Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Babban Mugun Abu Gun Da, Ya Yi Fushi Da Iyayensa 


  Ina tsammani ban taba gaya maka ba, wata rana aka yi wa wadansu ‘yam makaranta jarrabawa. Daga cikinsu akwai dan limamin garin, ana kiransa Ilu. Ba ya kula da aiki ko kadan. Kullum in ana koya musu aiki, shi sai ya yi ta wasa. Saboda haka da aka yi jarrahawan nan bai ci kome ba. Sai ya sami sifiri. Malaminsa ya yi fushi kwarai da ya ga haka, ga yaro dam manyan mutane ya lalace. Saboda haka ya je ya gaya wa liman abin da dansa ke ciki, don kada nan gaba a kore shi, uban ya bara rai.

Da aka gaya wa uban, sai ya kira shi wai ya yi masa fada ya kara kokari. Ya zazzage shi yana cewa in bai yi kokari ya yi karatu ba, ba shi da wani amfani, sai fa ya je ya yi tallan tsire.

Yaro ya tashi yana ta hushi, wai uban ya ce in bai yi kokari ba, zai ba da shi ga manauta ya je ya yi tallan tsire. Ya koma karamin zauren gidan, ya zauna. Yana nan yana ciccika, lokacin cin abinci ya yi, kanensa Ibrahim ya zo ya kira shi su je su ci. Sai Ilu ya dube shi da hushi, ya ce, “Je ka, ci! Ni ban ci.”

Ibrahim ya bushe da dariya, ya ce, “Kana tsammani wani ya kula don ba ka ci abinci ba? Je ka, huta.” Ya tafi ya gaya wa iyayen.

Liman ya ce, “Fushi ya ke yi, don na yi masa fada? To, kyale shi! Don cikinsa.”

Matar ta ce, “Ya da ta ki auren Sarkin Noma ba?” Ko da ya ke uwar ta ce haka, duk da wannan hankalinta na Wajen Ilu. Ta kaikaici idon liman, ta tafi wajensa tana rarrashi, ya ki cin abinci. Ta ya ta yi, sai ya dube ta, ya ce, “Ina ruwanku da ni, ni da kuka ce ba ni da amfani sai ga masu tsire? Ina kokarina, don malam ya ki jinina ya zo ya ce ba na kokari. Na ko san duk ajin nan ba a samun yaro goma gabana.”

Sai uwar ta tashi, ta ce, “Bar mu je mu ajiye maka.”

“Me za ku ajiye mini? Ni ko kun ajiye, ba na ci. Me za ku yi da mai tallan tsire?”

Da liman ya duba, bai ga matar ba, sai ya yi tsammani tana wurin Ilu ne, saboda haka ya sa baki ya kira Ilu, ya ce, “taso ka ci abinci, kada ka yi sakarci.”

Ilu ya c,e “Ba sakarci na ke yi ba, karatu na ke yi. Kuma ni mai tallan tsire, yaya zan ci abinci da ku?”

Liman ya ce, “Ho lalatacce, dan banza, mai taurin kai! Allah wadan yaron zamani!”

Ilu ya ce, “Na kuma zama dan banza, lalatacce, bayan da fari ga ni ba wan mahauta?”

Ashe Ilu ya ji, sai ya ce, “Kai kuma me ya sa bakinka ciki? Cin danko har da kaza?” Sai kuma fushi ya koma kan Ibrahim, ka san da ma an ce zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayi. Ya ce, “Wa ya tambaye shi ma ne, da ya sa bakinsa? Ka san Ibrahim ya raina ni.” Sai ya tashi, ya shiga dakinsu na kwana. Da zuwa sai ya tarad da wandon Ibrahim bisa gadonsa, sai ya jeho shi waje, ya ce, “Raini ke nan ya sa kazamin wandonsa bisa gadona, ya sa mini kyaya.” Ya haye gadonsa ya kwanta, yunwa kuwa ta fra dafa shi.

Yana nan kwance, wai don ya fito sai Ibrahim ya zo ya ce masa, “Ka yi bako.”

Ilu ya harare shi, ya ce, “Fita, ba ni wuri!”

Ibrahim ya yi murmushi, ya ce, “Abokinka ne ya zo.”

Ilu ya ce, “Na gaya maka ka tafi ka ba ni wuri tun da girma, ko?”

Ibrahim ya wuce, yana cewa, “Na san dai yunwa ta sa ka wannan hushi, ba kome ba.”

