Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Magana Jari Ce  



  A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abinya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa – kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba susan abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi.

Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da ‘ya ‘ya, ba shi da kane, ba shi da wa. ‘Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da ‘yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni’imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin.

Ana nan ran nan sai ‘yan nan tasa ta haifi da namiji, aka yi shagali, aka sa wa yaron Malimudu. To, amma ko da ya ke Sarki ya yi murna kwarai da ya sami jika, duk da haka murnarsa ragaggiya ce domin dan mace ba ya gado, balle har a ce ya yi saraunta.

Yana nan cikin wannan bakin ciki, sai ran nan wani shaihun malami ya so ya ce masa, “Na yi mafarki jiya, a gaya mini da za ka tara malamai arba’in su yi ta yi maka addu’a har kwana arba’in, in Allah ya so za ka haihu.”

Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya dauko kudi da riguna zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kudi suka kawo shi ba, ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallama, ya tafi.

Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa manya malamai guda arba’in na kasarsa, ya gaya musu abin da ya ke so. Suka ce, “To, Allah ya karbi rokonmu!” Mutane suka ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duka.

Bangiji ya nufe su da katari, ya karbi rokonsu. Kwanan nan arba’in ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin da aka yi cikin kasan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan al’amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin wannan dan karamin littafi. Aka dai fada wa yaron nan suna Musa. Watan tsakaninsu da jikan Sarki abin bai ko yi shekara ba.

Sarki kuwa ya dauki ransa ya kallafa bisa kan yaron nan. A ma tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa dan nan nasa, abin ya zama kauyanci ke nan.

Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuma ya aika aka kawo jikan nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba daya, don su rika wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin da ke raba su.

Da duk abin nan burin Waziri, tun da Sarkin nan ba shi ba da namiji, in ya mutu shi ya ci saraunta. Yana alla-alla Sarki ya mutu bai haihu ba, sai Allah ya kaddara haihuwar wanan yaro. Tun ran da Waziri ya ji gudar haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi baki kirin, daga ran nan ya zama ko mai suna Musa ba ya so ya gani, ya shiga kulle-kulle kullum na yadda zai yi ya kashe Musa, ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gagara. Har yara suka yi kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da su ya ke zuwa.

Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri ya sami wata dabara, ya ce a ransa ‘Alhamdu lillahi, ko-da-ya-ke ba yadda za a yi in sami Musa wani wuri shi kadai ba tare da Sarki ba, balle in san abin da zan yi masa, ai in na yi kokarin da na raba Musa da Mahmudu, kome ya yi kyau. Domin yadda suka shaku haka, lalle in aka raba su hankalin Musa zai tashi ta wannan hanya zan san yadda zan yi in sa shi ya sulale da dare ya bi dan’uwansa.” Sai ya yi dariya, ya buga kafa a kasa.

Kashegari, ko da ya tafi wagen fadanci aka fara ‘yan tade-taden duniya, sai ya takalo maganar yaki, ya ce, “Mu dai mun saki jiki da duniya yanzu, ba mu shirin kome.”

Sarki ya ce, “Me ya kawo wannanmagana, Waziri? Muna cikin sulhu haka, me ruwammu da wani shirin mayaka?”

Waziri ya ce, “Ai ka san ba a san abin da sauran kasashe ki ciki ba. Gwamma ko mu zauna da shiri, don ba a fafa gora ranar tafiya.”

Sariki ya ce, “Wane shiri ya wanda mu ke da shi yanzu? Ga Sarkin Yaki, ga Barde, ga Madawaki, cikinsu kowane ya yi kikan kura sai a ba shi hanya.”

Waziri ya ce, “Wadannan ai duk sun tsufa, ga Sairkin Yaki yanzu a kalla ya ba saba’in baya. Wanda ya ke haka, tun da Allah ya nufe shi da samun magaji, ya kamata ya huta. Dabarata sai Mahmudu ya koma gidansu, ubansa ya rika koya masa al’amuran yaki.”

