dasu daga nahiyar Africa. Yanzu haka dai bakaken fatar America sun shallake kowa a fllin kida da wakokin zamani a nahiyar turai. Don haka ya kamata tun daga makarantun farko da yaran hausawa ke zuwa na zamani, a fara koya masu muhimmancin kida da waka a al'adun hausawa.

Muhimmancin kowace aPumma shine tsare da kuma inganta al'adunta na gargajiya masu kyau. Barin al'ada tamkar barin wani ginshikin tubali ne na ginin halayyar jama'ar wannan al'umma. A yanzu haka a kasar Hausa an tashi tsaye don inganta al'adun hausawa domin kuwa tun kafin zuwan turawa an san cewa hauswa suna alfahari da al'adunsu musamman wadanda suka jibanci sutura da bukukuwa. Haka kuma an san hausawa da zumunci, misali lokacn aka yiwa wani rasuwa zaka gansu a wajen jana'iza da zaman makoki. Haka kuma idan haihuwa aka yi zaka ga jama'a sun taru a wajen radin suna don u.| dan uwansu murna. Idan kuma muka duba ayyukan gona za'a ga hadin kai wajen noman gayya. A halin yanzu kuma ga ayyukan gayya na gyaran gari jama'ar hausawa ke haduwa suna yi. Koda yake halin matsi na kudi ya tauye abubuwa masu yawa a kasashen Hausa amma duk da haka wasanninmu na gargajiya kamar lokacin salla karama da babba, ko sallar gani da kuma wasa kamun kifi na "Argungu" ana kokarin inganta su da kawatasu. Wani abin lura ma shine yadda yanzu aka tashi tsaye don inganta kayan kidan hauswa saboda su dace da zamani. Wadannan kayan kida wadanda suka hada da Gar Kalangu, Duman girke, Gangi, Dundufa, Shantu, Amada, Tandu da kidan bi duk sun sami karbuwa ga 'ya'yan zamani bayan kuwa a shekarun baya datta ne suka fi sha'awarsu. Haka kuma kidan goge, gurmi, kuntigi da Garaya yar sun sami wani sabon matsayi musamman idan aka dubi yadda kidan kukum tashe a yanzu


 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.