|
|
Bayanin
Wakokin Direbobi
|
Domin tabbatar da cewa Alhaji Mamman Shata mawaki
ne na kowa da kowa ana ganewa cikin wannan waka ta biyu da ya
yiwa direbobi cewa ya kan kira wadansu mutane da sunan 'ya'yansa.
Yayi amfani da kalmar 'ya'ya ne don nuna amincewa. Ya amince
masu suma sun amince masa. Umaru Dan Danduna na Gwandu yana
daga cikin 'ya'yan shata na aminci. Shi kuwa Umaru Danduna marigayi
Danduna direba ne mahaifinsa. Marigayi Danduna Direba yayi zamani
da mashahuran direbobi dake bin hanyar Ikko kamar marigayi Dantanbuwal,
marigayi Jibo Dan mai mota, marigayi Alhaji Baba yaro na Audu
Bako, Habun Gyare, Mamuda Musa kataku, marigayi Mu'azu da Alhaji
baban kara da sauransu wadanda suka zauna a unguwar Fage dake
Kanon Dabo. Umarun Danduna tare suka yi yayi da Sarki Labaran.
Lokacin da Alhaji Mamman Shata ke yawonsa na waka a kasashen
hausa, duk lokacin da yaje Kano a gidan marigayi Jibo Dan mai
mota Allah ya jikansa yake sauka. Marigayi Jibo Dan mai mota
yana da 'ya'ya da yawa, amma a cikinsu akwai fitacce wanda ake
kira Ahmadu wanda abokin Umaru Danduna ne kuma makwabtan juna
ne a Fage. Dukansu biyu sun amince da Alhaji Mamman Shata kuma
sune yake aike a duk lokacin da yake Kano a gidan marigayi Jibo
Dan mai mota don suje su sayo masa kayan masarufi. Kasancewar
Alhaji Mamman Shata ya dade yana wakoki da yawa, rannan sai
ya tuna cewa ya kamata ya tuna 'ya'yansa, wannan shine dalilin
wakar Umarun Danduna wanda Shata ya dauka shine babba kuma yaji
dadin hulda da shi. Umaru Danduna yana da hakuri da karimci
kamar mahaifinsa bashi da ganganci a lokacin da yake tuka mota
kamar yadda mahaifinsa yayi ya gama lafiya kan haka ne Alhaji
Mamman shata yake cewa:
Ankararrawa jirgi zai tashi
mai sauka kayi sauri ka sauka,
mai shiga kayi sauri ka shiga
jirgi baya jiran uban wani.
|
|
|
|
|
|