Musa da ke nan sai ya tsolma baki ya ce, “In dai don a dauke Mahmudu ne, a bar ni ni kadai, ni ban yarda ba, sai dai mu je a koya mana tare.”

Waziri ya kau da kai ya kuta, ya ce, “Ina ruwanka da koyon yaki, kai da za ka sa a je a yi maka?”

Musa ya ce, “Ni dai ban yarda mu rabu ba.”

Sarki ya e, “Tun da musa bai yarda ba, dabararka ba ta yi ba ke nan, Waziri.”

Waziri ya bata fuska, zai fara wata magana sai ga wani ya zo ya fadi gaban Sarki, ya ce, “Ga Wazirin Sarkin Sinari ya zo da wadansu manyan garinsu, ya ce a yi masa iso.” Sarki ya ce ya shigo. Da ya shigo ya yi gaisuwa, ya mika masa takarda. Magatakarda ya karba ya buda, sai ya ga an rutuga:

“Takarda ta fito daga Sarkin Muminai, Sarkin Sinari, Abdul’azizi, dan Shahu Muhtar, zuwa ga masoyinsa amininsa Sarki Abdurrahman, gaisuwa mai yawa, da so, da yarda, da aminci. Amma bayan haka ina so in karfafa zumuntan nan da ke tsakanimmu, saboda haka na ba dana Musu ‘yarka Sinaratu, in sun kara girma a yi biki. Sai mu shirya a gama su tun muna da rai, Haza wasalamu.”

Da Sarki ya ji abin da takardan nan ke ciki sai ya tashi da fada, ya fizge takarda daga hannun, Magatakarda ya kyakke ta. Ya tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefad da shi gefe guda. Sarakunansa suka shiga tsakani, suna “Hucewa mai duniya! Rashin hankali ne na yara.”

Sarki ya ce, “Ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi aka yi Sarkin Sinari, balle ‘yarsa Sinaratu?”

Ya dubi mutanensa, ya ce, “Ku yi ta dukansu sai sun bar kasata!”

Wazirin Sinari ya ruga, ya haye dokinsa, mutanensa suka dafi bayansa. ‘Yam birni suka bi su eho, eho. Fada duk ta rude, fadawa suka yi ta duban juna. Liman ya ce, “Allah ya ba ka nasara, abin nan da aka yi, a aika lafiya dai?”

Sarki ya ce, “me ya firgita ka? Don dai mai garin Sinari ko cewa na yi a mare shi, ya yi magana?”

Barde ya ce, “Ai Sarkin Sinari yanzu ganin kansa ya ke daidai da kowa. Ban yi tsammanin abin nan da aka yi masa zai kyale ba.”

Sarki ya ce, “Kai ma ka karai ne, kamar Liman?”

Waziri ya ce, “Ba karaya ba ce, ai gaskiya ce abin da na ke fadi yanzu na kan ba mu da shirin kome.”

Mutane suka ce, ‘Gaskiyarka, Waziri, ga Sarkin Yaki yau kwanansa kamar ashirin ke nan sai a kwantar a tayar, ba shi ko da magaji.”

Sarki ya kara fusata, ya ce, ‘Ba shi da magaji? Watau kun shiga maganar tsohon banzan nan? In dai maganar Mahmudu ku ke wa mita, na dauki alkawari, ko bai iya kome ba, duk yakin da ya fara tashi nan gaba, shi zai zama jagaba.” Aka gama fadanci aka watse, suka tafi suna zunden Waziri.

