|
Alhaji Mamman shata ya fada da bakinsa cewar mahaiflnsa
wanda bai ayyana sunansa ba yana da 'ya'ya uku. Biyu maza, mace
guda. Sunan macen line Yalwa wadda kanwa ce ga Alhaji mamman
shata, a dalilin haka ne yasa ke masa kirari da cewa shatan
Yalwa kwana wasa. A lokacin da Alhaji [amman shata ke yaro ya
saba da ya tashi da sassafe ya kora shanunsa zuwa iwo, wani
lokaci tare da abokansa. Asalinsa bafulatani ne wanda iyayensa
ika sanya shi a makarantar allo don ya koyi karatun Alkur'ani
mai tsarki tun ana da shekaru biyar da haihuwa a duniya. Malam
Ahmadu ne Malaminsa na irko. Bayan ya fara sanin baki sai ya
koma wajen Malam Imamu dan Alhaji audu. Ya kuma yi karatu wajen
Malam Ali. Alhaji Mamman shata yace babu Dinda yaki jini a lokacin
da yake makarantar allo kamar kururuwar 'yan akaranta da ake
kira kolaye musamman cikin dare lokacin da 'yan ci rani kan
ira wuta domin yin tilawa ko kuma a kiskadi.
Alhaji Mamman shata bai tsaya ya sauke Al-kur'ani ba ya fada
sana'ar saida >ro. Amma kafrn ya bar makarantar allo saida
ya sami na tsarki da salla. Bai u bada cikakken bayanin dalilin
da yasa ya tsere daga makarantar allo ba. akar Asauwara ce
wakar da take tashe cikin 1936 lokacin da Alhaji Mamman tata
ya fara kwankwasa kofar film waka. Ga abinda yake cewa cikin
wakarsa
Bakandamiya:
irarin waka bai san tsoro ba na fito shata ne, ya san ku,
in san shi, sai kaka?
Malam Ya'u babban yaron Alhaji Mamman shata ya tabbatar da
cewa ita wannan waka ta Asauwara Shata ne ya fara amma ba'a
samu a gutsurata cikin wannan littafin ba saboda rashin sanin
tabbacin wanda ya kirkirota. Amma ance masana tarihin al'adun
hausawa yanzu sun dukufa wajen samo ainihin tarihin wannan
waka. A kashi na biyu na wannan littafi za'a bayyana sakamakon
binciken masana tarihi kan wakar Asauwara. uaga cik.ui da
Alhaji Mamman shata ya fara zama akwai Malunfashi da Bakori.
Daga Bakori ne ya wuce zuwa Kano. Bayan ya dan shakata a Kano
sai ya koma gida Musawa dake jihar Katsina ta yanzu. Da ya
sake fitowa a karo na biyu sai ya yada zango a Funtuwa, sannan
ya zarce zuwa Kano. A kasashen waje kuwa, Alhaji Mamman shata
ya ziyarci Abija ta kasar Ivory Coast, ya kuma je Makka1 inda
ya sauke farali na aikin Hajji. Alhaji Mamman shata bai manta
da yawon duniyar da yayi na kasashen yammacin Africa ba domin
ya bayyana duk wuraren da yaje cikin wakarsa ta duniya mafarki
ne Alhaji Shata.
|
|