Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

 Kabilar Hausa dai, kabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Kabilace mai &imbin al'umma, kuma a al'adance mai mutukar ha$aka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare su. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane.Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai,Borno da kuma Fulani. A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin angizo na fulani,sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa karkashen mulkin birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Nijeriya.

Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan addinin islama da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.Ginshikokin al'adun hausawa na da mutukar zaranta, <warewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sana'ar noma ita ce babbar sana'ar hausawa, sabo da ingancin noma; hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, sa<a da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanai'yar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cu&eni-na cu&eka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba hausawa bane a nahiyar Afirka.

Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa yan' mulkin mallaka na birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajame da aka kirkiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.