Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wakar Matar Sarkin daura Mai Dakin Gabas 


  AMSHI: MAI DAKIN GABAS 'YAR IRQ

Duk bafulatanin duniyar
nan ko na dawa zuwa nan birni,
babanki ne yake mulki nai.
Mai dakin gabas'yar Iro.
Balle kuma 'yan fulanin Nijer.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Kai yara kaka-tsara-kaka
zani wurin uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Mai raba riguna 'yar Iro
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Yaro yi kidan uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro
Yara zani birnin Daura
don in gano uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Rannan sai na sauka a Daura
nan na ishe uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Nan a gidan Bashar mai Daura.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Ta ce ga riguna nan Shata,
kana ta bada dawaki tayi
kyauta cikin fillanci tace
ga saniya kayi tatsa.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Ni dai bani kukan kurdi
sannan bani kukan yunwa,
mai dakin gabas na zaune.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Mu sheke ayarmu birnin Daura
mu kwana kida muna yin waka,
mai dakin gabas na zaune.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Sannan ga Bashar mai Daura.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
In ci abinci ga kurdi
nan ga sutura aba ni dawaki,
mai dakin gabas ke zaune
sannan ga Bashar mai Daura.
Mai dakin gabas 'yar Iro
Diyar Sarkin fulanin Nijer.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Allah kai ni birnin Daura
don in gano uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Kai yara za ni birnin Daura
don Shata uwa tai na can.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Mamman Shata uwata na can
sannan har ubana na can.
Mai dakin gabas'yar Iro.
Ga mai dakin gabas 'yar Iro
sannan ga Bashar mai Daura.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Matar garnakakin maza dan Iro
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Ga matar kutunkun bauna
Mamman Bashar mai Daura.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Allah Kai ni birnin Daura
don na ishe uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Yara in je na gano uwar dakina.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Mai kyauta ta bada dawaki
har saniya ayi tatsa.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Tafiyarmu Kaduna birnin Gwamnati
rannan ta bani mota kyauta.
Mai dakin gabas 'yar Iro.
Tafiyarmu Kaduna birnin Gwamnati
rannan ta bani Fijo kyauta.
Mai dakin gabas 'yar Iro.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.