Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Sauri Ya Haifi Nawa 



  An yi wani Sarki nan arewa wanda ke da dan auta da ba a taba ganin kyakkyawa irinsa ba. Da fari dai ga shi, shi bai cika kyamushewa ba, shi kuwa ba kakkaura ba hakanan. Wuyan nan nasa sai ka ce goran nono, idanunsa ko fari fat sai ka ce madara. Gashin kansa ma abin kallo ne, don sai ka ce mai ya ke shafa masa. In ko har ya yi dariya ka ga hakoran nan, wayyo Allah! Kafafunsa kuwa—

Musa ya ce wa aku, “Kai don Allah in za ka ba mu labari ka ba mu mu sha, in ko ba ka ba mu, ka kyale mu kowa ya san abin da ya kama.”

Aku ya ce, “A’aha! A bar ni in gyara labarina yadda zai yi dadi.”

Wata rana Sarkin nan ya hau duk da mutanensa, don ya kewaya kasarsa ya buga musu haraji. Suna cikin tafiya sai autansa ya janye wani baransa, suka rika ja da baya. Suna son a wuce su kama labarin duniya. Ko da suka ga rundunar Sarki ta bace, sai suka yi ta tadinsa suna kakkawa suna tafawa. Suna cikin haka sai suka isa wani dan kauye wanda Sarki ya wuce tuni. Da suka ga azahar ta yi sai suka sauka, don su yi salla. Baran nan ya tafi gidan mai garin ya gaya masa ga dan Sarki nan zai yi salla a garinsa.

Da bayin nan na Waziri suka ga ga shi har asuba ta yi Musa bai ko motsa ba, balle su sami damar gama masa aiki, sai suka sake shawara, wani daga cikinsu ya zo ya durkusa gaban Musa kamar mace, ya ce, “Ana kira ciki.”

Musa na tsammani baiwarsa ce, sai ya ce, “Je ki, ina tafe,” ya koma, Aku ya ci gaba da labarin da ya ke bayarwa, ya yi ta jansa, don kada ya kare gari bai waye ba Musa ya ce zai tashi.

Da baran ya wuce, sai ga wata yarinya kamar ‘yar Labarawa ta fito daga wani gida kusa da masallaci. Tana leko kai sai duk wurin ya haske, in ka dube ta sai ka yi tsammani ba ta cin abinci don ba alamar ciki. Jikin nan nata kuwa na rantse har da girmanka, yallabai, kamar in ka duba za ka ga bargo. Hancinta kosaika ce ita ta yi wa kanta. In da ka dubi idanuntasai ka rantse da Allah ba ta kifitawa, Gashi ko—Muse ya ce, “Kai, ya isa hakanan. Ci gaba da labari, ka ji ana kirana gida.”

Aku ya ce, “Ina zuwa.” Ya yi ta tsawaita shi:

Dan Sarkin nan ya ta da kai, ya dub ta tun daga kasa har sama, sai ya ce a ransa, “An ce dan Adam duk bai cika goma ba, to, yau ga wadda ta kai goma sha biyu.”

Ya kara dubanta ya ce, “Yam mata, daga ina?”

Ta ce, “Daga Waila Fadama. Mun zo biki ne nan jiya, yanzu kowa da azaharin nan za mu koma.”

Dan Sarki ya yi mamaki, ya ce, “A Waila Fadama? Wane gida ki ke kuwa har ban sani ba?”

Ta ce, “Nan gidan mai garin. Ai ni ce babbar ‘yarsa. Ba na fita ne, daga biki sai salla, shi ya sa ba ka san ni ba. Amma ka ga, ni kuwa na san ka. Ko kai ma ba ka rasa jin labarin Nana Yauki ta Waila Fadama ba.”

Dan Sarki ya yi shiru, ya ce, “Wallahi kuwa, na ji ana labarinta.”

Ta ce, “To, ai ni ce.”

Da dan Sarkin ya ji haka sai ya takale ta da maganar aure, ya ga alamar lalle tana sonsa. Wancan mijin da za a ba ta wai dattijo ne mai gemu, ita kuwa ta ce ba ta auren mai gemu.

