|
|
Bayani
Kan Bakandamiyar Shata
|
Mutane da yawa suna jin dadin kade-kade da wake-wake,
amma saboda hada addini da al'ada sai hakan ya zaina bidi'a
ta fuskar addinin Musulunci. Kida da waka na iya zama bidi'a
muddin maza da mata zasu hadu don su saurara. Yawaita habaici
da mawakan Hausawa keyi da wasu yaren ma kan haddasa fitina
a tsakanin mutane. Haka kuma mawaka kan daukaka mutumin da sukewa
waka har yaji kamar ya fi kowa a duniya, bayan kuwa sanin Musulmi
ne cewa babu wanda yafi wani a wurin Allah subhanahu wa ta'ala
im banda wanda ya fi tsoron Allah.
Haka al'amura suka rika tafiya har zuwa bayyanar Mujaddadi Shaihu
Usmanu Dan Fodiyo (Allah ya kara masa yarda) wanda a lokacinsa
ya yi hani ga yin wakoki da kade-kade. Duk da haka mujaddadi
Usmanu Dan Fodiyo bai hana yin wakar baka da wakar zube ba.
Shi da kansa ya rubuta wasu wakokm kamar yadda dansa Muhammadu
Bello ya rubuta kuma ya bayyana cikin (Inf'aq al-Maisur). Hana
yin wakoki da kida ta sigar bidi'a da mujaddadi Usmanu Dan Fodiyo
yayi ya karya zuciyar Hausawan dake sha'awar waka da kida, koda
ki cikin fulatanci ne. Gefe guda kuma Maguzawa wadanda ba Musulmi
ba a wai lokaci musamman a kasashen Hausa cikin Nijeriya, Niger
da Ghana, Kamar Saliyo, an sami wadanda suka fara yunkurowa
a filin kida da waka, kuma ba hadu da irin wancan hanin da aka
yi masu ba. A dalilin haka za'a ga Hausaw kasashen Ghana da
Niger sun kere na Nigeriya a filin waka da kida. Bayan akasarin
kasashen Africa sun sami 'yancin kansu daga 'yan mulkin mallaka
sami wani tashin gwauron zabin da mawaka da makadan hausa suka
yi, yari kuma cikin wannan yunkurin ake yi na yin gasa da sauran
kabilun Nijeriya filin waka da kida kuma ba za'a taba mantawa
da yunkurin farko da mariga; irin Narambada, Musa dabalo, Inu
Chaji, Mamman Sarkin taushi, Hamisu ft ganga, Mu'azu Dan alalo
suka yi ba, A yanzu kuma ana damawa da Alh. Mu, dan kwairo,
Sa'idu Faru a fannin kotso, su Alhaji Mamman shata Katsina a
kida da wakar kalangu, kuma liar yau tare da Alh. Mamman shata
ake dam; shi da kansa ya fadi haka cikin wadannan baitocin nasa
a wakar Bakandarr indayake cewa:
Mutane kowa yake addini
kun sanbaya kamar Manzon Allah.
Kowa ka gani na sabon Allah,
ko wanene ke kafirci
kun san babu kamar Fir'auna.
To, ashe haka duk wanda ke yin waka, yara bai yi kamar Shata
ba.
A duk lokacin da Alhaji Mamman Shata ya zuga kansa a wakarsa
ta Bakandamiya sai ya bada dalili, kuma ya nemi duk wanda bai
amince da hj ba yana iya fitowa filin waka a gwada a gani kamar
yadda yake cewa cikin wannan baitin kamar haka:
Idan kuma kayi musu sanya
Mu gani ko daga ina a yi wakar.
Alhaji Mamman Shata Katsina ya nuna tausayinsa ga marokan birni
da n; kauye masu yin kida da waka domin su sami na abinci, idan
kuma kidan y; masu kyau suyi auren zamani. Babu shakka Bakandamiyyar
Shata kalu-bale-ce ga duka maroka da makadan hausa. Yanzu kuma
bari mu leka muga abinda wakar Mai martaba Sarkin Zazzau Dr.
Alhaji Shaihu Idris ta kunsa.
|
|
|
|
|
|