Waziri ya koma gida da fushi, ya kama shawarwarin abin da zai yi wa Sarki ya huce haushinsa. Daren nan ya kasa barci, ya kulla wannan ya kwance, har asuba. Da gari ya waye sai ya rubuta takarda zuwa wajen Sarkin Sinari, ya ce, “Kada wani abu ya ba ka tsoro da Sarki Abdurrahman, shirim ne ba inuwa. Muddin ka dauki alkawarin za ka nada ni Sarkin garin nan, ni ko na san yadda zan yi in taimake ka ka ci kasar. Domin duk mutanen kasar sai abin da na ce musu. Da farko sai ku dauri niyya maza ku zo kafin su shirya. Ku biyo ta kadarkon Kimba, don ta wannan hanyar har ka shigo birni kowa bai sani ba. Ku taho tare da wannan yaro ya nuna muki hanya, domin ko ban da shi nan kasar ba wanda ya san wannan hanya.” Sai ya ba wani amintaccen bawansa, wai shi Barakai, ya gaya masa yadda zai yi, ya sallame shi.

Sarki Abdurrahman kuwa bai sake komawa ta kan Sarkin Sinari ba. Ana nan ran nan ya sa aka daura wa dawaki sirada, ya hau tare da yaran nan suka tafi shan iska, har suka kai wata fadama, suka sauka suna hutawa, sai ga wani Balarabe dauke da aku cikin keji. Ko da Musa ya daga ido ya gan shi sai ya ce, “Alo, alo, ga aku a saya mana!”

Nan da nan wani bawan Sarki da ska je da shi ya kira Balaraben nan, ya tambaye shi kudin akun. Balarabe ya ce, “In ba jaka guda ba, ba na sayad da shi.”

Da bawan nan ya ji haka sai ya ce, “A’a! Da Sarkin za ka yi ba’a? Kana tsammani sarki ya tambaye ka karin magana ce?”

Da bawan nan ya fusata Sarki haka, sai ya cika ya ce a kama Balaraben nan. Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za su cinye shi danye, da shi da tsuntsunsa duka.

Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya kada fifike, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijna. Ni ma a jaka gudan nan da ya fadi a ganina ya karya mini daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda kadai ba.”

Sai sarki ya ce wa bayi su tsaya. Ya dubi dan tsuntsu, ya ce, “Kai kuwa dan tsuntsun nan mene ne dalilinka na wannan cika baki haka?”

Sai aki ya dukad da kai, ya ce, “Akwai kuwa, Allah ya ja zamaninka, takamar da na ke yi ba don saboda kyaun jikina kadai na ke yi ba, ba ko don saboda dadin bakin nan da Allah ya ba ni ba, amma saboda baiwa wadda Ubangijimmu ya yi mini ta wajen iya duba. Har yanzu ta kai ni fagen ina iya ba da labarin abin da za a yi nan gaba, balle ma a tambaye ni wanda aka yi ya iyaka. In kuma labaruruka ka ke son ji, ko na aljannu, ko na barayi, ko na Sarakuna, in ka saye ni in ya so ma kada ka sake batad da kudinka a banza garin sayen Alfulaila, ko wadansu littattafai na Turawa wadanda ba su da wani labari daga na tafiye-tafiyen gan kasashe, sai fa na tarihe-tarihe da na lissafe-lissafe, da na kiwace-kiwacen lafiya, masu gundurad da mutane. In kuma karuwa ka ke nema wurin arziki, in ka saye ni bukata ta biya.”

Sarki ya ce, ‘Ta wajen suruntun naka na wofi?”

Aku ya ce, “Surutu ba abin rainawa ba ne. Magana ai jari ce.”

Da yaran nan suka ji ya iya ba da labarai, da ma abin da su ke so ke nan, sai suka yi ta tsalle-tsalle suna murna. Sarki ya rike baki yana mamakin wannan tsuntsu. Sarki ya ce wa aku, “Tsaya mene ne na wanan irin fafarniya? Yabon kai jahilci. In kana da hikima, gaya mini yau shekarun Musa nawa?’

Sauran mutanen da suka zo tare da Sarki suka fashe da dariya, suka ce wa Sarki, “Allah ya ba ka nasara, ka ko kashe mana bakinsa! Ya fadi mu ki kan ba karya ba.”

