Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Labarin Sarkin Busa  


  Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala’i. Aka saukar musu da beraye ko’ina cikin garin. Berayen nan suka yi ta karuwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum ya duba garin ba ya ganin kome sai beraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuku-tuku suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da beraye. In takaice maka labari, yawansu ba su kidayuwa. In da za ka kidaya su, ka kidaya kudajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan kudanjen nan kamar sau dari. Gari dai ba wajen sa kafa, duk beraye ne.

Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye.

Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su kwace shi.

In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da guje-guje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kasha su. Bala’I sai sa’ad da Mai abu ya sawwake abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin Karfi. Don kyanwa kuwa, wannan karamar alhaki, ba su kula da ita ba.

Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kasha su, sai ka ga kamar kara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rudinsu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi.

Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka halicci duniya ba su taba jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da berayen nan, ko kuea su fitad da shi, su kore shi daga kasar.

Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai kara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wadannan dattijai su zo su zazzage shi su wuce, wadannan su zo su zunzungure shi su wuce. Sai ga wani dan tsoho bako ya zo, ya duka ya gai da Sarki.

Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, “Malam, daga ina? Wace sana’a ka ke yi?”

Tsoho ya ce, “Ga ni dai. Inda na fita da nisa, amma sana’ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa.”

Sarki ya ce, “To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala’i.”

Sarkin Busa ya ce, “Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwadi, da macizai, da beraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wadannan ‘yan berayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su?”

Sarkin ya dube shi, ya ce, “Yau ga abin mamaki, mene ne sule dari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala’i.”

Sarkin Busa ya ce, “To, madalla.” Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai berayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wadansu manya, wadansu kanana, wadansu tultul, wadansu kyamas-kyamas. Ga wadansu ja wur, wadansu fari fat, abin har da shudda da rawaya. Ka ga wadansu ruku-ruku da ciki wadansu suna ‘yan kuka tsui tsui, kamar suna fara’a da wata bushara.

Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fada cikin ruwa yana busa, beraye kuma ba su san sa’ad da suka bi shi ba, yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fadi farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa da wannan bala’I, ya zama kauyanci.

Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun bace, balle a ce wani makirci aka kulla da shi.

Da uban yaron nan mai dingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo dansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, “Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dad’ na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nu-nu mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bakin ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dadinsu, ni ina nan.”

Beran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wadansu yana cewa, “Ba ku sani ba, na yi daron cin dadi. A can ketaren banza, ga nama. Ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a taba sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, karamar alhaki. Zan isa, saura kadan, sai na ji na fada cikin ruwa. Yanzu ‘yan’uwana na can sun yi kiba ni rashin sa’a ya sa ni na tabe!”

Saura suka yi ta cewa, “Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan kasar, ya tafi da mu mu ma!”

Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko sami labarin ya bulla wani wuri da ‘ya’yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana.

Manyan gari suka ce, “Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun taba ko jin inda irin wadannan al’amura suka faru?”

Saura suka ce, “A’a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu.”

Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Ilyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kudi da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya.

[insert picture here, lower right-page 86]

Ka ji abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa. Musa ya duba ya ga wuri ya yi haske, ashe har rana ta fito ba su sani ba. Sai ya ce wa aku, “Na ji abin da ke aukuwa ga mai alkawari ba ya cikawa. To, me ke faruwa ga irinku masu hana a cika alkawari? Bai tsaya garin jiran amsa ba, sai ya shiga gida a fusace.

Da azahar ta yi Waziri ya kira tsohuwan nan ya yi mata kwando goma na zagi, don har yanzu ta kasa dabarar da za ta yi tfito da Musa. Tsohuwan nan ta ce, “Kullum ina kokari, wani dan aku gare shi mai tsai da shi da labaru ko yaushe har gari ya waye.”

Waziri ya tashi ya mangare ta, ya ce, “Tun da ba ki da wata dabarar da za ki wayace dan tsuntsu, tafi, yau na sa wani.” Sai ya kira bawansa Barakai, wannan da ya aika wajen Sarkin Sinari kwanan baya, ya gaya masa abin da ya ke so, da kuma yadda aku ke hana Musa zuwa da labaru.

Barakai ya yi shiri irin na mata, ya tafi gidan Sarki, ya tarad da Musa inda tsohuwan nan ta yi masa kwatanci. Ya yi masa maganar Mahmudu na can rai ga Allah, ya ce wai Mahmudu ya ce a gaya masa, tun da ba ya kaunar zuwa su gana, shi ma ko lahira kada Allah ya gama su. Musa ya fashe da kuka, ya ce, “Kullum ina so in tafi, dan akun nan ke tsaishe ni da labari. Ga ko Sarki ya ce in na yi wani abu ba da na shawarce shi ba, bai yarda mini ba duniya da lahira.”

Barakai ya ce, “Don dai wannan dan tsuntsu, yau ka tafi. Nan zan kwana, da mun ji bayin nan sun yi barci mu je tare ka salami akun, in hana shi ya tsai da kai.”

Musa ya ce, “Da kin kyauta.” {Don yana tsammani mace ce.) Suka zauna nan, har barci ya share bayin da ke saure. Suka tashi suka nufi wajen aku.

Ko da aku ya hango su tafe su biyu, sai ya gane Barakai namiji magana, ya riga su ya ce, “Don Allah, yallabai, yau ka tafi. Ni ba na iya ba ka wani labari. Duk inda ka ke son zuwa, ka tafi.”

Barakai da dubi aku, ya ce, “Ko ba ka ce ba, da ma yau ba mu son wani labari naka.”

Aku ya langabe kai kurum, sai tausayi ya kama Musa, ya ce masa, “Me ya same ka yau?”

Aku ya ce, “Tunani na ke yi.”

Da ya ke Musa ba ya son ya yi wa akun nan abin da zai motsa masa rai, sai ya tambaye shi tunanin da ya ke yi. Aku ya ce, “Ina ya tara five da abin da Allah ya ba shi.”

Musa ya ce, “Wannan masassaki ya ja wa kansa halaka.”

Aku ya ce, “Da ma ka ji abin da ya same shi, ai da ka san lalacewar ba ta da iyaka.” Bai tsaya a ko ce ya fadi ba, sai ya fara.

 

 

 

Koma Baya


{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.