Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara 


  Akwai wani Sarki a Zairana wanda Allah ya nufa da kiba, abin har ba iyaka. Idan ka gan shi sai ka ce giwa, in ya zauna ba yadda zai yi ya ga cibiyarsa, dokin duniyan nan duk ba mai iya daukarsa. In ya tashi daga zauren gidansa zai shiga, mutum ya yi tafiyar loko biyu Sarkin nan bai isa ba.

Sarki fa duk abin duniya ya dame shi bisa ga wannan kiba, shi kuwa ba abin ya ki cin abinci ba ya mutu. Saboda haka ya tara bokayen kasarsa, ya ce su yi kokari su samam masa maganin da zai sha ya rage kiba. Bokayen suka shiga aikinsu. Kowa sai ya sassako wannan itace, ya gino wannan sauya, ya kai wa Sarki. Ya yi ta sha, amma a banza. Maimakon ya ragu sai karuwa ya ke kullum safe, sai ka ce ma maganin ya kara kiba su ke ba shi. Da Sarki ya ga haka sai ransa ya kara baci, ya yi kamar ya kashe kansa don haushi. Ga duniya Allah ya ba shi, kiba ta hana shi jin dadin cinta.

Yana nan haka sai ya ji labarin wani boka wanda a ke kira Gara Mai Aburkuma. Sarki ya aika aka kira shi, ya bayyana masa bakin cinkinsa. Ya ce in warkad da shi kuwa zai yi masa kyauta har ya kasa godiya.

Gara ya ce, “To, Allah ya taimake mu. Amma in ka yarda, ranka ya dade, ina so a ba ni kwana uku in je in shawarci Aburkuma, Inna uwa ma ba da mama, abina da muka yi da ita duka zan zo in gaya maka.”

Sarki ya ce, “To, je ka, na ba ka iznin kwana uku, amma kada ka wuce haka.”

Gara ya yi ban kwana, ya tafi. Ya yi ta tunanin inda zai fito wa Sarki ya yaudare shi. Ya san dai, in ba wautar Sarki ba, wane boka ne zai iya ta da hukuncin Allah?

Bayan kwana uku sai Gara ya komo wajen Sarki, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, na dawo.”

Sarki ya ce, “To, ina labari?”

Gare ya ce, “Allah ya daukake ka, ai sai a bar kaza cikin gashinta, al’amarin ya tayar mini da hankali.”

Sarki ya ce, “Me ka gani, na ce. Fada mini mana in ji.”

Gara ya ce, “Allah ya ja zamaninka, ai ba na iya fadin abin da Inna ta gaya mini. Saboda bakin cikin al’amarin, jiya, na rantse har da rawaninka,ban yi barci ba. Abin da na gani ya fi sai a bar wata wahalar neman magani, a tasam ma istingifari.”

Sarki ya fusata, ya ce, “Yau ga zancen banza. Na ce ka gaya mini abin da ka gani, ka tsaya kana kewaye-kewaye.”

Gari ya ce, “Allah ya yi wa Sarki rahama, Inna ta ce saura kwana arba’in ka riga mu gidan gaskiya.”

Sarki ya fusata, ya ce a kama shi a daure. Dogarawa suka café shi. Gara ya ce, “Da ma abin da na ke gudu ke nan da gaya maka gaskiya.” Aka dai iza keyarsa zuwa gidan kurkuku.

Sarki ya shiga zulumin abin nan da Gara ya fadi, ya ce, “Na san Gara fa shahararre ne bisa ga al’amari da aljannu. Ba abin da ya fi dai sai a rika kidaya kwanakina da ya fai. In sun cika arba’in na ga ban mutu ba, na san Gara karya ya ke yi. In kuwa na ga bayan kwana talatin da takwas, ko talatin da tara, na fara ‘yar mashasshara na san ni tawa ta kare.”

Wannan zulumin da ke ran Sarki fa ya sa ya tsunke. Ko abinci ba ya iya cin abin kirki, balle ma ya faranta ransa da wadansu kawace-kawacen duniya. Saboda haka kullum sai ramewa ya ke don zulumi Duk mutane suka rasa kansa suka rasa gindinsa.

Bayan kwana talatin da wannan magana sai tashin hankalin da tara da ya ji ciwon kan na karuwa, sai ya kira dansa ya danka masa mabundin taskoki, ya yi ta yi masa wasiya, yana gargadinsa yana cewa su tasu ta kare. Yaro bai san abin da ya ke nufi ba, tsammani ya ke don ya fara tsufa ne ya ke so ya nuna masa al’amuran mulki.

