Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wakar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris 


  Wannan waka an yita ne ranar shagalin nada Mai martaba Sarkin Zazzai; Alhaji Dr. Shehu Idris a birnin Zazzau. Akwai wasu hikimomin waka da A Mamman Shata yayi amfani dasu cikin wannan waka ta Mai martaba Sar Zazzau. Yanzu misali idan aka tambayi mai karatu ko me Shata ke nufi da da yawa aka baiwa doki, ruwa kadan sai dai mai dokin? Haka kuma zai yi mu gano abinda Shata ke nufi da "kaji jika jiko gogarmar Sambo?


Alhaji Sarkin Zazzu Shehu
Gwauron giwa mai ban tsoro na Garba jikan Malam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Tausa a sannu Shata ne ke waka.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Kidan kutunkun Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Baba kai aka tsoro na Garba banda ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
In- kai aka tsoro wa aka tsoro na Garba banda ikon Allah?
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Amalen Sarakuna dan Malam Mamman.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Na Garba jikan Malam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Toron giwa mai ban tsoro na Garba jikan Malam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Wandara maki-sake dan Mallam Mamman
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ki-gudu na Zazzau giwa ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mani na Garba giwa ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Baban Jakadiya bargon mai fada
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ka duba cikar Zazzau birninta
birninta zuwa kuma kauye,
kauyen kuma har can daji
Allah Sarki wanda ya yita,
ya kammalasu- ya- tattarasu
ya baiwa Mani wannan yaron.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
A'a ya baiwa Mani wannan yaron.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
In kai kuma gasu amanar Allah
rikesu jikan Malam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Maki-gudu giwa ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Yara inji kidan dan Malam Sambo.
K A L A N G U-KALANGU.
Kunji tambarin dan Mallam Mamman.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Da farko zamanin kakanni,
sun ce Zazzau mafarin Gwari
yanzu ko birnin Malam Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Tun da farko zamanin kakanni sun ce
Zazzau mafarin gwari,
yanzu ko birnin Mallam Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Yanzu kuwa Zariya birnin Mallam Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
A'a Zage-zagi wa ab-babbansu?
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Tambayo mani Zage-zagi wa ab-babbansu?
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Suka ce Mani Sarkin Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ashe kun yarda da ikon Allah
kun ce Mani ab-babbanku.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mugun Madanbanci dan Mallam-Mamm-aha.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
A'a Zage-zagi wa ab-babbansu?
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Tambayo mani Zage-zagi wa ab-babbansu?
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Suka ce Mani Sarkin Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ashe kun yarda da ikon Allah kun ce Mani ab babbanku.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mugun Madanbanci dan Mallam-Mamm-aha.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Kada tamburan giwa dan Malam Mamman.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mani mai kasada dan Malam Mamman.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mai tafiyar nasara dan Mamman
na Garbajikan Mallam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Haba mai tafiyar nasara dan Mamman
na Garbajikan Mallam Sambo.
Alhtxji Sarkin Zazzau Shehu.
Kajijika-jiko gogarmar Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Wannan dan Katsinawa ya kasaita.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Wannan dan Katsinawa ya gawurta.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Dubi yanzu shi ke mulkin Zazzau.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Duk wani bazazzagi shi ne babbanshi.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Gwauron giwa mai ban tsoro na
Garbajikan Mallam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Kai da garaje, kaki garaje
na Garba ikon Allah, aha.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Daina sakewa gwauron giwa,
na Garba jikan Mallam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Giwa kin wuce kaho wane mai tarko.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Na Garba giwa ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Su Shehu kwasau na gode mai
saboda jikan Mallam Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Fadawa Saidu lya na gode
saboda sarkin Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Cewa Fagacin Zazzau na gode
saboda sarkin Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Dallatun Zazzau na gode
saboda sarkin Zazzau Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Sun mani saboda giwa ikon Allah.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Tsaya bani shan ruwa in huje butar.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Duk wadda ni kai kan gaggawa
Alhaji bani wuce fadar Zazzau.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Shata na Yalwa bai wuce fadar Zazzau.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ni dai na san kiwon kaza ta koshi
ta cika dan tumbinta.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu
Ruwa da yawa aka bai wa doki
ruwa kadan sai dai mai dokin.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Shehu ruwa da yawa aka baiwa doki
in yai kadan sai dai mai dokin.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Mani ruwa kadan sai dai mai doki.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Shehu na Ahmadu bakon turai
na Garba jikan Mallam sambo
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ranar ba da sandar sarki
Zage-zagi sun ban mamaki.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ga bakon Sakkwato birni
bakon Katsinawan Dikko,
bakonku Kanawan Dabo
Garba kuwa har Baucin Yakubu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Har na Yola sun san Malam Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Har na Gwambe sun san jikan Sambo.
Alhaji sarkin Zazzau Shehu.
A'a Jakadiya Zauna bari kuka
Aminu ne na nan bai kau ba.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
To tsaya in Aminu ya kau an bashe shi.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu
Sarkin rikon Amana jikan Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Ina masu waka da habaici
masu roko da zage-zage?
A uku wa zaku ma habaicin?
Mallawa dai dangi nai ne
Barebari kuma dangi nai ne;
to bare Katsinawa kakanninsa.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Don haka ba'a habaici fadar Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Duk wanda ya yi waka da habaici
ko yayi roko da zage-zage;
yanzu wawa ya doke shi.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Wawa tashi buga mar gorar taka.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Muje mana ba'a habaici fadar Shehu.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.
Taka lafiya Sarki jikan Sambo.
Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.