Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo  


 

  Kafin in zo wajen Balaraben nan da Sarki Abdurrrahmani ya sayo ni a gunsa, da wajen wani Bayarbe na ke wai shi Ojo. A cikin garin nan da ya ke duk ba wanda ya kama ko kafarsa wajen arziki. Amma duk da haka abin ya ba ka mamaki in ka ji na ce matarsa daya ce tal. Da yana da uku, sai ya auro wata hatsabibiyar karuwa, suka yi su hudu. Ko da karuwan nan ta shiga gidansa, sai ta tasam ma shiga bokaye da ‘yam bori, don ta sami maganin da za ta kori sauran matan. Kwanci tashi, ta ko samu. Ojo kuwa da ma ba ya ganin kowa da gashi, ba da karuwan nan. Don tsananin son da ya ke mata shi ya sa ya aure ta.

Da ta sami maganin da za ta yi ta raba Ojo da sauran matansa, sai ta ce, “Kome ya yi kyau. Amma ai fa an ce kau da bara ba ta ci sai an gama da gociya.” Saboda haka fa ta soma kulla makirci, tana gama Ojo da mantsa dai dai. Yau ta sa ya kori wannan, gobe ya kori waccan har ya zama gidan ba wata sai ita. Ga mijin kuma Allah ya ba ta a hannu. In kara ta gifta masa ba shi da ikon ketarewa, sai ka ce ba mai arziki ba. Mulkin nata ya wuce bisa kan mijin, har yaran gida ba mai ikon tari in tana nan. Da wani, ya yi mata dan tashin kai, sai ta sa a kore shi. Kai, bari ta su mutane, har ni ma da na ke dan tsuntsu shakkarta na ke yi. Ga mijin mutumin kirki, yana son yin wani abu, amma yana shakkar kada ta yi hushi ta ce za ta fita ta bar shi.

Da na ga dai abin nan ya rude haka, sai na ce, “Abin nan ya kamata mu sa hannu.” Na yi kwana uku ina shawarar hanyar da zan bullo wa wannan al’amari, yadda karuwan nan ba za ta ji ba, balle ta halaka ni, yadda kuma Ojo ba zai gane nufina sosai ba balle shi kuma ya tsane ni. Don ka san an ce, “So, hana ganin laifi.” Da na sami wata dabara, sai na kyale. Ran nan muna tare da Ojo, sai na ga yana sauraron wata ‘yar tsuntsuwa da ke kuka nan bisa taga. Na dube shi na ce, “Da kana jin abin da ‘yar tsuntsuwar nan, ke cewa, ashe da ban san abin da za ka yi ba don murna.”

Ojo ya ce, “Haba, yadda na ke da arziki haka, ya zama kuma ina jin abin da dabbobi da tsauntsaye ke fadi, ai da ba haka ba.” A raina sai na ce, “Wannan ya samu.” Na dube shi, na ce, “Akwai maganin da a ke yi a ji, amma da sharadi guda mai wuya, shi ya sa ba shi da amfani sosai, ba don haka ba, ko ni ma da sai in ba ka. Ba wanda ya san wannan asiri ko cikin tsuntsaye, sai zuriyar gidammu kadai.”

Ojo ya ce, “Don Allah ka ba ni. Gaya mini sharadin kome wuyarsa na iya.” Na yi dan musun karya, ya matsa ni. Sai na tafi, na samo maganin na ba shi, na ce ya sa a dandaka, a rika zuba masa ruwa cikin kunne kullum, da dare.

Ya tambaye ni bayan kwana nawa za a bari. Na ce masa in lokacin bari ya yi, ba sai an gaya masa ba, zai ji abin da ya ke so ya samu. Yana doki zai shiga gida ya bayar a dandaka, sai na ce masa, “Ai ba ka ji sharadin ba.” Ya dakata. Na ce, “Sharadinsa shi ne duk wanda Allah ya yi wa wannan baiwa kada ya bi shawarar mata, kome mace ta gaya masa, ko ‘yar wane ne, ko da shawarar mata ko sau daya, ran nan fa shi kuma sai labari. Wannan, ma in an fadi ba a kwana, ni na kara shi.”