Ashe fa gaskiyar Ibrahim. Ilu ya tashi ya rasa inda zai sa kansa don yunwa. Ya yi shawara ya koma ya ce a ba shi abincin da aka ajiye masa, ya ga in ya yi karaya haka a yi masa dariya. Saboda haka ya jure dai. Can zuwa la’asar ya ji abin ba dama, sai ya dauki wandonsa, ya sulale zai kai kasuwa, sai ya ji motsin ubansa a zaure. Ya ga in ya gane zai ba shi kashi. Saboda haka ya komo ya kurda ta kofar damfami, ya fita. Ya nufi kasuwa wajen ‘yan tsumma. Ya tarad da wani mai dinkin mashimfidi, ya ce masa “Kana sayen wandona?”

Madinki ya karba ya duba, ya ce, “Kai, karbi abinka” kyallen ai namuzu ne. Tir! Ko Ingila ba sayenka a ke ba, sai Turawa su watsar sadaka. Amma to, nawa za ka sayar mini don in rika kara wa jakina wajen laheru?”

Ilu ya ce, “Nawa za ka biya?”

Madinki ya ce, “Kwabo hudu. Ko ma na zura jiki ne?”

Ilu ya ce, “An ce in bai yi kwabo takwas ba, kada in bari.”

Madinki ya bude baki kamar zai yi hamma, ya mika wa Ilu wando, ya ce, “Lalle in ka kewaya a sami mai sayensa sule ma. Duba shi, ai sabo ne.”

Ilu ya lura ba’a ya ke yi masa, sai ya mika masa wando, ya ce, “Kawo kudi.”

Aka mika masa awalaja, ya runtse a hannu, ya shiga kasuwa neman abin da zai ci. Magariba ta kusa, kowa ya watse, bai sami kome ba. Sai ya nufi tukubar tsire ya tsunguna, ya sa aka zare masa wajiya ta kwabo hudu, ya ci ya ci har ya koshi. Ya nemi ruwa ya sha. Ya tasam ma gida yana cewa, “Tun da aka zazzage ni, sai na sayad da kayana duka na ci abinci. Ba na sake cin abincinsu sai sun zo sun rarrashe ni.”

Yana zuwa gida, sai ya tarad da fura mai zuma uwar ta kai masa dakinsa. Ya bude, ya duba, ya diba kadan da ludayi ya kurba, sai ya ji ta coin. Ya ce, “Yau ga ni ina son furan nan, amma in na sha lalle a yi mini dariya.” Amma bari in kurba luddayi uku, na san dai ba a ganewa. Ya tsunguna ya sha. Ya gama ke nan, sai ga kanen ya shigo, ya ce, “Ina ka tafi, ga Inna ta ce in kawo maka fura?”

Ilu ya ce, “Ina ruwanka da in da na tafi? Me ka ba ni ajiya? Dauki furarku, ba na sha. Ni sakarai, dan banza, me ruwanku da ni? In je in mutu mana.”

Ibrahim ya fita ke nan da fura, sai wajiya ta yi ta taso wa Ilu, sai amai. Nan da nan ciki ya murde shi, ya yi ta murde-murde bisa gado yana kugi.

Da uwar ta ji, ta kira Ibrahim suka rugo su ga ko mene ne. Suka tarad da shi sai amai ya ke yi, duk idanduna sun jujjuye, suka tambaye shi abin da ya ce. Ya ce, “Na-na-nama.”

Nan da nan uban ya ce a nemo tsamiya. Uwar ta ruga. Ilu sai kuka ya ke ya yana murde-murde, ya kasa kwance ya kasa tsaye. Nan da nan uwar ta kawo, aka jika, aka dura masa ya sha. Sai ya barke da zawo. Kafin lisha ya sami sauki. Gari na wayewa ya warke sarai. Sai ya tafi wajen iyayen, ya roke su gafara, ya ce daga yau ba ya sake yi musu musu. Aikin makaranta kuwa, su saurari abn da zai faru in an sake yi musu jarrabawa. Daga ran nan ya koma dan kirki, duk ajinsu aka rasa kamarsa. In ka ki jin joron iyayenka, ka ji na Mahaliccinka.

Musa ya duba, ya ga har rana ta kunno, sai ya ce wa aku, “Ka ga dai da zan yi tafiya, ka tsai da ni a wofi, ga shi ka sa na makara.” Ya koma ciki da hushi. Duk yinin nan ya hana a kawo wa aku wani abinci sabo.

Da rana ta fadi, asuba ta yi, aku ya kura ido hanyar da Musa ke fitowa. Ko da ya hango shi tafe da takobi tsirara, sai ya ce, “Daukan ni mu tafi tare.”

Musa ya harare, shi, ya ce, “Ka yi mini amfanin me wurin yaki, dan tsurut da kai haka? An ce maka labari a ke so?”

Aku ya ce, “Ko ba don labari ba, dabara ai ita ce yaki, ba karfi ba. Ina zaton ba ka taba jin labarin yadda bunsuru ya yi dabara har ya kori kura ya gaje gidanta ba ne?”

 

 

Koma baya




{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.