Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Labarin Wani Bakauye Da Wadansu ‘Yam Birini 



  Wata rana wadansu ‘yam birni na zaune, sai ga wani bakauye tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma yana cafewa.

Da ‘yam birin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, “Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so.”

Saura suka ce, “In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? A buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace.”

Sai dan birin nan ya tashi ya bi yaban bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa,ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika ya’yan’uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto.

Can da dan birin nan ya ga ‘yan’uwansa sun bace da jaki, sai ya ja ya cirje. Bakauye ya ja ya ya, yana has has has! Amma bai waiwaiya ba, yana jin kada ya dauke kansa dan hoto ya yi wani abin mamakin da ba gani ba. Da ya ja dai ya ji jakin bai biyo ba, sai ya waiwaya don ya buge shi su tafi. Dubawan nan da ya yi sai ya ga mutum maimakon jakinsa. Abin ya ba shi mamaki, ya ce, “kai, me ya faru haka?”

Dan biri ya ce, “Ni ne jakinka, tsaya ka ji labarina, domin abin na da ban mamaki. Tun asali ni da ma ba jaki ba ne, mutum ne dan’uwanka. Ina zaune da tsohuwata, sai ran nan kuruciya ta debe ni, na sha giya. Sai na zo gida, ba ta san abin da ya faru ba Ta yi mini ‘yar magana kadan ba ma ta sashin hankali ba. Ka san wanda ya yi sha bai san inda kansa ya ke ba, sai na zage ta. Ta dafe kai ta dube ni, ta ce, ‘Ni ka ke zagi? Ashe har Allah ya kawo mu lokacin da ‘ya’ya kezagin iyaye?” Ka san mai maye sai na ce, ‘Na zage ki! Ke wace ce da ba za a zage ki ba?” Sai ta sa hannu kai, ta yi ta kuka, ta roki Allah ya mai da ni jaki. Tun ran nan na ke jaki har Allah ya sa na zo hannunka. Yau ina ga ta gafarta mini ne, ka ga na koma mutum.”

Bakauye ko da jin haka sai tausayi ya kama shi, ya kura masa ido, ya ce, “Don Allah ka rika bin maganar iyayenka, kada ka yarda kuruciya ta debe ka, ka yi kyalkyalin tsada. Ga ka kyakkaywan sauraiy, amma zuciyarka ta munana.”

Dam birni ya yi sako, yana jin wa’azi, kamar wani mummuni. Da bakauye ya kare ba shi wa’azi ya ce, “To, na ko bi wa’azin nan da ka yi mini.” Ya faki idon bakauye, ya yi masa gwalo. Bakauye ya kwance masa igiya ya tafi, ya nufi wajen ‘yan’uwansa. Suka kai jaki wani gida suka daure, kafin ranar kasuwa su kama shi su kai su sayar.

Bakauye ko daga nan bai isa kasuwa ba, sai ya koma gida ya gaya wa matarsa duk abin nan da ya faru. Suka yi ta jin tausayin dam birini, domin wulakantad da shi da suka yi suna tsammani jaki ne, ba dan Adam ba ne.

Ran nan bayan kamar kwana uku, ranar kasuwa ‘yam birinin nan suka kai jaki su wayar, su sami abin zaman gari. Sai aka yi muwafaka bakauyen nan kuma ya tafi neman jaka. Da ma don ya sami mace shi ya sa ya so ya sayad da nasa namijin.

Ko da ya isa ya duba haka sai ga jakinsa na da, sai ya matsa kusa da shi, ya dube shi, ya yi tsaki mts, ya ce, “Allah wadanka! Duk wa’azin nan da na yi maka ba ka lura ba? Mai hali ba ya a wofi. Dubi duk wahalar da ka sha wajena, buga wannan kasuwa, dauki itace kai wannan kasuwa, duk ba ka daddara ba, sai da ka sake yin sha. Ni dai na game ka. Sai ku yi can da wanda tsautsayi ke bibiya, mu dai muna tudunmun tsira.” Ya hauri jaki ya wuce.

Dan Sarki ya ce, “Ai ko wannan lalle ya isa bakauye!”

Aku ya ce, “Ina ka san ya isa muzi tukun? Ai da sauran labari.”

Da ya duba bai samu wani jakin saye ba, sai ya komo gida yana kunne da dam birnin nan.

Can zuwa maraice, ‘yam birnin nan suka karyar da jaki, suka karbi awalaja.

Da wata kasuwa ta kewayo, sai bakauye ya samo kudinsa ya komo kaduwa neman jaka. Yana zuwa kusa da kofar gidan mai gari, sai ga dam birnin nan da ya ce shi ne ya rikide jaki, bakauye ya saya. Ya yi sitati za shi kasuwa, kayan nan sun dauki zargina tsar. Ko da bakauye ya gan shi sai ya gane shi, haushi kuwa ya kama shi, ya ce a ransa “Kai ba na dai yarda in yi asara a wofi don lalataccen nan!” Sai ya dubi dam birni, ya ce, “Ashe ka koma mutun kuma?”