Aku ya dubi Musa, ya ce, “Yau shekarunsa goma sha hudu da wata biyar d kwana uku.”

Mutane suka ce, “A’a! Ai ko, allah ya ba ka nasara, gaskiyarsa!”

Sarki ya ce, “Kai ji ya yi wajen wadansu ana fadi. Labarin musa yanzu ina ne bai kai ba?” Ya sake ce wa aku, “To, mun ji ka rike wannan da ka ji mutane ke fadi, amma wace rana ce aka haife shi?”

Aku ya sake duban Musa, ya ce, “Ranar Jumma’a da la’asar.”

Sarki ya ce, “A’a! Ai ko gaskiyarsa.” Ya dubi aku, ya ce, “Da ya ke kana da hikima, sai ka gaya mini me zai fara aukuwa gare shi?”

Aku ya ce, “Ba za ka so ka ji wannan al’amari ba, don zai bata maka rai kwarai. Ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta.” Sarki dai ya nace sai ya gaya masa, in ya ki kuwa yanzu ya sa a hura wuta a babbaka shi da rai.

Da aku ya ga Sarki ya fusata sai ya ce, “Ka yi mini gafara bisa ga abin nan da zan fadi. Musa zai zama sanadin cuce-cuce, da raunuka, kai har da halakar rayukan mutane kamar dubu na kasan nan. Wannan al’amari kuwa ba da dadewa ba zai auki. Da ma kana ganewa, ka sake shiri tun da wuri.”

Da Sarki ya ji haka sai ya hasala, don aku ya ce dansa zai zama sanadin mace-mace. Ya dauki kejin ya jefar. Ya tashi zai je ya take dan tsuntsun nan ya mutu. Bayi kuuma suka zaburam ma Balarabe, duk wurin ya harmutse. Sai kwaram suka ji kuwwa. Su waiga haka, sai ga wani mai doki sukwane, ya zo ba ko sirdi, duk jikinsa jina-jina, abin ba kyaun gani. Ya fadi gaban Sarki, ya ce, “Wayyo Allah! Wayyo Allah! Ka yi mana agaji! Ai ga Sarkin Sinari can ya shigo kasarka da yaki, yan garuruwammu na nan kan iyakar arewa duk sun zama toka. Na rantse har da girmanka, ni kadai na tsere!”

Sarki da mutanensa duk suka yi sako, kowa na duban dan’uwansa. Sai kawai daga bayansu suka ji wani abu, ha ha ha! Duk suka waiga firgigi, sai suka ji daga cikin keji an ce, “Ai ga ta nan. Da ma na gaya maka, ka tashi kashe ni, kai ne ba ka sani ba, ba irin magana kamar tamu a ke rainawa ba.”

Sarki bai sami ta cewa ba. Aku ya ce, “Ko yanzu in ka bi shawarata Allah ya kyauta, ba wani abin da zai bata maka rai.”

Sarki ya dubi aku da fushi, ya ce, “Ka rufa mana baki nan! Wata shawara gare ka?”

Musa ya a baki ya ce wa Sarki, “Allah ya ba ka nasara, matambayi ai ba ya bata, ya fadi muji.”

Sarki ya ce, “To, fadi, in ko shawarar taka ba ta fita ba, ina murde maka wuya, kowa ya huta.”

Aku ya ce, “Yanzu Sarkin Sinari ya kusa kawowa kadarkon Kimba, nufinsa ya biyo ta tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki ya kewayo ta gabas ya fada wa birni ta inda ba a tsammaninsa.”

Sarki ya ce, “Cikin ‘yan gari ma akwai wani mahalukin da ya san wannan hanya, balle Sarkin Sinari?”

Aku ya ce, “Kai dai ka ji abin da zan gaya maka. Yanzu maza ka koma gida ka aika da ‘yan kwarbai su tsare makurdin nan da ke tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki. Kome yawan rundunarsa, ko mutum goma masu karfin zuciya sa iya mai da shi baya a wannan wuri, kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaki.”