Bayan sun shirya da ita a nan sai ta tafi. Ya dauki buta a masallaci ya yi alwala, ya shiga ya yi salla. Da yai sallama, ya yi addu’a ga Fiyayyen taliki ya nufa Allah ya sa ya auri wannan yarinya. Don dokin bukatar auren yarinyan nan har ya yi subul a baka ya ce wai in Allah ya nufa ya aure ta ya kashe kansa don murna.

Bayan ya fito daga masallaci sai ya tarad da mai garin ya kawo masa sauka. Suka gaisa, ya hau, suka mika da baransa. Suka bi Sarki har suka iske su. Yana tafe yana ba baran nan labarin yarinyar.

Da aka kare kewayar kasa aka koma gida. Sai dan Sarkin nan ya gaya wa Wazari yana son su neman masa ‘yar Sarkin Waila Fadama da aure. Waziri ya gaya wa Sarki.

Aka neman masa, aka ba shi. Aka yi biki aka kare.

Bayan sun yi kamar shekara uku da auren, sai ran nan Nana ta ce tana son mijin ya raka ta ta gano gida. Dan Sarki ya gaya wa ubansa, uban ya yarda. Ya sa wani babban bawansa ya raka su, aka yi musu shiri, suka hau rakuma suka tafi.

Suna cikin tafiya har suka kai garin da dan Sarkin ya fara ganin Nana, suka yi zancen aure, suka tsaya kusa da masallacin, don ya yi alwala ya yi sallar azahar. Ko da ya shiga ya gama salla zai fara tasbaha, sai ya ji kamar daga bisa an ce masa, “Ina alkawarin da ka dauka, da ka ce in Allah ya nufa ka auri Nana za ka kashe kanka don murna da godiya ga Ubangiji?”

Da dan Darki ya ji haka, sai ya tuna da alkawarin nan da ya yi. Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga mai magana da shi ba, sai jinkinsa ya dauki rawa, ya yi salati, ya ce, “Lalle baki shi kan yanka wuya!” Sai ya zare takobi, nan ya fille kansa. Ya fadi ya mutu.

Da aku ya kawo nan sai suka ji assalatu. Wani daga cikin bayin Waziri ya yi maza ya sake zuwa ya durkusa gaban Musa, ya ce, “Ana kiranka maza maza ciki.”

Musa ya ce, “Haba, su sai su dami mutum da kira. Ins kika ga zan iya tashi ban ji karshen wannan labari mai dadi ba? In wani abu a ke so, Sarkin Gida, je ka ka gani.”

Da bawan nan ya ga Sarkin Gida zai biyo shi sai ya ce, “A’a zauna abinka, Sarkin Gida, shi a ke nema. In ba ya zuwa, bari in je in gaya musu.” Sai ya koma ya gaya wa ‘yan’uwansa, suka yi waje da sauri, suna wa juna barki da Sarkin Gida bai biyo ba, da yau sun bakunci lahira. Suka tafi suka gaya wa Waziri abin da ya faru. Waziri ya ce ku koma su sake kokari, zai kara musu fam goma goma. Suka sake shiga irin ta maza, suka komo. Duk gari an tashi, har rana ta kunno, aku kuwa sai jan labarinsa, ya ke yi.

Da Nana ta ga ya dade bai fito ba, sai ta ce wa bawan nan ya shiga ya gani wane irin dogon wurdi ya kama, har yanzu bai gama ba. Da shigarsa sai ya tarad da shi kwance male-male cikin jini, ba kai, ga tokobi can gefe yashe. Ya dafe kai, ya yi salati, ya ce, “Yanzu in na fita na fadi abin da ya faru, lalle za a ce ni na kashe shi, Ban ga wata hanya ba sai in kashe kaina nan tare da shi, in an ga hakak a san lalle sai da na yi kokarina har na kasa, abin ya faru haka.” Sai ya dauki takobin nan ya fille kansa. Ya fadi gefe daya ya mutu.

Nana tana waje tana jira. Shiru shiru, ba ta ga wani ya fito ba, ta ce, “kai yau fa ga inda na yi ma’aikin kibiya. Abin nan lafiya dai?”

