Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wakar Direbobi 


 

(Amshin wannan waka shine)
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Umaru na Garba jikan Abdu Sadauki
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Wandara na Danbala Umaru na Gwandu
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Barkada faman badar na Jamma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Inadirebobin zamani?
ku saki jikinku ku mike kafafu,
kowane ya yi abinda yake so
Umaru ya tafi Nijer da Jamma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ya tafi Nijer Sanda Zarandami,
da ya tafi Nijer, ya tafi da Jamma;
ya barni birni ni da Kanawa.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Da ya tafi Nijer Umaru Gwandu,
sadda ka komo ka dauke Jamma
gun wa ka barni Umaru na Gwandu?
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ka san halin mutanen namu kanawan Dabo.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Su ko kanawa basu ganin kankantarka.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Umaru kanawa basu ganin kai yaro ne.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.

CHASHIYAR KALANGU:

Wandara na Garba jikan Audu Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ki gudu na Garba jikan Audu sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Bauna masha jini darzaza Sadauki dan Usmanu
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ya kwan da lafiya Umaru gidan Danduna
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ya tashi lafiya darzaza Sadauki dan Usmanu
Umaru dan Danduna na Gwandu.
Kwananka lafiya Umaru gidan Danduna
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ga mai jirgi, ga mai jirgi
ga mai mota Umarun Gwandu.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
A kimtsa kaya a gyara lodi,
fasinja kowa ya hau ya zauna
jirgi yazo tasha na-na Jamma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
A lafta kaya, a kimtsa lodi,
fasinja kowa ya shiga ya zauna
jirgi yazo tasha na -na Jamma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
An kararrawa jirgi zai tashi,
mai shiga kayi sauri ka fada
mai sauka kayi sauri ka sauka,
jirgi baya jiran uban wani.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Don haka Umaru bai dakata ma-ma kowa.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Allah ya jikan Danduna na Musher
Allah shi rayan Umaru da nai.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Allah ya jikan wandawa na Musher
Allah ka bar min Umaru da nai.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Da babu ran Danduna na Musher
basu ganin wandawa uba nai,
har Kanawa suke shigo ma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kai kuma kar ka sake Umaru kara shiri dan Mamman.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Barka da faman badar na Jamma.
Umaru Dan danduna na Gwandu.
Wandara na Garba jikan Audu Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kai tsaya dai mu wasa dutse wasu suji haushi.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Dakata dai mu koda dutse wasu suji haushi.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Mu wasa dutse mu muji dadi,
mu kula dutse su suji haushi.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Barka da rana, barka da fama
barka da yakin badar Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Arna suna fadin ga Umaru nan ya danno dan Usmanu.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kura mabi dare Umarun gidan Danduna.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kashi mai bugun kashi darzaza Sadauki dan Usmanu.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Amale mai kwarjini da kaya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Sai sun ga hanya ta lalace
sun duba daji yayi dameji,
kai xas,u. tur a. Sanda k.a doibo.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ba wani tsoro, ba wata shakka
ayi masa lodi Sanda ya rugo.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Idan yabi 'yan yara subi bay a.
Jmaru Dan Danduna na Gwattdu*
Jirgi ya nike hanyar maza kubi baya.
Umaru Dan danduna na Gwandu.
Giwa ta tsare icen maza kubi baya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
'Yan tan ashirin da biyar kubi baya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Giwa ta karya icen Sanda Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Gurnanin Damisa Sadauki,
wanda kare kegudu na Jamma.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ga giwa nan kwance a sarari
sai mai kiwo suke harara.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Umaru ne gashi nan a sarari
sai mai waka suke harara.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
In dan Umar gashi a fili
Shatan me Sanda Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.

CHASHIYAR KALANGU:

Na tafi Badar Sadauki
wanda yayi masa hassada yana ji.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Na sauka kwanni yawo ya kai ni,
sai gajikan Audu da jirgi.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Yara suna fadin ga Umaru can
ya taho dajirgi.
Umaru dan danduna na Gwandu.
Barka da faman dawa da birni.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Barka da yakin badar da arna.
Umaru Dan Danduna na Gwandu
Masha kwarauniya Umarun Sanda.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Masha hayaniyar duniya Umaru jikan Audu
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ina ‘yan kiya-kiya bodin katako?
Umaru wannan babu ruwa nai.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Shi Umaru don tsananin gatanci
mai tafiyar Mesa aka bida mai.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kaga mota kanta dabam bayanta daban can.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Ka ganta gabanta mota baya kuwa jirgi.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Jirgin ruwa tsaya a dada ma kaya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Um-um Kanawa Umaru ne fa.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Kun san halin uba nai- Umaru kun san
halinshi Umar Sanda Sadauki.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Gama direbobin tun da can
sun san akwai Danduna a birni.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Su kuwa direbobin zamani
sun san kana nan Umaru Gwandu.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
In don direbobin zamani
zari sanda shiga bugun abinka,
dau gora tittiki abinka kisan
biri bai kai ga igwa ba.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Uwar raggo muka yiwa jaje
ga danki can an wuce shi baya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Tsaya iya, ga danki can mun wuce a hanya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.
Matar raggo aka yiwa jaje
mijinki ne an baro shi baya.
Umaru Dan Danduna na Gwandu.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.