Sarki ya yi tsaki. Musa ya ce, “Dan akun nan ya san abin da ba mu sani ba, sai a bi shawararsa mugani.” Ko-da-ya-ke abin nan da aku ya fai Sarki na jinsa kamar tatsuniya ce, duk da haka tun da Musa ya sa baki sai ya hau, suka koma gida, ya zabi ‘yan kwarbai guda dari ya aika da su inda aku ya misalta masa. Ya kuma ta da manzanni ya aika da su kudu da arewa, gabas da yamma, a gaya wa mutane su yiwo harama su zo maza da shirin yaki. Makera kuma suka shiga gyara makamai.

Ana nan yatan kamar kwana biyar sai ga wani daga cikin ‘yan kwarban da Sarki ya aika ya zo a sukwane da bushara, ya ce wa Sarki, “Allah ya ba ka nasara, ai wannan dabara da ka yi ta fita. Shekaranjiya da hantsi muna nan mun yi kwanto inda ka ce mana, sai muka hangi kura ta toshe sama, sai tsinin masu kawai ka ke gani suna wal wal wal. Ga masu dawaki da dakarai bilahaddin, muka hanga har iyakar ganimmu, ba mu ga karshensu ba. Muna nan dai sai da muka bari goshin yaki ya kawo dab da mu, sa’an nan muka yi ta sako musu kibau kamar ruwan sama. Na gaba suka juya da baya suka gamu da wadanda ke biye, abin ya cude, ga ‘yar hanya karama, dawaki suka yi ta zallo suna fada wa junansu. Mu ko dai sai zuba musu kibau mu ke, na bisa na ta sullubowa kasa, dawaki na tattake su. Cikin na gaban nan sai sai dai suku sami komawa wajen uwar yaki. Jim kadan kuma sai ga wadansu suka taso wai za su yi mana sukuwar salla. Ba dama, don hanyar ta cika matsatsi tsakanin duwatsu. Muka yi musu yadda muka yi wa na farko. Aka yi ta aiko wadansu, muna yi musu hhakanan, har la’asar ta yi. Da suka ga ba dama suka koma, suka bar gawawwakin ‘yan’uwansu nan, abin sai wanda ya gani!”

Ko da Sarki ya ji haka, sai ya yi kamar ya ce kaka don murna. Ya shiga ya gaya wa aku, ya yi ta gode masa, ya yi kamar ya fauke shi ya hadiye shi. Nan ake ya dauko jaka biyu ya ba Balarabe, kudin aku. Ya kawo ingarma taka hau ya ba shi, ya kara masa da bayi bakwai, ya ba shi kyankyandi goma sha biyu na tufafi, ya sallame shi ya tafi.

Cikin daren nan sa ga Barakai ya komo ya gaya wa Waziri abin da ya faru, ya ce, “Mu ke kan gaba, sai kawai muka ga ana ta zubo mana kibau, har aka sami dokina ban sani ba, sai na ga kawai mun zube. Ni ko da na ga haka sai na kwants karkashinsa kamar na mutu. Na yini nan ba motsi, ana ta yaki bisa kaina. Da dare ya yi tsaka, na ji sun yi shiru, sai na sulale na dawo.”

Waziri ya yi masa barka, ya ce, “In ji ba a gane kai ne ba?”

Barakai ya ce, “Na tabbata ba wanda ya gane ni.”

Waziri ya ce, “To, madalla. Ama ina mamakin yadda Sarki ya gane ta nan za su bullo.”

Barakai ya ce, “Ni, ma hakanan. Bakina dai ban yi da kowa ba.”

Waziri ya ce, “Lalle mutanen Sinari akwai munafukai. Amma ba kome, gobe ma rana ce.”