To kara hakuri dai har la’asar ta yi sakalliya, sa’an nan ta ce, “ko da mata ba sa shiga masallaci, lalla ni in je in ga abin da ya auki.”

Sai ta sauka, ta kutsa kai cikin masallaci. Da shigarta sai ta ga mijinta da bawansa duk ba kawuna. Ta ja da baya, ta yi dan ta yi nan, ta fadi ta yi ta kuka. Da ta ga dai kuka ba ya magani, sai ta dauki takobi, ta ce, “Bari ni ma dai in kashe kaina, In huta da wannan bakin cikin, raina dai ba shi da amfani gare ni muddin mijin nan nawa ba ya numfashi.”

Ta cira takobi za ta sare kanta, sai ta ji an ce, “Tsaya. Dauki kawunansu ki lillika musa, duk sai su tashi.”

Ta duba gabas, ta duba yamma, ba ta ga wanda ya yi mata magana ba. Sai ta tashi da rawar jiki, ta dauki kawunan ta lillika jikunansu.

Ashe cikin dokin ta ga mijinta ya tashi har ta kidima ta dauki kan da Sarki ta lika wa jikin bawan, ta dauki kan bawa ta lika wa jikin dan Sarki. Sai suka tashi, dan Sarki da kan bawa, bawa da kan dan Sarki! Kowane da mikewarsa sai ya rungume ta, ya ce matarsa ce.

To, jama’a, wa kuka gani ke da mata?

Bayi suka tashi da gardama haya haya, haya haya, wadansu na cewa mata ta kan dan Sarki ce, wadansu na cea a’a, mata ta gangar jiki ce.

Suna cikin gardamar, ga bayin Waziri tsaye bakin zaure, ba wanda ya san abin da su ke jira sai aku. Sai aka ji tambura Sarki ya tinkaro. Kafin a yi haka, kofar fada ta fara daukar ‘yam bushara.

Bayin Waziri da suka ga ba dama, suka koma suka gaya wa Waziri, ya yi ta cizon hannu don bakin ciki. Jim kadan Sarki ya kawo, Mahmudu na gaba maroka sun daho shi, sai kirari a ke masa ana yi masa waka.

Mahmudu, jimre ka dau himma,

Sai an gwada za a san babba.

Zama ga daki na raggo ne.

Wan Musa, taso mu je gaba.

Mai son fada, duk ya zo nana,

Gun Mahmudu, yanzu ya bar wasa.

Sinari bana sun tabo wahala,

Wan Musa Allah ya jaya ma!

Sakaci da tsoro ka yashe su,

Duniyag ga ba tai mai wauta.

Sinari sun tuba, sun bi ka,

Sarkinsu ya zo, ka gafarta.

Kyaun saurayi duk a dau mashi,

Don shi da mata a bambanta.

Ayyururui! Mutane, mu dau guda,

Mahmudu da mai kamar baba.

Allah ka dube mu kai rahama,

Allah ka dube mu kai rahama.

Allah ka dube mu kai rahama,

Ka ji kan mahaifa, mu ce amin!

Da suka iso duk gari aka dauki alo alo. Musa ya tafi ya taryi Mahmudu a kofar gida, ya rungume shi, suka yi ta murna. Ya tambaye shi kwana nawa ya yi yana jiyya, ya ce shi ko kaya ba ta taba sukarsa ba tun fitarsa, balle ya yi jiyya. Musa ya yi ta mamaki. Ya tambaye shi batun takardar da ya sha yiwowa, ya ce shi bai aiko kowa ba. Musa ya tafi dauko takarda, ya tarar ba ko daya, ashe duk aku ya kwashe su ya boye.

Waziri ya zo yana ‘yan dararraku, wai shi yana murna. Da aka natsa, aku ya ce wa Musa, “Na ji kana neman takardun da Mahmudu ya aiko maka sa’ad da su ke wajen yaki, ai suna nan na ajiye maka.” Ya tafi ya dauko ya kawo musu, suka yi ta karantawa suna tu’ajjibi, suka boye takardun suka kyale.

