Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Labarin Sahoro Da Sahorama  


  Wai akwai wani saurayi ne wanda a ke kira Sahoro. Kullum ba ya tabuka wani aiki sai ya kora akuyarsa, ya kai ta bakin rafi ta yi kiwo, da maraice ya kwanto ta. Nonon akuyan nan shi ne abincinsa, ko ya sayar ya sayi wani abu, ko ya sha hakanan. In akuyar ta yaye kuwa, sai ya sayar da ita, ya sayi wata mai da.

To, ba abin da ya miskile shi sai kiwon akuyan nan. Kullum ya dawo gida sai ya ce, “Wash, ba shakka kiwon akuya ba aikin da ya sha kansa kan wahala! Haba, lokacin nan yanzu akwai abin da ya fi mutum ya sami inuwa mai sanyi, ya kishingida, ya yi ta barci? Amma ba dama, dole ne mutum ya bi ta, in ko ya ki, ta fada wata gona ta shirga barna a ci mutum tara, ko kuwa ta ki dawowa kura ta sami kalaci. Kai, ya kamata dai in tuna yadda zan sanyaya wa raina daga wannan azaba. Rai fa an ce dangin goro ne, ban iska ya ke so.”

Yana nan kullum yana zulumin wahalar kiwo, sai ran nan ya ce, “Ah! Na san dabara, ba abin da ya fi sai in auri Sahorama. Ga ta da akuya daya ita kuma tana kiwo, ka ga in na aure ta sai ta rika gamawa da tawa, ni ko I samu in rika taba dan kailula.”

Sai ya nemi Sahorama aure. Iyayenta suka ce, “Am ba ka. Da ma Tukura da Bako duk Umbutawa ne.”

Aka yi aure, ta tare, ta shiga hidimar kiwon awakinsu biyu. Don ba su da wani abinci sai wanda suka samu daga gare su. Sahoro ya yi ta shara barci a natse.

Ba a dade ba kuma Sahoroma ta ce wa Sahoro, “maigida, ni fa ga gaji da wannan irin wahala, kudaje na cizona, ina tuntube. Don Allah, dubi jikina. Da na zo nan gidanka ina sheki, duk yanzu na fara kirci don cizon kudaje. Kai, ba na yarda in tsofad da kaina tun ina gabar kuruciya, sai mu sake dabara.”

Sahoro ya ce, “Wannan batu naki ba makankara. Ni ma fa na ga kin fara baki, ni ko dubi yadda na fara ajiye taiba. To, yaya zan yi da su?”

Sahorama ta ce, “Sai mu ba Dabo, ya ba mu amiya guda, mu ajiye a bayan gida, in zuma ta shiga ta yi saka, mu rika diba muna samun abinci. Ka ga ba ruwammu da kiwonsu, balle mu wahala.”

Sahoro ya ce, “Kai, ai ko kin samo dabara, ga shi kuma ko ba a fadi ba zuma ta fi nono dadi.” Sai ya sa matar ta je ta yi magana da Dabo. Ya yarda da musayar, don ya ga da riba. Ya ba su amiya guda, suka yi ta samun zuma daga ciki suna sha. Suka sami wani gora suka cika, suka rataye.

Sahoro dai in ya kwanta tun da dare, ba ya tashi sai rana ta take. Ya kan ce wai tashi da wuri shi kan hana gira tofo, kuma ya kan sa dundumi. Ran nan ya farka daga barci da rana tsaka, sai ya ga matarsa ta dauko goran zuman nan, za ta diba ta yi musu ta fi ku! Dubi goran zuman nan har ya kusa karewa. Watau zuman nan ta kare ne, har za ki fara dibar ta gora? Abin da nu ga rika yi mana kwai suna kyankyashewa.”

Sahorama ta ce, “In ko haka ne sai mu sami yani yaro wanda zai rika zuba musu ruwa da hatsi. Ni dai ba na iya wannan jidali kullum kwanan duniya.”

Sahoro ya ce, “Lalle kiwon kaji wahala ne ja wur. Yaran yanzu kuwa kowa ya san su a kan ragwanci. Yanzu ko, ko mun yayo wani yaro don ya rika lura da kajin, in mun saya sai ki ga wasa ya dauke masa hankali, ba ya wani abin kirki.”

Sahorama ta ce, “Ko wane yaro muka dauko in ya ki yin aiki sai in dauki sandan nan” (ta sa hannu ta dauke wani guntun itace), fashe, ‘yar zumar da su ke takama da ita ta tsiyaye.

Sahoro ya ce, “Shi ke nan, ta faru ta kare, an yi wa mai dami

daya sata! Da kijin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba.” Ya dubi matar, ya ce, “Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse barcina tun ban koshi da shi ba.”

Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin labari tana cewa, “Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, “Ba kome, sauri shi ke haihuwar nawa!”

Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma da wayo, tana zuba masa suruntun banza. Sai haushi ya kama shi, ya ce mata, “Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba dindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai kin nemi yaro, Mutuniyar banza, sullutuwa!”

Sahoro yana dai daga kwance ya ce, “Wa ki ke zagi, Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!”

Sahorama ta ce, “An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba. In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!”

Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko, ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya gaaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da kasa. Sai ya ce mata, “To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta ke nan?”

Sahorama ta ce, “Af! To, in sake ka, ni in fadi?”

Musa ya ce, “Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. To, kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da wadansu ‘yam birini?

Aku ya ce, ‘Wannan shi ma yana da ban dariya.”

 

 

Koma Baya


{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.