Bayan kamar kwana uku gayyar yaki ta taru, gari ya cika da dawaki da dakaru har ya amaye, kauyukan rabe da birni ba wanda bai cika ba. Da Sarki ya ga duk an hallara, tun da sassafe sai ya kira Waziri ya bar shi tsaron gari.

Waziri ya duka, ya ce, “Na ko karbi amanan nan taka da hannun dama.” Yana, ‘yan koke-koken munafunci.

Sarki ya tashi ya shiga gids, ya kira wadansu bayinsa amintattu guda goma sha biyar, ya bar su tsaron digan, ya ce su lura kada so Musa su fita waji sai sa’ad da Allah ya dawo da su lafiya. Ya kuma tafi ya kira su Musa wajen aku, ya ce musu, “In kun kuskura kuka fita wajen gidan nan bayan ba ni nan, ban yarda muku ba. Kama kome za ku yi ban yarda muku ku yi shi ba, sai kun zo kun shawarci akun nan. Abin da ya ce muku kuwa, ko da kunsa tsammani kari kuskure ne, kada ku ketare shi.”

Yara suka fashe da kuka suna cewa, “Baba, mun ji abin da kai ce duka, ma ko bi.”

Sarkin ya juya wajen aku, ya ce, “Kai kuma, go amana nan, in ka ci amanata, to, Allah ya isa.”

Aku ya ce, “Hakannan ne, ranka ya dade. In allah ya so kuwa, ka tarad da abin da ka ko so.”

Sarki ya ce, “To, madalla.” Zai tashi ya ce, “Af, jiya kuwa na ga wani da wata macen aku, na saya don in gama ku tare, ta rika debe maka kewa.” Ya aika aka kawo ta, aka gama su. Aku ya yi godiya, suka yi sallama da Sarki.

Walaha na yi, aka buga tamburan tafiya. Sarki ya taka ya hau, sai Waziri ya zo ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ko ka sha’afa ne? Ka yi alkawari duk yakin da ya fara aukuwa da Mahmundu za a.”

Sarki ya kawo iya wuya, ga bakin cikin rabuwa da iyali, ga kuma wata maganar banza. Sai ya sa baki ya kira Mahmundu ya ce, “Ga doki nan, hau mu tafi, da kai za a.” Mahmundu ya dare doki.

Musa ya ce, “Ni ma zan tafi!”

Sarki ya ce, “Ba na zuwa da kai.” Musa ya fashe da kuka, ya ce ba ya rabuwa da Mahmundu. Sarki ya daka masa tsawa ya koma gida, ya kira Sarkin gida da bayin nan da aka bari tsaro, ya ce, “Ku lura kada ku bar Musa ya ko leko waje, in wani abu ya same shi ina yanka ku!” Suka shiga da shi. Runduna ta dunguma, aka taryi inda Sarkin Sinari zai fito.

Da Waziri ya ga an raba Musa da Mahmundu, ga shi kuma Sarki ba ya nan, sai ya tafi gida ya yi ta murna, yana tsalle-tsalle. Ya shiga tunane-tunanen abin da zai yi ya halaka Musa kafin Sarki ya daawo. Domin in ya samu ya kashe Musa, kome ya faru wurin yaki shi ke bisa. In Sarkin Sinari ya ci nasara, bukaa ta biya, in ko Sarki Abdurrahman ma ya ci, duk daya, don ko ba jima ko ba dada shi ne zai gaje shi.

Da ya kurar yaki ta bace, sai ya kira wadansu katti hudu cikin bayinsa wadanda ya amince da su, ya ce yana da wata bukata, wanda duk ya biya masa ita zai ‘yanta shi.

Bayin nan suka dauka gaga daya, “Fadi, yanzu ka ga aiki da cikawa!”

Waziri ya ce, “Inaso ku kashe mini Musa. Yana nan cikin gidan Sarki an kulle shi, an sa duk bayin gidan su tsare shi.”