Da ya ji haka sai ya harare ni, ya ce, “Da ma don dan wannan sharadi ne ka ke cewa ba na iyawa” Me ka mai da ni ne.”

Na ce, “Iyakarsa ke nan. Da ma batun mutuwan nan kadai na ke tsoro gare ka.”

Sai ya yi tsaki ya shiga gida ya dandaka maganin da hannunsa, ya kwaba, ya zuba ruwa cikin wata ‘yar kwalaba. Kullum da dare sai karuwan nan ta zuba masa cikin kunne sa’ad da zai kwanta barci. In ta tambaye shi dalilin da ya sa ana yi masa haka, sai ya ce mata kunnensa ke ciwo, aka ba shi magani.

A kwana a tashi, ran nan da ya farka barci, sai ya ji wani dan bera ya ce wa gudan, “Shin Damburuntu, me ya sa kyuanwoyi ke cimmu ne? Su ba su da wani abinci sai mu? Da haka a ke zaman duniya, wanda ya fi wani karfi ya cinye shi, ai da yanzu ba kowa!”

Damburuntu ya ce, “Haba raina mu dai suka yi. Babban munafikin kuwa mai gidan nan. Shi ba Sarki ba, ba Waziri ba, har da ajiye kyanwoyi uku! Don Allah dubi yadda ya kwanta ya bude ciki, sai ka ce taiki!”

Ojo murna ta cika shi, ya yi kamar zai yi dariya, sai ya kanne, don kada ya yi su gudu. Yana nan shiru, sai ya ji wancan na fari ya ce, “Damburuntu, kewaya can, ni in kewaya nan, mu ciji kunnuwansa, ko nan ma mu more.”

Da jin haka sai Ojo ya yi wuf ya tashi. Beraye suka watse. Ya bushe da dariya, yana godiya ga samun wannan babbar baiwa.

Yana nan kwance, ya kasa barci don murna, har aka yi kiran asalatu. Ya tashi matarsa ta kawo masa ruwan alwalla, ta ajiye ta tafi. Ya fito ya fara alwalla. Ya kusa gamawa, sai ga wani burtu nasa da ya ke kiwo ya nufi wajen wata kaza, ya ce “Ni dai, kaji, kuna ba ni mamaki wajen butulcin nan naku da cin amana.”

Kaza ta ce, “Me ka gani ne, ka ke tsinammu haka.”

Burtu ya ce, “Dubi alherin da mutane ke yi muku. Da rana su ba ku hatsi da ruwa, ku sha a huce. Da dare su sa ku cikin daki su rufe, su yi ta saurare don kada muzuru ko maciji ko wani naman jeji ya je ya cuce ku. In kun haihu; su sa ;ya;yanku daki, su yi ta ba su abinci har su yi girma, don kada su fito tun suna kanana, shirwa ko shaho su raba ku da su. Hasali ma dai, zaune ku ke kawai, ba abin da kuka rasa. Amma kuwa ran da suka ce za su kama daya daga cikinku, duk ku gama gari da kuka, ku tashi ku fada bisa wannan shigifa, ku yi tsalle bisa wannan zaure. To, wannan ba butulci ba ne, mene ne? Hala irin godiyarku ke nan?”

Kaza ta yi misa wata irin duba haka yakine, ta ce, “To, kai da ya ke ba butulu ba ne, gaya mini ta inda ka fi mu godiya ga mutane.”

Burtu ya ce, “Ni a dawa Allah ya halicce ni, ba kamarki ba, amma duk da haka in mutane suka kama ni suka kawo gida, sai in dangana, ko da ya ke ban saba ba, in yi ta yi musu duk abubuwan da su ke so suna dariya. In sun kira ni, sai in taho. In na ga ubangidana sai in bi shi, in rika hawan buzunsa ina wasa. In ya jefa wani abu in bi in rida, don ya yi dariya. To, wannan ba rashin butulci ba ne, mene ne?”

Kaza ta ce, “I, gaskiya ne, ya kamata kuwa ka yi alfahari bisa ga godiyan nan taka. Amma da ka taba ganin mutane sun kama ‘yan’uwanka sun yanka, sun fige suna soyawa,yadda na ke ganin kullum suna yi wa dangina, da ran da suka tashi kama ka, bari ta gudu kana fadawa shigifu, in ka balle daga nan ka shiga daji, ko labarin inda ka ke ba a sake ji.”

