Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wakar Sarki Labaran na kano  


  AMSHI: Sarki Mijin 'yar Sarki Labaran.

To Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Dodo mijin ;yar gata Labaran.
Sarki mijin'yar Sarki Labaran.
A Kano yake ba kauye yake ba.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Wayyo Sarkin Kanon 'yan mota Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Da haka nan nake ban iya waka ba '
da nayi karen motar Labaran.
Sarki mijin'yar Sarki Labaran.
Sai ya sakani a baya ya kai ni Ikko.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Mm, ya bani abinci ya min taguwa.
Sarki mijin'yar Sarki Labaran.
Im mun sami kudi kuma muyi shagali.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Karkadan mai namijin karfi
sannu bindiga mai dadin sababi.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Mutum na daga kwance yana sababi.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Wannan sai bindiga mai dadin sababi.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Ashe dan Alhaji ne mijin Hajiya
Dan Alhajiya jikan hajiya,
Sarkin Kanon 'yan mota Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
A ranar mutuwar goggon Labaran
ranar rasuwar innar Labaran,
dangi suka taru suna addu'a
Allahu Akbar, Allahu Akbar
Allah ya jikan goggon Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Niko nace masu amin tare da mu.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Ya Allah y a jikan baban Labaran
Allah ya jikan goggon Labaran,
don har sun mutu bai saba masu ba.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Dodo mijin 'yar Sarki Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
Dai kana kuma mata tai Hajiya.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.
A ran nan a Ilori aka yi kwamba
ga kura baya tana a gaba,
nace masu wanene a gaba?
Suka ce mani Sarki ne Labaran.
Sarki mijin 'yar Sarki Labaran.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.