Dam birni ya yi biris da shi. Sai bakauye ya tasam masa ya kama shi, ya sa masa akumari, ya ce wai zai hau ya tafi da shi ya yi kwarami.

Dam birni da yana tsammani da wasa ya ke, sai ya ga ya yi wuf ya haye kafadarsa. Ga shi ya fi dam birnin karfi, ya kuma fi shi iyo kokawa, ya yi ya yi ya ka da shi, ya kasa. Mutane suka cika wuri su ga ikon Allah. Bakauye ko bai kula da su ba, sai dl, dl, dl, ya ke yi, yana has! Kur! Wai shi ya hau jaki, yana ta ba shi dudduge a ciki, yana duka.

Dan dam birni ya ji ba dama, sai ya kwanta. Bakauye ya haye cikinsa yana duka, wai ya tashi su tafi, yana cewa, “Ai fa ko a janye sai na kai ka gida, ka daukam mini taki, ba na yarda I yi asara. Ka sho ka zagi uwarka, ta mai da kai jaki, na saya ban sani ba, ta koma ta gafarta maka ka koma mutum, na dauki asara, na sake ka. Ranar Talata kuma, da na zo cin kasuwa, na tarar ka sake yin wani abu ta mai da kai kuma jaki, wani ya saya. Ga shi yau kuma ina ga ta gafarta maka, ka koma mutum. Ka sa kuma wancan mutumin da ya saye ka ya yi asara kamata.” Ya dubi mutanen da ke kewaye, ya ce, “Don Allah, jama’a, gaskiya fa kaya? Ai ka san ba abin da zai hana ni yin kwarami da shi, ko kuwa ya fanshi kansa.” Sai ya sake hau masa da bugu, wai ya tashi su tafi dai kauyensu.

Suna cikin haka sai ga wani Dogari, ya kwashe su ya kai ga Alkali. Alkali ya tambayi bakuye yadda aka yi, duk ya kwashe ya fadi, bai rage kome ba.

Da mutane suka ji haka, suka ce me za su yi ba dariya ba? Alkali ya tambayi dam birni in hakanan ne. Dam birni ya ce faufau shi bai ko taba ganin bakauyen ba, sai yau.

Alkali da ma ya san halin irin mutanen nasa sa aika. Sai ya sa Dogarai su tambaye shi sai ya fadi gaskiya. Da masu fushi da fushin wani suka same shi, ya ji zafi, sai ya ce, “Wayyo Allah, ku tsaya, ku tsaya!” Suka dakata. Ya kwashe maganar bakauye, ya ce duk hakanan ne, mutane suka yi ta al’ajibi. Alkali ya sa ya biya bakauye kudin jakinsa sule goma sha daya da taro, yadda bakauye ya e ya saya. Ka san abu hannun barawo, shi fa dam birnin nan sule shida da sisi ya sayar da shi wannan kasuwar da ta wuce.

Alkali ya sa aka daure dan birni. Bakauye ko aba ba shi kudinsa, ya tafi. Bakauye dai bakauye ne. Duk abin nan gogan naka har ya tafi bai san wayo ba dam birnin nan ya yi masa ya sace jakinsa shi har yanzu tsammani ya ke dai rikida ya yi.

Musa ya yunkura zai fita, sai ya ji magana a babban zaure, wadansu daga cikin bayin sauro ya dame su, sun kasa barci. Suka farka suka yi ta tadi har gari ya waye. Musa ya koma gida yana jin haushi.

Da shigarsa gida ka san ba abin da ke cikin idonsa sai barci don duk cikin ‘yan kwanakin nan bai runtsa ba. Ko da ya kwanta bai farka ba sai can zuwa la’asar, ya tashi ya yi salla, yana nan har magariba ta yi, aka ci abinci. Bayi suka duka hira.

Da Musa ya ji bayi sun yi barci, ya tashi ya shigo damaru, ya ce wa aku, ‘Don Allah yau kada ka tsai da ni, sallame ni in tafi. Kai, Allah ya kiyashe mu! Ban taba ganin tsuntsu mai surutunka ba.”

Aku ya tuma nan ya tuma nan, ya ce, ‘Ba kai kadai ba, Allah ya ba ka nasara, kowa na ganin surutummu, amma in kun lura da mu ba mu surutu a banza. Ko dai mu ba da garadi, ko kuwa don rashin munafuncimmu mu bayyana asirin da muka gani ana kullawa za cuci jama’ar Annabi. Don haka yanzu duk inda muka fi rashin fada shi ne wurin mata. Tsaya ma ka ji yadda wani aku ya yi da wata mace, don ka san dai al’amarimmu muna yi don Allah ne, ba don mutane su yaba ba.”

 

 

Koma Baya

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.