|
Wata rana an yi wani mutum wanda ba shi da da,
ba shi da jika. Ya yi maganin duniyan nan don ya sami da, Allah
bai nufa ba, ya gaji ya dangana.
Ran nan yana zaune a kofar gidansa, sai ya ga wani ya kama
dansa yana ta duka, ba ji ba gani, sai ya ce, “M, Allah mai
girma! Dubi wani Allah ya ba shi har yana bugu, ni kuwa ga
shi ina nema ruwa a jallo, Allah bai nufe ni da samu ba. In
da ni Allah ya ba wannan, kome rashin jin kansa, me zai sa
in buge shi? Da da ya yi jin kai, da kada ya yi, ai duk uwarsu
daya, in ba dai don battan basirar mutane ba.”
A kwana a tashi, ran nan sai Allah ya ba matar mutumin nan
ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji. Aka yi suna, aka
sa wa yaron nan Hafaru. Yaron ya girma a sangarce, kome ya
yi uban ba ya ce masa kanzil. Ta kai dai fagen yaron nan ba
ya jin kan uban, balle ya taimake shi. Don son da uban nan
ke yi wa dan har abinci ma tare su ke ci, har ya kai ga aure
ba su raba kwarya da ubansa ba.
Da ubansa ya fara tsufa sai Hafaru ya rika kyamar cin abinci
da shi. In suna ci sai ya hana uban ya taba gabansa, yana
cewa wai uban ya faye kazanta, duk yana barin majina a hanci,
wai kuma ga shi da yawan tari, yanazuba musu yawu a ciki.
Uban dai bai ce masa koma ba. Ana nan dai har ya kai ga fagen
yana ci hannu na rawa, na baka na fadowa cikin kwarya. Sai
dan ya buga masa tsawa ya janye kwanon abincin, ya ce sai
ya ci kana ya ba uban.
Suna nan haka, sai ran nan Hafaru ya ce wai uban ba ya sude
kwarya, kullum sai ya bar kwano cakal, duk ya bata shi da
yawu. Saboda haka sai ya samar wau uban akushi, aka rika zuba
masa nasa abincin dabam. Ran nan yana ci garin makyarkyata
sai ya tuntsurad da dan akushin, tuwon ya zuba. Hafaru ya
zo ya yi ta yi masa fada, wai ya faye gidi-gidi. Saboda haka
sai ya tafi kasuwa ya sawo kwami irin na ban ruwan shanu,
ya kawo gida ya rika zuba wa uban abinci a ciki, ya ce, “Ture
wannan kuma, mu gani!”
Uban da bai ce kome ba, sai in abin ya dame shi ya yi ta
kuka yana cewa, “Wannan dai duk laifina ne da na ki kwabonsa
tun yana karami. Amma ba kome, Allah ya ba da mai rama mini.”
A kwana a tashi, sai ran nan Allah ya ba matar Hafaru ciki,
ta haifi da namiji, aka sa masa suna Ishiye. Da ya kai shekara
hudu ya yi wayo, sai ya zama ba shi da wajen wasa sai tare
da kakansa, ko abinci ma tare su ke ci. Uban ya yi ya yi ya
hana shi cin abinci da kakan, yaro ya ki. Saboda yaron nan
har aka rika sa wa abincin tsohon mai da nama. Kome yaron
nan ma ya samo sai ya nufo kakansa.
Ana nan har Ishiye ya kai shekara shida, ran nan suka tafi
gona da uban, yana rike masa da goran ruwa. Da suka isa uban
ya yi ta noma, har rana ta yi tsaka, sai ga matarsa, uwar
yaron, ta kawo masa abinci, ya kakkabe hauyarsa, ya zo ya
zauna yana ci, matar kuwa ta zauna kusa da shi. Sai yaron
ya dauki wani dan guntun gatari da ke nan, ya shiga gona ya
fara saran wata ‘yar itaciya da ke ciki, kwas, kwas, kwas.
Da uban ya hanga ya gan shi, sai ya ce, “Kai me ka ke yi nan?
Ajiye wannan abin banza, ka zo ka ci abinci. Haka ku ke yi
har ku sare ‘yar kafarku, ku bar mutane da jiyya.”
Da yaron nan ya ji haka, sai ya ce wa uban, “Ci naka, ka
bar mini nawa nan. Ni ina nan sai na sare itacen nan tukuna,
ina so in gyara rassan ne in yi maka dan kwami da shi, in
kai gida in ajiye, don in ka tsufa in rika zuba maka abinci
a ciki!”
Da iyayen yaron nan suka ji haka, sai suka yi nadama, suka
rike baki suka ce, “Ashe gaskiya ne abin da mutane ke fadi,
kome ka shuka shi ka kan girba.”
Daga nan Hafaru bai sake iza keyar yaron nan har gida. Da
isarsu gida Hafaru ka kama hannun dansa har wajen kakan. Ya
durkusa, ya gaya wa tsohon abin da yaro ya ce a gona, ya kuma
sake durkusawa ya roki tsohonsa gafara, yana ahi da kuka bisa
ga abubuwan da ya yi masa. Yaro na kallo, bai san abin da
a ke yi ba. Tsohon nan ya ce, “Mhm. Ai duk abin nan da aka
yi, ni na ja. Je ka, na gafarta maka duniya da lahira.”
Hafaru ya tashi yana murna. Daga ran nan bai sake, tozarta
ubansa ba, har Allah ya nufa ya cika a hannunsa, suka rabu
da alheri. Kullum in Hafaru ya ga dan nan nasa, in ya tuna
da maganar da ya yi, sai ya rike baki ya ce, “Ya’yan zamani,
saninku baa sanin halinku ba!”
Da Musa ya ji aku ya kai karshen wannan labari, ya ce, “Wannan
labari naka gargadi ne mai amfani ga wanda ya ji shi.”
Aku ya ce, “Ba wannan kadai ba, duk labarin da na ke bayarwa,
in ka lura, ka ga haka ya ke. Ai ba muni ga mutum da ya fi
ya kai muddin mutane bai iya bakinsa ba. Ga wani karamin misali
nan na kunkuru da gauraki.
|
|