Da gari ya waye, sai suka dauki takardun nan suka kai wa Sarki. Ya duba, ya ce, “Wannan ai hannun Waziri ne.”

Mahmudu ya ce, “Hannun Waziri! Karanta ta ka ji.”

Sarki ya karanta takarda, sai ya rike baki, ya ce, “Me ya ke nufi da wadannan?” Ya juya ga Musa ya tambaye shi yadda aka fara, har aka aiko masa da wadannan takardu.

Musa ya ce shi bai san abin da a ke ciki ba, tsammani ya ke Mahmudu ke aiko da su. Ya kwashe abin da aka fara aikowa, da dukan abubuwan da suka auku, da yadda aku ya yi ta rudinsa da labaru har bai sami fita ba, duk ya fada wa Sarki.

Da Sarki ya ji haka, ya ce, “Ba shakka akwai magana. A kira aku.” Na da nan aka zo da shi, Sarki ya tambaye shi. Aku ya zauna ya kwashe yadda aka yi duka har da abin da suka yi da Waziri sa’ad da ya aiko a je da shi,da labarin bayin nan da a ke aikowa suna yiwo shirin mata suna zuwa, da abin da ya faru daren da Sarki zai dawo, har ya sa suka komo cikin bayin da aka bari tsaro ya rika ba su labari don kada su yi barci, da yadda ya yi ta fama da Musa don kada ya fita, duk ya fadi.

Da Sarki ya ji wannan abu, sai hawaye suka zubo masa don tsausayin aku, ya dauke shi ya rungume, yana cewa. Yaya za mu yi mu fito wa wannan a;’amari?”

Aku ya ce, “Duk wadanda a ke aikowa, ko ina suka shiga, in na gan su na gane su. Bari in kewaya wajengidan Waziri in na ga daya daga cikinsu a kira shi ya zo, in an matsa masa ya fadi abin da suka yi niyya. Da zan sami ganin wata tsohuwa da ta fara zuwa, da ta fi bayyana abin sosai.” Sai wani bawa ya sa shi a wuya, suka yi ta yawo unguwar Waziri, da wadansu katta uku kuma suna biye. Suna kawowa kofar wata ‘yar rusasshiyar bukka, sai aku ya kela cikin bukkar, ya ce, “Ga ta!”

Kattan nan da ke biye suka kutsa kai ciki, suka jawo ta, suka iza keyata har gaban Sarki. Da Musa ya gan ta ya ce, “I, lalle ko ita ce, wannan aku abin nana sai a yi shiru.”

Sarki ya tambaye ta abin da Waziri ya tashi kullawa game da Musa. Tsohuwa ta gigice, ta ce, “Iye, na’am! Allah ya ba ka nasara, wallahi tilasta ni ya yi.”

Mahmudu ya mike, ya dube ta ya kashe ta da mari, ya ce, “Sarki ke tambayarki, ki gaya masa abin da aka tilasta ki yi.”

Tsohuwa ta durkusa, ta fede wa Srki biri har wutsiya. Da Sarki ya ji haka sai ya aika duk dogarawansa suka zo ya ce, ‘Ku je ku kamo mini Waziri!” Dogarawa suka ruga.

To, ashe tun sa’ad da aka kama tsohuwah nan wani ya tafi wurin Waziri, ya ce, “Ranka ya dade, na ga wadansu bayin Sarki guda uku da wani aku sun zo sun kama tsohuwar baiwarka ta nan bayan gida, ko lafiya?”

Da Waziri ya ji haka, sai ya ce, “Lafiya mana.” Bai sake wata magana ba, sai ya shiga gida, ya sa aka daura masa sirdi, ko rawani bai tsaya nema ba, balle bara. Sai ya hau, ya sulale ta bayan gida ya fita gari, ba wanda ya gan shi.

Da dogarwa suka zo, suka fada cikin gida suka tarad da Jakadiya, suka ce, “Ina Waziri?”

Jakadiya ta ce, “lafiya, har cikin gida ba sallama?”

Dogarawa suka iza ta, suka ce, “Je ki, ki yi mana iso.”

