Allah daya gari bambam,
Hausawa sun bazu ko'ina cikin duniyar nan tamu, kuma daliban Hausa
sai kara yaduwa suke cikin jamioi (Universities) masu
koyar da Hausa a duniya. Sabo da haka muke kawu muku wannan shafi
domin karuwarku da karanta rubuce-rubuce cikin Hausa.
A matsayin mu na masu tallafawa bisa bincike akan harshen Hausa
a duniya ta hanyar sadarwar zamani ta cikin naura mai kwakwalwa
wato Internet, zamu cigaba da kawo muku bayanai dangane da littattafan
harshen Hausa a kai a kai, domin ilimantar da masu shaawar
wannan harshe a duniya.