Burtu ya yi shiru, ya rasa abin da zai ce wa kaza bisa wannan magana tata. Kaza ta harare shi, ta juya, ta ce, “In za ku yi magana, ku rika tsayawa tukun kuna lura, kuna auna ta tukun kafin ta fito bakinku har wadansu su ji. Ga irin abin da a ke gudu ke nan, mutum ya fadi maganar da bai san kanta ba, bai san gindinta ba, ta zo ta dame shi daga baya. Kai, Allah wadan zaman daji!”

Da Ojo ya ji haka ya bushe da dariya, har ya haure ruwan alwallarsa bai sani ba. Da ya gama dariya, ya kare alwalla, ya shiga daki ya yi salla. Da ya gama, sai karuwan nan ta zo ta ce masa, “Maigida, yau ni marmarin shinkafa na ke ji, ita zan dafa sai a sayo tozo.”

Zai ce to, sai ya tuna da maganar aku, yana tsammani da ya yarda zai mutu, ga shi kuma ba ya son bata wa matar zuciya, sai ya tuna ba abin da ya fi ransa dadi. Ya san yanzu da ya mutu sai ta fita ta auri wani, shi ta manta da shi. Sai ya ce mata, “An ki, ni yau tuwon dawa za a yi mini, miyar shuwaka.”

Ta dube shi haka yatsine, ta watsar, ta yi tsaki, ta ce, “In wani ke min da hannun, ba sai ya sa in yi na dawa ba? Ni na shinkafa zan yi, in kama kazarka a yanka in ka ki sawo mini tozo. In ya so, in na yi, ko ka ci, ko kada ka ci, ni ba abin da ya dada ni da kasa.” Sai ta tashi ta nufi wajen buhun shinkafa, za ta diba. Ojo ya ga in ya bar ta ta yi abin da ta ke so, watau shi zai mutu ke nan. Sai ya tafi ya kama ta. Sai kokawa ta kaure kiki kiki. Ojo ya tuna shi namiji ne, ya dauke ta ya kantara da kasa, ya yi ta bugu.

Da mutane suka ji kuwwarta tana cewa, “Wayyo Allah, na tuba! Ba na kara yi maka musu, ka ji kaina!” Sai suka rugo, aka zo, aka kwace ta da kyar. Ta yi yaji.

Bayan kwana uku Ojo ya bi ta, aka yi rarrashin duniyan nan ta dawo, ta ce in ta koma gidan nan ya zama kabarinta. Ta tashi za ta yi masa halinsu na karuwai, ta tona masa asiri cikin jama’a ya ce ya sake ta.

Abinka da mai sule, kafin kwana bakwai ya nemi ‘yam mata uku ‘yan gaske, aka ba shi. Da ya mila, sai ya ce a sa su lalle gaba daya. Aka sa su, aka yi biki, aka gama. Muka yi zamammu lafiya lau da matan nan nasa, ba sauran mai kuka da wani.

Da aku ya kawo nan, ya ga gari bai waye ba, sai ya dubi Musa, ya ce, “Don Allah ka yi kokari ka yiwo abin da kowa zai yaba. Ka tabbata wata dabara taka, da wani tsoro, duk ba su hana maka mutuwa, domin duk ran da ajali ya yi kira, ko babu ciwo a je. Gama Sarkin Yaki yana zaune lafiyarsa lau, amma ran da ajalinsa ya sauka, sai da ya sayo wa kansa halaka.”

Musa ye ce, “Ai Sarkin Yaki ya sami lafiya har ya tafi tare da Sarki.”

Aku ya ce, “Ba Sarkin Yakinku na nan gari na ke magana ba, ina zancen Sarkin Yakin Niraini ne.”

Musa ya ce, “Ina ne Niraini? Ban taba jin sunan wannan gari ba, balle Sarkin Yakinsu. Me ya sa saya wa kansa halaka?”

Aku ya ce, ‘Yanzu kuwa ka ji.”

 

 

Koma Baya




{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.