Jakadiya ta shiga cikin gida. Jim kadan ta fito, ta ce, “Ai ba ya nan.” Dogarawa suna tsammani karya ta ke yi suka bazu cikin gida, wadansu suka tsare kofar zaure. Da suka yi nema ba su same shi ba, suka kama duk bayin gidan suka kai wa Sarki, suka ce ba su ga Waziri ba.

Sarki ya ce, “Ya gudu ne.” Ya sa ‘Yan Doka su hau su bazu ko’ina, duk inda suka same shi su kamo shi.

Aku ya dubi bayin nan na Waziri da aka zo da su, ya ce, “Ranka ya dade, ga ko shaidu da suka san abin da aka yi.”

Sarki ya ce, ‘Ka san su?”

Aku ya ce,, “Na san bakwai daga cikinsu, har ma ga wanda aka aika gun Sarki Sinari.”

Sarki ya ce, “To, nuna mini su.”

Aku ya tashi ya ce wa wani dogari, “Da wannan da wannan, kai su nan. Wadannan, ku ku komo nan. Kai, wancan da ke noke kai, komo cikin wadannan.” Ya dubi Sarki, ya ce, “Ga su Wadannan, su aka ce su boye nan kofar gida in Musa ya fito su kashe shi. Wadannan, su suka wo shirin mata suka zo shekaranijya, daren da za ka dawo. Wannan ko,” (ya nuna Barakai) “shi ne babban munafukin, shi aka fara aika wurin Sarkin Sinari ya nuna musu hanya. Shi kuma ne ya, shigo cikin gida bayan tsohuwan nan.”

Da bayin nan suka ji haka sai suka dauka. “Wallahi, karya ya ke yi. Allah ya ba ka nasara, mun rantse har da rawaninka ba mu taba shigowa na ba.”

Sarki ya dubi dogarawa, ya ce, ‘Ku tambaye su.”

Dogarawa suka same su da duka, suna ihu. Sai Barakai ya ce, “Ni zan fadi gaskiya, na sai da raina don ubangijina ya yaba, ban sami kome ba sai duka, nan kuma in zo haka?” Sai ya kwashe duk a;’amarin ya gaya wa Sarki. Sauran da suka ga ba dama, su ma suka fadi gaskiya. Sarkiu ya sa aka daure su cikin gidansa.

Aka kwana biyu, rana ta uku da azahar sai ga “Yan Doka sun zo da Waziri, sun kamo shi can kan iyaka, ya kusa ketare kasa, ya nufi sinari. Da aka zaunad da shi gaban Sarki, sai ya bata fuska, ya tashi da fada ya dubi Sarki yanan cewa, “Na mene ne za a aika ‘Yan Doka su kama ni, ban ci kayan kowa ba?”

Sarki ya tashi da mamaki, yana tafa hannu yana cewa, “A’a! Ashe kamo ka suka yi?”

Waziri ya harari ‘Yan Doka, ya ce, “Kamo ni suka yi mana.’

Sarki ya ce, “Ni ban ce su kamo ka ba, cewa na yi su kira ka, in ji ko lafiya, don tun shekaranjiya waccan rabona da ganinka.”

Da Waziri ya ji maganar lumana sai ya ce a ransa, “A’a! Ashe da ma asirina bai tonu ba na ke son tona kaina a wofi. Da ma na da ma san Sarkin nan gabo ne, ba ya gane kome. Kuma ko ma ba wawa ba ne, irin makircina ai ba mutum duka zai gane shi ba.” Sai ya ce, “Af, ashe Shamakina bai gaya maka ba?” Ai na tafi ganin wata goggona ce da aka aiko mini ba ta lafiya. Amma dai, Allah ya ba ka nasara. ‘Yan Dokan nan sun karya mini irli.”

Sarki ya ce, “Sai ka yi hakuri da su. Da ma ina gaya maka sakarkaru ne, kai ke cewa suna da kirki.”

Waziri ya harari ‘Yan Doka, ya ce, “na rantse har da girmanka, ba na iya yafe musu, tun da suka ci zarafina haka. Su duk sai daure su yanzu. Ko mahaukaci ai ya san abin da ya kamata.