Bayin nan suke ce, “Af, in haka ne yaya za mu yi mu kashe shi?”

Waziri ya ce, “In dai kun kasa kunne kwa ji, aiki a ke so ba surutu ba. Yanzu duk hankalinsa yana ga Mahmudu dan uwansa. Na san lalle in kafa ta dauke, yadda aka yi duk sai ya yi kokarin da ya fito don ya bi shi. Sai ku nemi buhu, in dare ya yi ku je da shi kogi ku jefa.”

Baye suka ce, “An gama.”

Musa ya yini ran nan sukuku. Mutane suna tsammani uban ya ke tunawa, saboda haka ba su koma ta kansa ba. Da magariba ta yi Sarkin Gida ya kulle kofofi duka, ya miko wa Musa mabundi ta taga, yadda Sarki ya ce ya rika yi kullum. Ya koma zaure wajen bayin nan da aka bari, suka yi ta hira har kusan asuba, sa’an nan barci ya kwashe su. Duk abin nan kuwa Musa bai yi barci ba, yana jira bayin nan su yi, ya je ya gaya wa aku ya bar shi ya fita ya bi su Mahmundu.

Da ya ji sun yi barci, sai ya shirya, ya dauki mabundan nan, ya shiga damaru, ya dauki garkuwa da mashi, ya nufi wurin aku. Sai ya tarad da aku namijin, watau wanda aka fara saye mai sihiri, yana barci. Sai ya ce, “Af, tun da wannan ke barci bari in tambayi matar, da Bako da Tukura ai duk Umbutawa ne.” Ya tsaya gaban macen aku, ya ce, “Na zo in gaya muku ne don ku sani, za ni bin Mahmudu, duk abin da zai same shi ya same mu tare.”

Da akun nan ta ji haka sai duk ransa ya baci, ya harari aku ya ce, “Har ke dan tsugunin nan naki kin isa ki hana ni zuwa wurin dan’uwana? Karyarki ta sha karya!” Sai ya kama ta, ya murde kan, ya yar. Yana jefad da ita sai mijin ya farka. Musa ya juya wajensa, ya ce, “Kai kuma me ka ce?” Na zo in gaya muku ne zan bi Mahmudu yanzu.”

Da akun nan ya ji haka, sai ya dubi matar, ya ga abin da ya auku gare ta. To, ga shi Sarki ya bar masa amanar yaro, in ya bari ya fita, lalle ya ci amanar Sarki. Ya ga kuma in ya hana yaron nan tafiya, lalle abin da ya auku ga matarsa zai auku gare shi. Yana nan yana tunanin wadda za ta fisshe shi, sai Musa ya ce, “Ban ji ka ce kome ba, ko kuma kai hana nin za ka yi, yadda matarka ta tashi hana ni?”

Aku ya daga fiffike, ya duka, ya ce, “Mamakin abin da ya sa ka ba mace shawara na keyi Ai magana irin wannan sai mu tsakanimmu maza. In ba rashin hankalin mata ba, ina mutum zai ce za shi ga dan’uwansa, sa’an nan a hana shi? Yi maza ka tafi, kada ka ji tsoron kome.

Ba shakka dai ka cika dan kirki, tun da ba ka saba abin da tsohonka ya hore ka da shi ba, da ya ce kome za ka yi ka shawarce ni. Ga shi ka san ni ba kome ba ne, amma don ka cika umurnin ubanka ka zo. Da ma abin da a ke so ke nan kawai ga dan kirki ya bi maganar iyayensa da malumansa. Dan zaki da ya bi halin ‘ya’yayen zamani, ya ki bin maganar magabatansa, ai ka ga yadda ka kare.”

Musa ya ce, “Dan zaki? Wace magana ya ki bi? Su ma dabbobi suna wata magana ne?”

Aku ya ce, “A! Suna yin irin tasu mana. Bari ka ji yadda suka yi.”

 
{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.