|
Akwai wakoki da yawa wadanda Alhaji Marnman Shata yayi don kansa
ba are da an bashi kudi ba. Akwai na kishin kasa kamar wadda
yayi ta 'yan arewa ku bar barci Nigeriar mu akwai dadi. Akwai
ta kowa ya shiga dajin rugu da wadda ya yiwa kogin Bahar Maliya
da wakar gargajiya da kuma wadda ya nuna lankwasa harshen Hausa
a wakarsa ta " ayaure duniya labari". Yana daya daga
cikin tsarin hikimarsa ta waka wajen jeranta kalangu da wakarsa
wanda hakan ke taimaka masa ganewa a duk lokacin da makadinsa
ya dan yi kuskure sai ya gyara ta hanyar kwalmada wakar da zata
dace da kidan don hana mai saurare gane kuskuren da wuri. Idan
kuma aka dubi wakar dajin rugu za'a ga yadda Alhaji Mamman Shata
ke kamanta halayyar zaman duniya da ta namun daji. Akawi kuma
wakar nomadonjan hankali jama'a su koma ga aikin noma don cida
kansu da kasa baki daya.
Cikin wakarsa ta 'yan Arewa ku bar barci, hikimar da ya nuna
a wakar tasa mafi yawa daga cikin mutanen Arewa suka fara ajiye
kudinsu a Bankuna. Hikimar dake tattare cikin wakokin Alhaji
Mamman Shata sai an natsu sosai za'a zakulo su saboda lankwasar
da yake yiwa luggar Hausa don ta dace da zamanin da ake ciki.
Yana kuma amfani da kalmomin Hausa masu saukin fahimta. Idan
aka dubi tsarin wakokin Alhaji Mamman Shata wadanda suka kusanci
jinin sarauta, za'a ga ba kamar sauran makada da mawakan Fada
bane domin Alhaji Mamman Shata bai ta'allaka kan wani Sarki
guda kamar yadda marigayi Narambada makadin Sarkin Gobir Isa
da sarkin taushin Sarkin Katsina da Jankidi, makadin Sarkin
Musulmi da Marigayi Abdul-Rahaman sarkin kotson Sarkin Kano
wanda shima ya gaji marigayi Alhaji Musa Dabalo. Alhaji Mamman
Shata, kamar yadda yake cewa ne cikin wakarsa ta Bakandamiya:
Fadawa mutane na kowa
ya rasa Shata yayi asarar waka,
ko wanene kuma ko dan wa.
Wannan ya nuna ke nan Alhaji Mamman Shata mawakin Hausa ne
na kowa da kowa duk da cewa bai gaji kida da waka ba idan
aka dubi jerin wakokinsa za'a ga ya dara wadanda suka gaji
kida da waka. A lokaci guda idan ta raya masa ko aka shaida
masa abinda zai yiwa waka sai kawai ya fara kuma mai kalangu
da 'yam amshinsa su tafi tare kamar yadda ake bukata.
Alhaji Mamman Shata bai bar ma'aikatan Gwamnati a baya ba
domin ya yiwa Alhaji Sa'idu Barda da Abdu V.I.O. wakoki, ga
kuma wakar da ya yiwa Mamman da da wadda ya yiwa marigayi
Kanal Abba Siri-Siri da marigayi Sani Audi Katsina. A Bangaren
attajirai banda wakokin da aka tsara a wannan littafi, akwai
wadda kuma ya yiwa marigayi Alhaji Haruna Kassim Ringim wanda
shi ya fara kai Alhaji Mamman Shata aikin Hajji. Ana iya samun
tabbacin haka cikin wadannan baitocin dake cewa:
Rannan na da wo daga tashe birni
sai Haru yace kai makadi aje
'yarganganrka, kazo na kaika
ka gano dakin Allah.
Sauran attajiran da Alhaji Mamman Shata ya yiwa waka sun
hada da Alhaji Ali Kotoko da Alhaji Bukar Mandara dukkansu
dake zaune a jihar Barnon Nijeriya. Babu shakka idan aka dubi
tsarin wakokin da Alhaji Mamman Shata yayi da wadanda sauran
mawakan fada suke yi, za;a gane cewa wakokin Alhaji Mamman
Shata sun zama sune a gaba kuma wadanda keda saukin samu a
kowane lokaci.Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin janar
Olusegun Obasanjo mai ritaya ta baiwa Alhaji Mamman Shata
lambar girma cikin shekara ta 1976. Jamrar Ahmadu Bello ta
Zariya ita ma ta bashi lambar girma shi yasa ake yi masa lakani
da Dokta Mamman Shata Katsina.
Dangantaka tsakanin Alhaji Mamman Shata da sauran mawaka a
wani gefen tana da danko amma mafi yawa saboda hassada mawakan
Hausa basa kaunarsa. Dalili ke nan a wakarsa ta Bakandamiya
yake cewa:
Goge da Molo wargin yara ne
su sami abinci suyi shakwara suyi jamfa,
idan sun sami kudi suyi auren zamani.
Daga cikin mawakan Hausa, marigayi Alhaji dan Anace yafi
yin farat-farat da Alhaji Mamman Shata duk da cewa shima ya
sami kishiya a filin wakar Dambe. Alhaji Mammman Shata baya
barin sai ta kwana. idan anyi masa abu nan da nan yake kokarin
ramawa ko ya bayyana ra'ayinsa na kin abin. Alal misali idan
aka dubi bayanin da ya yi a lokacin da Sarauniyar Ingila ta
ziyarci Nijeriya a zamanin marigayi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan
Sakkwato Allah ya jikansa. An gayyato A'ishat Fallatiyya daga
Sudan don yin waka, ganin haka sai Alhaji Mamman Shata ya
rera wakar dake nuna kishi inda yake cewa:
A gaya maka Ahmadu jikan Shehu
taura biyu bata tauno koda kuwa,
a bakin kura ne.
|
|