Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Munafuncin Dodo, Ya Kan Ci Mai Shi 


  Wata rana wani bakauye wai shi Kado ya dauki gatarinsa, ya shiga daji zai yiwo itace. Dawan nan kuwa da ‘yam fashi, mutanen dan kauyen nan duk sun san da su. Can bakauyen nan ya yi nisa cikin daji, sai ya hango wani abu tsibe yana daukar ido, ya matsa ya ga ko mene ne, sai ya tarad da sulalla ne tsibe. Ya waiwaya baya, ya waiwaya gaba, bai ga kowa ba. Sai ya duka ya cika aljihun taguwarsa fal, ya saba gatarinsa, ya sheka da gudu ya nufi gida.

Ya rabu da wajen da ya debi kudin nan ke nan, sai ya gamu da ‘yam fashi su uku. Suka ce masa, “Kai, tsaya! Me ya koro ka?”

Kado ya tirje yana kaduwa,yana tsammani kudin nan da ya debo nasu ne. Sai ya c, “Iye! Ni? Na’am. Mutuwa ce na gani a fili, shi ya sa na ke gudu.”

‘Yam fashin nan suka yi dariya, suka ce, “Mutuwar da kanta ka gani, ko kuwa maciji dai?”

Kado ya ce, “Iye! Ni wallahi mutuwar ce da kanta na gani a can tsibe, shi ya sa ban ko tsaya wurin ba, don kada a ce na gan ta, na sheko da gudu.”

Da ‘yam fashi suka ga lalle ya tsorata da su, sai suka ce masa, “To, mu je, ka kai mu mu gan ta mu ma.”

Kado ya wuce gaba suna biye, har wajen da kudin nan su ke. Ya ce, “Ga ta! Na rantse da Allah kuwa ban diba ba, kada ku ce ko na diba ne.” Yana boye-boyen aljihu yana tsammani ajiyarsu ce, shi ya sa ya kara rudewa haka.

Da Allah ya sa ba su dubi aljihunsa ba sai suka ce, “To, tafi. In ka fadi kuwa, muna zuwa da dare mu yanka ka.”

Ko da Kado ya ji haka sai ya ranta cikin na kare, bai zame ba sai gida. Ya kai yana haki, kamar ransa zai fita. Ya boye kudinsa, ya kama bakinsa ya tsuke.

Da ‘yam fashin nan suka ga ya wuce, sai suka yi ta mamakin kudin nan, suka ce, “Watakila wadansu barayi ne suka sato, da suka ga sun yi musu yawa suka zubad da sashi nan. Allah Sarki! Bakauyen nan fa tsammani ya ke, namu ne.”

Babbansu ya ce, “Kai, ai ko ya firgita. Yanzu fa ya dade da kaiwa gida.”

Sauran suka ce, “Haba, tuni. Sa’ad da ya garzayan nan, ai ko mota ba ta kamo shi.” Suka bushe da dariya.

Sai babban ya dauki sule guda ya ba karamin, ya ce, “Ruga maza kasuwa ka sawo mana abinci mu ci tukun, idanummu su bude, sa’an nan mu san yada za mu yi kasafin wannan kudi.”

Karamin ya karba, ya sa riga kamar ba barawa ba, ya yi nadi, ya tafi kasuwa, ya nufi wajen mai tuwo, ya sayo, ya kuma biya mahauta, ya sayo musu tsire ya dora kan tuwon, ya dauko ya nufo daji. Yana kulle-lullen abin da zai aikata da kudin nan, da nasa ne shi kadai. Sai ya ga itacen tinya, ya ajiye kayansu, ya ce, “Alhamdu lillahi! Bari in debi ruwan tinya in zuba wa abincin nan, in kai musu. Ni kuwa ko sun ce in ci, sai in ce na ciwo daga kasuwa. Ka ga da suri ci duk sai su mace, ni kuwa in kwashe karfena, in shiga gari in yi ta kece raini.” Ya karya tinya ya zuba.

Shi kuma ashe kafin ya dawo ‘yan’uwansa sun yi shawara da ya zo su kashe shi, su kwashe kudi, su raba su kadai. Suka ce ai haka abin ya fi auki.

Can sai wannan karamin ya iso da kayan abinci. Ko da ajewarsa sai suka hau masa da bugu, bai san hawa ba, bai san sauka ba, suka kashe shi. Suka fada abinci da ci, in sun gama sa’an nan su kwashe kudi su san inda suka nufa. Da gama cinye abinci, sai kowanensu ya fara kaduwa, yana faduwa yana tashi, kafin kiftawa da bismilla duk suka kai takarda.

Can bayan kamar kwana bakwai sai Kado ya ce a ransa, “Bari in koma wurin nan, in na tarar suna kwashe kudinsu in tsuguna in yi kala, ko Allah ya ba ni dan taro. In kuwa na tarad da su sai in ce na zo ne in gaya musu Sarki zai aiko da dogarai a kama su gobe, abin da ya fi kowa ya yi ta kansa. In ce kuma abin da ya sa na gaya musu don haka, sun ji kaina ne ran nan. Ka ga watakila ma sa ba ni dan sule. Kudin dai ga su nan tsibe kamar ba su so, ba su da alamar karewa.”

Da isarsa wurin sai ya tarad da su duk sun mutu. Ya yi juyayin abin da ya kashe su, ya rasa. Da ya lura har kuraye sun ci su, sai ya yi zaton su ne suka kashe su. Ya rasa abin da zai yi don murna. Ya shimfida gwadonsa, ya kwasa. Ya yi ‘yan kirare ya dora, don kada a gane, ya kai gida, ya gina rami ya binne. Magariba na yi kuma ya kira dansa, suka tafi suka kwashe saura. Ya zauna ya yi ta cin kudinsa sannu kan hankali, da shi da dansa, ba wanda ya gane.

Musa ya bingire da dariya, ya ce, “Allah mai girma! In rabo ya rantse, sai mai shi!”


Ya Saurara haka sai ya ji kiran salla, ya ce wa aku, “Wancan kiran sallan fa, na fari ne, ko na biyu?”

Aku ya ce, “Sai, dai na fari. Amma bari mu ji.” Sun yi shiru suna saurare, sai suka ji ladani ya ce, “Assalatu!”

Musa ya ce, “Subuhana lillahi, ashe har gari ya waye ba mu sani ba!” Sai ya tashi fuu ya shiga cikin gida. Tun safiyan nan har magariba bai sa ko loma bakinsa ba don bakin ciki.

Ko da wata ya fadi, tun ba a ko yi kiran sallar asuba ba sai ga Musa ya shiryo. Ya zo ya ce wa aku, “Sai na dawo.”

Aku ya ce, “Ka dawo lafiya.” Ya sake duban Musa, ya ce, “A! Kam ba Waziri ba, a dubi kakkarfan dan Sarki kamarka a ce za a hana shi zuwa yaki? Shin halin Waziri wane iri ne?”

Musa ya ce, “Rabu da shi tsohon wofi! Ko da ya hana, ai ga shi yanzu za ni yana gani.”

Aku ya ce, “Tafi abinka, rabu da shi! Kome mutum ke aikatawa dai ai, kul ba jima, kul ba dade, ya ga sakayya. Da Allah ya sa ya ji labarin Hafaru da dansa, da ya rage wadansu abubuwa.”

Musa ya ce, “Wane labari ne na Hafaru da dansa? Gaya mini, ko ni ma in karu.” Aku ya ce.

 

 

 

Koma Baya


{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.