Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Bayani Kan Wakokin Mata 


  Yawancin mawakan Hausa kafin su fita filin waka ko wasa, su kan shirya wakar da zasu yi a gida domin tabbatarwa tare da yaransu wato masu amshin waka don kaucewa kuskure. Amma Alhaji Mamman Shata ya bambanta da sauran mawaka ta wannan fannin. Wakarsa zuwa take kamar mahaddacin waka ne, kuma wani abin mamaki shine da mai kada masa kalangu da su kansu 'yan amshinsa da zarar Alhaji Mamman Shata ya fara waka sai aji kida da amshi sun tafi tare da wakar. A lokacin da ya sauka a Daura kamar yadda ya nuna cikin wakarsa ta mai martaba sarkin Daura, bai tsaya yayi wani bincike a kan tarihin matar sarkin Dauran ba, abinda yayi kawai ya dan yi tunaninsa na tarihin da yaji kakanni na fadi sai ya fara waka. Daga karshe bayan ya kammala wakar mai dakin gabas babu wanda ya jawo hankalinsa da cewa yayi kuskure cikin abubuwan da ya bayyana game da ita. Da kuwa akwai kuskure da fadawan sarki ne zasu fara yin magana. Idan kuma aka dubi farkon wannan waka ta mai dakin gabas za'a ga cewa ya kirata da sunan mai dakin gabas bayan kuwa an san tana da suna. Dalilin da Alhaji Mamman Shata ya bayar shine bisa ga al'adar hausawa ladabi ne a boye sunan wanda ake jin kunya tun daga kan iyaye zuwa manyan kasa. Hikimar da yayi amfani da ita a nan ita ce, sai kawai ya nemi sanin bangaren da dakinta yake a cikin gidan sarkin Daura. Dakinta ne daga gabas don haka sai ya kirata mai dakin gabas. Kuma can wurin da yake cewa duk bafulatanin duniyar nan, ko na dawa zuwa nan birni, babanta ne ke mulki nai ya nuna ke nan tana da nasaba da sarauta, wato mai dakin gabas 'yar sarauta ce a kasar Nijer. A duk lokacin da Alhaji Mamman Shata ya je gidajen sarakuna don yayi waka, yawanci matan sarakunan ne ke bashi kayan mata da kudi masu yawa. Dalilin haka cikin wannan wakar yake cewa zashi wurin uwar dakinsa, mai raba riguna 'yar Iro. Alhaji Mamman Shata yayi wakokin mata masu yawan gaske kuma fitattu wadanda bamu tsara buga su a wannan littafi a yanzu ba sai a gaba. Wakokin sun hada da A'i kyaftin diyar nasara. Barira diyar
 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.