|
Alhaji
Dr. Mamman shata Katsina a halin da ake ciki yanzu ya zamewa
makada da mawakan Hausa Dutse baka daukuwa saida gammo, mutsu-mutsu
gobe jar kasa, ruwan dare mai gama duniya, ya buga da mazajen
farko gashi yana bugawa da mazajen yanzu. Abinda marokinsa ke
fada ke nan kafin ya fara wakarsa ta Bakandamiya. Babu wata
kasa a duniya da zata bugi kirji ita kadai tace ta sami ci gaba
a rana guda. Su kansu kasashen da suka ci gaba irin su Amirka,
Tarayyar Soviet, China, Birtaniya da Japan da Jamus sun yi amfani
ne da kyawawan al'adunsu wajen gina tushen ci gaban da suka
samu. Mawaka da makadan wadannan kasashe da suka ci gaba sun
bada gudummawa mai yawan gaske ta fuskar irin tasu fasahar wajen
ciyar da kasashen nasu gaba.
Farfesa Dandatti Abdulkadir, kafin ya zama shugabanjami'ar Bayero
dake Kano a Nijeriya, ya rubuta makalarsa ne kan rayuwa da wakokin
Alhaji Mamman shata sannan ya gabatar wa shaihunan Malaman Amirka
don su tabbatar masa da samun digirinsa na uku (Ph. D). Wannan
yunkuri na Abdulkadir Dandatti ya tabbatar da cewa shaharar
da Alhaji Mamman Shata yayi, ba a Nijeriya kawai ta tsaya ba
harma da wadansu manyan kasashen duniya.
Cikakken sunan Shata shine Muhammadu. Sunan Mamman lakani ne
irin wanda kakanni kan radawa jikokinsu tun suna yara. Ita kuwa
kalmar "Shata". lakani ne wanda ake kiransa da shi
lokacin da yak-e cinikin goro. Baba Magaji Salamu Musawa, wanda
a lokacin shine ubangidan Alhaji Mamman shata, shi ya rada masa
sunan "Shata". A lokacin da Alhaji Mamman shata ke
saida goro, ba'a san wata aba wai ita bakar goro ba, goron kawai
ake sayarwa hamsin-hamsin, kuma a kan saida guda-guda. Cinikin
baka na kasa goro ana sayarwa da guda-guda ai sai kananan 'yan
goro, inji Alhaji Mamman shata. A wancan lokacin da Alhaji Mamman
shata ke saida goro baya kirgawa, sai dai ya kwasa ya baiwa
mai saye dai-dai kudinsa, shi yasa ake ce masa -shata- wato
mai saida goro babu kidayawa sai ya shata ya bayar. Kalmar shata
nada wata ma'ana daban kamar ace a shata fill, amma wadda ake
amfani da ita wajen sunan Alhaji mamman shata ita ce ta diban
abu a bayar kamar ba'a so.
Kafin zuwan turawa kasar Hausa, al'ummar Hausawa na da addininsu
na Musulunci, akwai kuma kadan dake bin addinin gargajiya da
ake kiransu Maguzawa. Ba'a san hikimar rubuta sunayen yara da
shekarunsu a ajiye don tarihi ba kamar yadda yanzu ake yi. Wannan
shi yasa ba'a san cikakkiyar shekarar da za'a ce an haifi Alhaji
Mamman shata ba.Amma a shekarar da ya kai ziyara gidan rediyon
Amirka cikin 1989, yace shekarunsa 65 a wancan lokaci, an kuma
yi hassashen cewar an haife shi cikin 1926.
|
|