Sarka ya ce, “Ai kai ne da mulki, sai ka yi abin da ka ga dama da su. Amma bari in tambaye ka abin da ya sa na kira ka tukun. Tun da na dawo ban sami damar tambayarka wani abu ba game da gidana da na bar maka amana.”

Waziri ya ce, a ransa, “A’a! Ka ji tsohon banza da wata irin tambaya.” Sai ya dube shi, ya ce, “Ka tarad da wani abin tashin hankali ne? Ai ni ban yi wasa da gidan nan ba, da kaina na ke fitowa da tsakad dare in kewaya.”

Sarki ya c,e ‘Na san haka. Amma wadansu takardu ne aku ya nuna mini wadanda ban gane kansu ba.” Ya dubi aku, ya ce, ‘Je ka, kawo su.”

Aku ya tashi ya kawo su, ya zube gagban Sarki.

Da Waziri ya ga takardun nan, sai cikinsa ya ba da kulululu. Ya kwaikwayon hannuna. In ka bibiya ma shegen akun nan ne. Amma, Allah ya ba ka nasara, ya kamata a tsawata masa, in zai yi wasa, ya rika yi da tsarar-rakinsa su ungulu da jemage!” Ya fashe da dariya, wai shi gwanin ba’a. Ya daga kai ya dubi Sarki, ya ga shi bai yi dariya ba. Ya dubi Musa, ya ga shi ma hakanan. Ya juya ga Mahmudu, ya ga kowa kinne. Aku ko ma, sai wasansa ya ke yi da kwayar gyada, kamar bai ko ji abin da a ke fadi ba. Sai idonsa ya raina fata.

Sarki ya dubi Sarkin Dogarai, ya ce, “A zo da mutanen nan.”

Dogarawa suka duru da gudu cikin gidan Sarki, suka fito da bayin nan na Waziri, kowanensu an bankare shi.

Da Waziri ya gan su sai gabansa ya fadi. Ya gyara zama, ya duba gabas ya duba yamma, ya ga kowa ya kura masa ido.

Sarki ya dube shi, ya ce, ‘Ka san wadannan?”

Waziri ya ce, “Ka ji kaina, ka yafe ni, ba don halina ba!”

Mutanen gari da aka tara suka yi ta duban Waziri, ba su san abin da ke ciki ba.

Mahmudu ya tashi, ya kashe Waziri da mari ya ce, “Sarki ke tambayarka, ka san su, ka dame shi da magiyar banza!”

Waziri ya dubi Barakai, ya ce, “Kai ne amintaccen bawana, don Allah bayyana musu sosai, su san ba ni da laifi cikin wannan al’amarin.”

Barakai ya ce, “A’a! Ba ka da laifi? To, wa ke da shi?” Makirin banza!” Ya gusa gaba, ya daga murya ya fadi duk makirce-makircen da Waziri ya kulla game da Sarkin Sinari, da game da Musa, bai rage kome ba.

Da mtane suka ji haka sai suka yi salati, suka taso wa Waziri gaba daya kamar za su cinye shi danye, sai da dogarawa suka shiga tsakani.

Sarki ya ce musu, “Ku dakata tukuna, ai ba a kare ba.” Shi kuma ya kwashe labarin yadda aku ne ya yi ta kokari ya kubutad da su daga zama bayin Sarkin Sainari. Ya kuma gaya musu yadda ya hana Musa ya fita waje, don a gane abin da Waziri ke hannu, suka dubi aku, suka dubi Waziri. Sai suka fara dibar kura za su yi masa ature, sai da Sarki ya tsawata.

Da suka dakata ya sake dubansu, ya ce, “To, jama’a, ku dubi laifin nan na Waziri. Wanda ya aikata haka me ya kamata a yi masa?”

Jama’a suka dauka gaba daya, “Sai a tsire shi! Da shi ai halaka mu ya tashi yi, don Allah ya ki nufinsa. Da ma ba mai kaunarsa garin, don mugun halinsa.”

Sarki ya ce, “Na ji tasa. To, wadannan mutanen ko fa?” Jama’a suka ce, “Su ma sai a tsire su, abin da ya ci Doma ai ba ya barin Awai.”

