Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi 



  Da aka yi wani Sarki mai son nishadi. Ana nan wata rana zuciyarsa ta yi baki kirin, har ya kasa barci. Ya kira yaronsa ya ce masa, “Maza ka tafi wurin Waziri, ka ce ina kiransa.” Yaro ya tafi ya gaya wa Waziri, suka zo tare, suka shiga wurin Sarki.

Da suka shiga Sarki ya ce wa Waziri, “Yau zuciyata ta baci, har barci ya gagare ni. Ina so mu tafi mu zaga rafi, ko zuciyata ta yi sanyi.”

Waziri ya ce, “To, shi ya fi, ranka ya dada.” Da fadin haka sai yaron ya yi dariya.

Sarki ya ce, “A’a! Mene ne? Ni ka ke wa dariya ko Waziri?”

Ya ce, “ Ranka ya dade, wane ni in yi maka dariya? Wani abu ne ya fado mini a rai wanda na gani jiya, shi na ke dariya.”

Sarki ya ce, “Wane irin abu ne?”

Yaro ya ce, “Ranka ya dade, jiya ina yawo a bakin kogi sai na iske wani mutum, mutane sun kewaye shi, yana ta ba su dariya.”

Sarki ya ce, “Maza ka tafi ka kirawo shi, ya zo ya mini abin da zai ba ni dariya, ko na samu zuciyata ta huce.” Yaro ya tafi wurin mutumin, ya ce, “Sarki yana nemanka.”

Sai mutumin ya ce, “To, da kyau. Me ya Sarki ya ke kirana?”

Yaron ya ce, “Yau Sarki yana bakin ciki, yana so ka zo ka ba shi dariya, don zuciyarsa ta yi fari.”

Sai mutumin ya ce, “Mu je.”

Yaro ya ce, “To, sai mu yi sharadi, abin da Sarki ya ba ka duka a kasa shi uku, kau ka kwashi kashi daya, ni in kwashi kashi biyu. In ka yarda da haka zan kai ka, in ba ka yarda ba, yi zamanka, ni kuwa in koma in ce ban gan ka ba.”

Sai ye ce, “To, shi ke nan, na yarda. Mu tafi.” Yaro ya kai shi wurin Sarki, ya fita.

Sarki ya ce wa mutumin, “Ina so ka yi mini abin da zai sa in yi dariya. In na yi in yi maka kyauta, in ban yi ba in yi maka bulala.”

Mutumin ya yi ta yin abubuwa masu ban dariya, da labaru iri iri, har ya gaji. Sarki bai yi dariya ba.

Sarki ya ce, “Shi ke nan, ko akwai saura?”

Mutumin ya ce, “Shi ke nan.”

Sarki ya ce, “Ga shi ban yi dariya ba. Kwanta in yi maka bulala.”

Mutumin ya matso, ya kwants. Sarki ya tsala masa bulala da karfi. Sai ya yi ta kururuwa, ya ce, “Tsaya, rank ya dade! Na karbi rabona, saura na yaronka. Domin mun sharada kome na samu in dauki kashi daya, shi kuwa biyu.”

Sarki ya kira yaronsa, ya ce, “Na ba wannan mutum rabonsa, sauran naka, matso kusa ka karba.”

Yaro ya matso kusa, yana tsammani zai sami kudi. Sarki ya tsala masa bulala da iyakacin karifinsa. Yaro ya kwala ihu. Sarki ya ce, “Tunkuna, ai kashi daya kadai ka sam, saure daya.”

Yaro ya ce, “Ranka ya dade, kashi dayan nan ma ya ishe ni, na bar maka dayan.”

[insert picture here—middle right page 97]

Da Sarki ya ji haka sai ya fashe da dariya, bakin cikinsa ya yaye. Ya kawo kyauta ya ba su, ya sallame su.

Kafin aku ya kare wannan labari gari ya waye Barakai ya koma yana cizon hannu, yana neman hujjar da zai fada wa ubangidansa.

Da zuwansa Waziri ya Harare shi, ya ce, “Ban ji an gama aikin ba. Ina dalili?”

Barakai ya ce, “Ruwa!”

Waziri ya ce, “Ruwa? Wane iri? Ruwa da aka yi aka dauke tun kafin a yi kiran sallar fari?”

Barakai ya ce, “Watakila nan wajen gidanka aka dauke da wuri, wajen fada har rana ta fito ana ruwa.”

Waziri ya cika, ya kawo iya wuya, ya zabura ya danne shi ya shake, ya ce, “Fada mini gaskiya, in ba haka ba ko yanzu in kasha ka, mutumin banza, munafuki! Lalle kai ne ka tona asirin da muka kulla da Sarkin Sinari. Da ma ina shakkar haka.”

Da Barakai ya ji haka sai jikinsa ya dauki rawa, ya ce, “Na tuba Allah ya ba ka nasara, gaskiyaa zan gaya maka yanzu. Akun nan sihiri gare shi, in y fara ba da labari, sai duk hankalin mutum ya rude, ya rasa abin da ya je yi. Muddin akun nan na numashi ba yadda za a yi a fid da Musa daga gidan nan, ko kai ka je da kanka.”

Waziri ya ce, “Rufa mana baki nan da karyar banza!” Ya dauki bulala ya tsala masa har ya gudu.

Waziri ya koma ya zauna, yana ciccika shi kadai, yana cewa, “Ina Wzairi kasan nan duk tsawonta da fadinta, ga shi dan abu kadan ya rage da zan yi in zama Sarki, dan tsuntsu ya ce zai hana! To, bar ni da shi.”

Sai ya aika wajen Musa ya ce yana son aku ya zo yau ya debe masa kewa da labaru. Ya ba da igiya, ya ce in Musa ya yarda a daura shi a zo da shi. Da aka gaya wa Musa, bai san abin da a ke nufi ba ya ce shi ya yarda, zai tambayi akun kuma ya ji in ya yarda. Ya tafi ya tambayi aku, aku ya ce, “yallabai, tun da ka ce in tafi, ai sai in tafi.” Yaron da aka aiko ya jawo igiya zai daure aku ya kai shi. Aku ya ce, “Mene ne na dauri? Ban saci kayan kowa ba. Ba cewa aka yi ana sona don nishadi ba? Wuce, in hau bias kanka mu tafi.” Suka tafi har gidan Waziri, suka tarad da shi a kofar gida. Aku ya sauka, ya tsaya nesa kadan. Waziri ya salami mutane. Da shi niyyarsa, yana da wata katuwar sanda a boye ya kasha aku, kowa ya huta. Da aku ya lura da sandan sunne cikin rigar Waziri, sai ya kara ja da baya.

Waziri ya ce, “Matso mana.”

Aku ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ina ni ina zuwa kusa da kai?”

Waziri ya ce, “Ina so ka ba ni labari, kowane iri ka ke iyawa, in na ji da dadi in yi maka kyauta.”

Abu ya ce, “To, sai ka zauna in fara.” Waziri ya zauna, aku ya fara.


 

 

 

Koma Baya

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.