Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu 



  Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane wani itacen baure a bakin wani rafi. Kullum suka tashi sai su nufi can su hau, su yi ta ci. Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani kunkuru. Kullum idan gaurakin na cin baure, wadansu ‘ya’yan su kan kucce musu su fado kasa. Da kunkuru ya ga suna fado masa yana ci, sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi kyauta, don suna sonsa. Saboda haka, da ya ga alherin ya yi yawa, ran nan sai ya daga kansa ya dubi gauraki, ya ce, “Kai ‘yan’uwana, ne gode! Kullum dai na kan ga ‘ya’yan bauren da ku ke sako mini. Abin maku ya yi yawa, wallahi har kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya saka da alheri!”

Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane abin da ke aukuwa. Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana ta. Ta dubi kunkuru ta ce, “Don mun ga kai ba ka yia hawowa, shi ya sa mu da Allah ya ba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar zumunci.”

Kunkuru ya ce, “Amin! Na ko yi godiya.” Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya. Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba su son abin da ya taba shi, shi kuma ba ya son abin da ya taba su.

Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare, gauraki suka koma neman kwadi da tana. Bayan kamar wata biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai duniya ruwa bai taba zama nan ba. Da gauraki suka ga haka, sai suka yi shawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda ke da danshi-danshi.

Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, “Ya kamata mu je mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, ya yi zaon wani abu ne ya same mu.” Suka tashi, suka tafi wajen kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura.

Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, “Af, to, ai ba ku barina, sai mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi ya yi Kaura. Ni ina na ke iya zama inda babu laima?”

Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, “Yaya za ka yi ka bi mu, alhali kuwa kai ba ka da fiffike?”

Kunkuru ya ce, “Sai ku dauke ni, in kun ga kwa iya kokarin hakanan.”

Babbar gaurakar ta ce, “Wa ka ke zato cikimmu zai yia daukar kato kamarka? To, ce ma muna iyawa, ina za a kama, ga ka jiki duk kwarya?”

Karamar ta ce, “Bar shi, mu ji tasa, watakila yana da dabara, Kin san an ce mai rai ba ya rasa kokari.”

Kunkuru ya ce, “I, ina kuwa da wata ‘yar gurguwar dabara, in tsakiyar, ku kuma kowace ta kama gefe guda da baki. Kun ga da haka sai ku tashi da ni har inda za ku.”

Babbar ta ce, “Wannan dabarar ban ga za ta yiwu ba ga kamarka, mai surutu.”

Karamar ta ce, “A’a, in ya ce dai ya iya kyalewa, sai sai mu dauke shi.”

[insert picture here bottom page 72]

Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi, ta ce, “To, don Allah in ka kama, ban da yawan magana.”

Kunkuru ya ce, “Haba, wannan ma sai an dankwafe ni kansa, sai ke ce yaro? In yi surutu mana, in ina so!”

Gauraki suka ce, “To, madalla!” Suka kama kara suka tashi da kunkuru yana cije.”

Suna cikin tafiya, sai hanya ta dauke su ta bisan kasuwa. Suna kaiwa tsakiyar, sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce “Eho, eho, ku zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai jama’a. abin mamaki ba ya karewa nan duniya!”

Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, “Kai, Allah ya tsine idandunan nan naku mutane, da ba su iya ganin abu su kyale.” Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya kawo kasa kum.

Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna cewa “Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba, lalle yana tare da halaka.”

[insert picture here middle page 73]

Musa ya saurara haka, sai ya ji wani daga cikin bayin nan na ta da ‘yan’uwansa, gari ya waye. Ya bata fuska. Aku ya ce, “Ai ko yau ba ka yi zaman banza ba, don na yi maka gargadi.”

Musa ya ce, “Gargado!”

Aku ya shiga shashatad da shi, har ya ‘ciwo kansa. Suka yini nan suna ‘yan tade-tade, aku “Yau, don Allah ba ka kyale ni in wuce baki alaikum?”

Aku ya ce, “Sai ka dawo.”

Musa ya ce, “Kai, yau wace rana ka kyale ni ba ka yi min wani surutu ba!” Ya sa mabudi ya bude zaure na farko ya taka zai shiga ya buda na biyu, aku ya biyo shi, ya ce, “Yanzu wani babban abu ya fado mini a rai. Kwankai na ba ka maganin karfe, na manta ban ba ka kau da bara ba. Ko kuwa ba ka so ka iya gociya?”

Musa ya ce, “Ban iya gociya ba, in kau da baran na kusa ka kawo mini. Ba wanda ya ki taimako.”

Aku ya ce, “Wani kauci ne nan kusa, bari in fita in kawo maka.” Ya fita fir ta taga.

Musa ya ce, “In kana wa Allah, ka yi sauri!”

Aku ya ce, “Shi babba.” Ya tafi ya sami wani lambu, ya yi ta satar baure yana ci. Da koshi, ya ga kamar asalatu ta yi, ashe farin wata ne, ya debo ganyen bauren ya taho, ya ce wa Musa, “Ga shi, ka sami saki ka dinke shi da shi, ka gama cikin damarunka, ko ana ruwan kibau, ka tabbata ba dayar da za ta same ka. Amma da sharadi guda, ya kamata ka koyi gociya, domin kau da bara duk ba ta ci sai ana gamawa da ‘yan zuke-zuke.”

Musa ya ce, “To, madalla.” Ya bude zaure na biyu, aku ya dubi gavas ya gani ko asalatu ya yi, ya ga ashe bai yi ba, farin wata ne ya rudo shi ya dawo da wuri. Sai ya tashi da ‘yan tsalle-tsalle yana bin Musa, ya tarad da shi har ya bude zaure na uku, ya ce, “Bari in gaya maka wani labari mai dadi. Wata rana akwai wadansu ‘yam makaranta…”

Musa ya ce, “Kai tafi ka ba ni wuri! Ni na gaji da labarun nan naka.” Ya bude zaure na hudu.

Aku ya yi tsalle ya bi shi, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ni dai wallahi kana kayatad da ni, tun da ba ka wuce maganar iyayenka ba. Dubi abin da Sarki ya gargade ka da ni, ka ga har Allah ya kawo mu rana wa ta jiya kana nan rike da abin nan da ya ce.”

Musa ya waiwayo ya ce, “Rana wa ta jiya kadai, ranar yau fa?”

Aku ya ce, “Ai kullum kana rike, da ma dai ai--.”

 

 

Koma Baya



{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.