Musa ya ce, “A’a, tun da dai Allah ya ki aniyarsu, ya gama fuskokimmu a Mahmudu lafiya, ga shi kuma Sarki ya ciwo nasara, sai a yafe su.”

Sarki ya ce, “Gaskiya ne, Musa. A kwance su.” Aka sake su, suka zo suka fadi gaban Sarki suka yi godiya, don da sun tabbata za a kashe su. Mutane suka yi mamakin Sarki a kan wannan nasiha.

Sa’an nan Sarki ya tashi tsaye, ya ce wa jama’a, “To, mun ga inda wadannan tasu ta kwashe. Amma ina tambaya, shin don me a ke yin Waziri?”

Jama’a a suka ce, “Don, ya rika taimakon Sarkin gari shawara, yana kwabe abin da zai cuci jama’a, ba kamar wannan ja’iri ba. Allah ya kiyashe mu da halinka!”

Sarki ya ce, “In don haka ne, na nada wannan aku Wazarina. Da shi zan rika shawara.” Ya dubi mutane, ya ce, “Ko kuwa kun ga bai isa a yi shawara da shi ba, don yana tsuntsu?”

Jama’a suka ce, “Wane irin isa? Wanda ya yi wadannan abubuwa a ce bai isa ba? Wanan tsuntsu ai baiwa ce Ubangiji ya nufe mu da ita, wa ke da ikon jayayya da nufin Allah? Mu dai wallahi mun so, mun so.”

Sarki ya dubi dogarai ya ce, “A kama Waziri, a daure shi cikin jaka da ya bayar a sa Musa, a tafi da shi a jefa cikin kogi, yadda ya yi niyyar yi wa Musa. Ku kuwa Sarakunana da makada, a tafi a kai Waziri Aku gidan Waziri, a fid da matansa na aure, sauran ko duk abin da ke gidan an ba shi.” Sarki ya tashi ya shiga gida. Duk fada ta yamutse, wadansu suka nufi wajen da za a kashe Waziri, wadansu suka bi sabon Waziri, ana ta goce ganguna da kakaki. Aku kuwa yana bisa wata karanga ta zinariya, an sa laima, katta na dauke da shi. Sai makada ke ta binsa suna waka:

Haba jama’amu, ku zo mu yi caffa,

Gunsa Waziri, mazajen aiki.

Masu rabo da yawa mai ba mu!

Sannu da sirdi, tsuntsun kirki!

Da ba don shi ba, masu fasaha,

Da yanzu da muna Sinari.

Ga wani sauna, don sakarci,

Ya yi butulci, ya bashe shi.

Ikon Allah wa zai ki shi?

Kowas saba yai jahilci.

Ka sai mana doki, baba Waziri,

Muje mu gwada wa mutan Sinari.

In ba donka ba, mai cika aiki,

Da wani mun ga irin bautanshi.

Masu fasaha, masu basira,

Mai tauhidi, Sarkin ilmi!

Ga ni a durkushe, na roke ka,

Ya Allahu ka gafarce ni.

Aka kai aku gidan Waziri, ya debi dawaki uku daga cikin wadanda ya samu gidan Waziri, ya ba makada da suka rako shi. Ya sa bayi su yi ta gadinsa. Aka yi ta shagalin saraunta har kwana bakwai. Da aka natsa, Sarki ya sami matan aku guda hudu ya sai wa sabon Waziri. Duk inda Sarki ya ji wani na da aku, in mace ce, sai ya sayo ya kawo wa Wazirinsa, watau kwarakwarai.

Ana nan, bayan ‘yan kwanaki daya daga cikin matan nan na Waziri Aku ta yi kwai. Bayan kamar kwana ashirin ta kyankyashe wani dan aku namiji. Ya sa masa suna Fasih, ya sa wani bawa ya yi ta kiwonsa.

Waziri Aku ya yi zamansa, yana ta muskakar sarauta. Ba ya shan ruwa sai da sukar, shinkafa ko ba ya cinta sai an dafa an sa gishiri da mai.

 

 

 


Koma Baya

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.