Ana nan dai kwana arba’in suka cika, Sarki na jiran mutuwa, bai ga ya mutu ba. Kwanaki dai suka kai kwana arba’in da biyar, Sarki bai ga ya mutu ba. Sai ya aika aka zo da Gara daga gidan sarka, ya ce, “Ka ce bayan kwana arba’in zan mutu, ga shi yau kwana arba’in da biyar da maganar, ban mutu ba.”

Gara ya ce, ‘Da ma maganin ka rage kiba ka tambaye ni, to, karyan nan da na yi na ce saura kwana arba’in ka mutu ita ce maganin. Ka tambayi kowa nan garin ka ji in ba ka rage kiba ba.”

Da Sarki y ji haka, sai hankalinsa ya kwanta, ya bushe da dariya, mutane suka yi kyakkewa baki daya, suka ce, “Lalle Gara ya isa dan duniya.”

Gara ya ce wa Sarki, “Ba abin dariya ba ne, sai ka ba ni abin da ka alkawarta.”

Sarki ya sa aka yi ta kawo masa riguna da zannuwa da wanduna, ya kuma ce duk mai kaunarsa ya yi wa Gara kyauta. Mutane suka yi ta zuba masa kudi, tun yana godiya har ya fashe da kuka don murna. Sarki ya sallame shi, ya kwashe kayan da aka ba shi duk, ya tafi.

Kullum in an ta da labari, sai Sarki ya yi ta yi wa kansa dariya in ya tuna abin da ya yi daren da kwanan nan arba’in za su cika, da ya yi ta yawo tsakar gida shi kadai, ya kai gwauro ya kai mari, yana ta salati ga Fiyayyen talikai.

Aku na kare wannan labari, sai Musa ya ji zakara na ta cara, gari ya waye. Ya rasha abin da zai ce wa aku ya huce, sai ya shiga gida, ya yini ran nan bai ce wa koma kome ba.

Magariba na yi, sai ga ‘yar tsohuwan nan ta dawo, Waziri ya aiko ta da takarda wai daga Mahmudu, ta kawo wa Musa. Musa ya karba ya karanta, ya ce, “Allah wadan dan abin nan da ke hana ni fita.”

Tsohuwa ta ce, “Yanzu haka, yallabai, duk karkaran nan da mace da namiji ba ka jin wani abu sai Mahmudu. ‘Yam mata ma yanzu ba su da wata waka sai ta Mahmudu.”

Musa ya ce, “Har waka ‘yam mata suka yi masa? Don Allah, in kin iya, rera mu ji.”

‘Yar tsohuwa ta karkace kai, don iya kissa ta fara wakan nan, ba da ko ta taba jinta ba:

Jama’a ku zo ga kallon Mahmudu,

Wanda ya wuce wargi.

Ya fi karfin sai gobe,

Ya wuce mai wargi.

Shi ne ka kori Sinarawa,

Har ya kashe musu Sarki.

Ya fi karfin sai gove,

Ya wuce mai wargi.

Mahmudu wa ga Musa, mazaje,

Da sunka kawo karfi.

Ya ki wargi dattijo,

Ba ya son mai wargi.

Zaman gida na raggo,

Sai dan da ke gudun mai karfi.

Dan Sarkin da ke cikin mata,

Shi da su ana nan daidai.

Ya fi wargi, Mahmudu,

Ba ya son mai wargi.

Da Musa ya ji wannan waka wai idandunansa suka jujjuye. Tsohuwa ta tashi, ta tafi wurin Waziri ta gaya masa. Waziri ya yi mata kyauta.

Da asubahin farko, Musa ya yi damara, ya dauki wata babarbara, ya tafi wajen aku, ya ce, “Zan tafi, ko ka yarda, ko ba ka yarda ba.”

Aku ya duka, ya ce, “Yallabai, ina da ikon hana ka? In dai ka fita, ka sami dan kwabo ka yi sadaka. Allah ya ba da sa’a!”

Musa ya ce, “Gaskiyarka. Yi maza ka debo, amma kada ka tsaya.” Aku ya fia ta taga, ya sami wata itaciya ya haye, ya yi zamansa.

Can da ya ga asalatu ta kusa, ya debo ganyen itaciyar, bai san ma ko wace irin itaciya ba ce. Ya taso fir ya kawo wa Musa. Musa ya karba, ya ce, “Amma kuwa ka tsai da ni.”

Aku ya ce, “Ba ka san iyakar inda na tafi ba ne, da ba ka zarge ni kan dadewa ba. Ka sa a dafa maka, ka yi wanka da shi, ba dai karfe ba, sai wani abu.”

Musa ya ce, “Ka ji asalatu ta yi.”

Aku ya ce, “Ba kome ka tafi gobe, zuwa da wuri ai ya fi zuwa da wuri wuri. Kafin a kare kiran salla bari in gaya maka wani dan labari guntu.”

 

 


Koma Baya

{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.