Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

M S Hashim Gumel 


 
An haifeni a cikin garin Gumel, a ran 05 ga watan march , 1953, nayi makaranta primary a Gumel Zango primary school, daga 1960 zuwa 1967 daga nan na tafi babbar makarantar sakandare wadda ake kira da sunan Kano Educational Development Center KEDC daga 1968 zuwa 1971.
Bayan gama karatu na KEDC na kama aiki da ma'aitar ilimi ta karamar hukumar Gumel, wanda aka tura ni zuwa wani kauye da ake kira Galadi. A wannan kauyen nayi aiki a matsayin malamin makaranta na shekara daya. Daga nan sai akayi min taransifa zuwa Maigatari nan ma a matsayin malamin makaranta, nayi aikin koyarwa har zuwa lokacin da na karBa ODOGI.

Bayan biyan kudin ODOGI na bar aikin koyarwa, na koma aiki a ma'aikatar gona cikin 1974, wanda aka kaini Kadawa a matsayin malamin gona wanda ake kira (Extension Walker) inda aike noman rani. Koda yake gurin aikina yana Kadawa amma muna zaune a cikin wani gari da ake kira Kura. Na zauna cikin kura har tsawon shekara biyar, amma dukkan wannan lokacin da nake zaune cikin Kura ina karatun zama akanta ta hanyar karatun nesa ( Karatun nesa shine wanda za su aiko maka da kayan karatu kayi da kanka).

Wannan karatun nayi da wata makaranta a London wadda suke da jami'a a Lagos ana kiranta College of Accountancy London. Bayan nayi karatu na kimanin wata shidda, na kuma kasa gama wannan karatu sabo da wahalal samun aika jarabawa da kuma samun littattafai daga makarantar. Wannan abu yasa nabar karatun ba tare da na gama ba.

Daga nan sai na samu aiki a ma'aikatar kotunan jaha (Judiciary Dept), a bangaren kudi a matsayin akayon kudi. Na fara aiki cikin 1975 aikina kuwa shine shirya takardun albashi. Na zauna a matsayin mai shirya albashi har shekara uku, daga nan na zama mai biyan albashi (paymaster).

Na samu zuwa karin karatu a makarantar School of Manangement Studies Kano, wanda nayi karatun Executive Officer Accountancy, bayan wannan karatun shine na koma babbar Ma'aikatar kudi (Ministry of Finance) cikin 1978, amma ina aiki a ma'aikatar alkalai.

A 1980 an mai dani Lagos Liason Office a matsayin Ma'ajin kudi na jihar Kano, nayi aiki a Lagos har shekara uku, daga nan an dawu dani ma'aikatar aiki watau (Ministry of Works) a matsayin Akanta, kai na dai rike matsayi masu dama daga mai taimakawa akanta zuwa matsayin babban akanta.

Bayan rike wannan matsayan kuma, bisa amfani da computer da nayi cikin aiyukana na samu matsananciyar sha'awa ga computer. Sabo da irin wannan sha'awa tawa da computer na nemi hanyar samun karo ilimi cikin wannan fanni.i

Alhamdu Lillahi na samu taimakon Allah da na wani dan uwana wanda shine kwamishina a ma'aikatar kudi wanda ake kira Mohammed Aliyu, wannan mutun ba zan manta da shi ba a cikin rayuwa ta domin shine wanda ya bani karfin zuciya kan wannan karatun nawa. Nayi karatun digiri akan ilimin na'ura mai kwalkwalwa a cibiyar ilimin fasaha ta Indiana, dake birnin Fort Wayne a Amurka. Na kuma halarci kwasa-kwasai akan ilimin na'ura mai kwalkwalwa a cikin Amurka.

 

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.