Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wakar Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashir 


 

Amshin wannan waka shi ne (Mamman jikan Audu)


A lokacin da aka yi hira da Alhaji Mamman shata a gidajen rediyo c Telbijin a Nigeria da Amirka, an tambayeshi wace waka yafi so a ra sai yace wakoki biyu. Bakandamiya da wakar bashar Sarkin daura Amma duk da haka bai yi wannan waka ta »arkin Daura da tsaho 1 wadda kuma a jerin wannan littafi ita ce ta farko. Rashin tsahon ws waka ta farko ya faru ne saboda ganin cewa Alhaji Mamman Shata riga ya wake Alhaji Muhammadu Bashar lokacin da yake Wamban Bari mu duba wakar da ya yiwa Sarkin daura tarfarko.


Mamman Jikan Audu.
Mahmman dan Mamuda
Mamman Jikan Audu.
Giwa ikon Allah, Mamman kogi ikon Allah
giwa bukkar daji.
Mamman Jikan Audu.
Kogi ikon Allah
Mamman Jikan Audu.
Mamman kogi ikon Allah.
Mamman Jikan Audu.
Yara daji ya kai daji
daga giwa sai lya 'yanta
sai Zaki ke yawo, sai 'ya'yan kyar-kyece.
MAMMAN JIKAN AUDU.
Daura birnin Mamman
daga zaki sai 'ya 'yan kyar-kyace.
Mamman Jikan Audu.
Mamman ayi a gama sai doki.
Mamman jikan Audu.
Kai manya-manya inji kanana
jure fari sai tofa- wuyar wuta sai karfe,
ayi a gama sai doki, ga wata rigima ba
mai maganinta sai dai Allah.
Mamman Jikan Audu.
Ga wani rikicin ba mai
warware shi sai dai Allah.
Mamman Jikan Audu.
Mamman ayi a gama sai doki.
Mamman jikan Audu.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.