Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Tarishin Kasar Gumel 


 

Kamar yadda aka sani dai, ba kasafai kawai mutane ke tattare kwan su da kwarkwatarsu su tasamma hanya haka kwatsam kawai domin kwadayin balaguro ko kuwa kwadayin wata fadar ba. Akwai dalilai masu dama da suka sa Mangawa na farko, yawan kaurace kauracen nan. Irin dalilan sun hada da neman guri mafi amfanin gona, guje ma fadace-fadace, yake-yake, rashin jituwa tsakanin hakimai, da manyan gari da sarakuna. Bugu da kari, akwai kuma wasu dalilai da suka hada da rashin jituwa da masu masauki, watau famar matsantawa daga yake-yake da Mai (sarkin) Borno wanda shine ya zama dalilin hijira da kuma hangen samun bunkasarshiyar filin noma domin samun amfanin gona da kuma makamantansu.

Masana tarishi sun yi imani da cewar a wannan lokacinne aka kirkiro, wannan gagarumar fadar ta Tumbi, wadda a cikinta ne aka soma amfani da tsarin mulki, wadda kuwa, har yau, da irinsa ake mulkin. Banda haka kuma, a wannan zamanin ne hukumar Tumbi ta sami askarawan tsaro masu kwazon gaske, da har ta zama abin alfahari. Wasu daga cikin gagararrun askarawan zamanin wanda suka cancanci a ambacesu sun hada da danjuma na Farko, Adamu Karro, Muhammadu mai kota, da dan Auwa, wadanda sune suka jagoranci nasarar kwatan yancin kai daga hannun hukumomin da ke mulki a kasar Borno.

Masu Magana dai sun ce, “taho mu zauna, shike zama taho mu sa$a”. Tarihi kuma ya nuna cewa an sami rashin jituwa ainun tsakanin wadannan fadodin guda biyu, musamman ma da yake haryau ana zargin Mai (Sarki) Borno da laifin kashe daya daga cikin jaruman Gumel, watau mai suna dan Auwa a Nguru a 1828, a yayinda shi dan Auwan ya guji bada nasa toshin (kyautar sarki) da aka sabunci baiwa masu sarauta.

Rashin bada wannan kyatar sarki da dan Auwa yaki, yasa Mai (sarkin) Borno da Damagaram suka farmasu da hare-haren yaki lokacin da suke Nguru, har kusan 1830-1840 wanda ya kawo sanadin da masu garin Gumel suka ga cewa idan ba sun guje wa wannan zangon ba, su da samun kwanciyar hankali zai yi wuya. Wannan itace basirar tashinsu daga kusa da Borno suka yada zango a garin da ya zame musu babban birni, watau garin Gumel, an kafa garin Gumel a shekara ta 1845. Koda yake sabuwar birnin fadar Gumel ta fada cikin zangon Sokoto ne, masarautar Gumel basu bada hadin kai ga sarakunan Sokoto ba, sai suka ci gaba da hada kansu da sarakonan Borno, har ya zuwan bayyan turawa a yankin. A takaice dai watau su Mangawa mutane ne masu wata shahararran tarihin kaurace-kaurace mai ban sha’awa, kuma mai yawan al’ajibi.

Kafin Mangawa su yada zango a Gumel, yankin gandun daji ne kawai, wanda bashi da iyaka, a lokacin banda filani masu kiwo babu wani wanda ya ta$a tunanin kafa wane gari ko kuma wata irin nuna sha’awar yin haka din a gandun dajin da yau ya zama babban birnin larden Gumel na yanzu.

Masana labari sun hakikance sarkin garin Tumbi na takwas watau Mai Muhammadu dan Tanoma na gidan Muhammadu Maikota ne ya kafa garin Lautai watau Gumel. Hakika, kashe Dan Auwa da kuma yawan halaka jama’a da dukiyar da aka tabka wa kasar Gumel a zamanin da suka kara da Shehun Borno ya ciwa mutanen Gumel tuwo a kwarya ainun, har ya kuma rage musu karfin shaharan da aka san su da shi wajen yaki. Wannan ya gurguntar askarawan Gumel baki daya. Ana kuma zaton cewa wannan shi yasa Sarkin Damagum Sarki Ibrahim ya raina Gumel ya dinga kai musu hare-hare akai-akai domin neman ya mallakesu baki daya.

Babu shakka wannan hare-haren da kuma wata sammaci da Shehu Laminu ya masa a 1830 ne, suka sanyo dalilan gudon Muhammada Mai dan Tanoma ya dinga yi har sai daya yada zango a garin Gumel na yanzu a 1837.

Banda kuma irin hare-haren da aka yi ta kai wa Gumel, kwadayin samun yancin kai daga karkashin hukumomin Damagun, da kuma Borno, suna cikin dalilanda suka sa Mai Dan Tanoma ya nemi shawarar wani bokansa wanda ake zaton cewa shi ne ya basu sa’a ta kauracewarsu zuwa wannan garin na yanzu da ake kira Gumel. Masana tarishi sun ambata a cikin tarihin Gumel cewa shi wannan mai tabaron hangen nesan ( Malamin Sarki) ya zana ayoyin al kur’ani ya baiwa wata saniya ta hadiya sa’annan yace a dinga bin ta sai inda ta tsaya taye fitsaren wannan rubutun sai su yada zango ya zame musu nasu sabon mazaune (garin).

Tarishe ya sanaddamu cewa saniyarce ta kada ta yi yamma kuma wasu shaharrarun mallamai kalilan suka dinga binta a baya, wannan saniyar takan tsaya a kowane tabki kokuma gulbe tadan sha ruwa ta ci gaba, sai da ta iso wannan jejin sai ta tsugunna a unguwar zuwo tayi fitsaren rubutun, da ganin haka sai wanda suke biye da ita suka ce Lau-ta-yi wanda ya sa aka rada wa garin suna Lautayi da farko, kamin a sake sunan zuwa Gulbe, wanda kuwa shine sunan saniyar. Ita kuma saniyar ta sami sunanta ne daga irin halinta na shan ruwa daga kowane gulben da ta samu a kan hanyarta a lokacin da ake biye da ita.

A wata siga dabam kuma da ke fadin cewa garin Gumel ya faru ne a yayinda tafiye-tafiyen Mangawa a karkashin jagorancin Muhammadu kanin Mai sarkin Ngazargamu, wanda shine sarki na goma sha shidda. Wannan sigar kuwa tana fadin cewa an sami rashin jituwa kan wata dukiya da ta shafi biyan kudin wani doki wanda shi sarki Muhammadu ya guji hukuncin da ya kamata a masa. Tare da jama’arsa baki daya, Muhammadu ya dauki dukiyarsa, da iyalansa, dakuma kannuwansa guda biyu. Suka kama hanya da manufar zuwa garin Ligalu a kasar Nijar, mai nisan kimanin mil dare biyu daga Gumel. Kafin su sami dacacciyar mafaka. Wannan kwambar kuwa sun yi ta tsaye-tsaye a garuruwa da dama da suka hada da birnin Shadika, Babaye, da kuma Dogama inda suka sami karin tarago har ma ya kai da cewa shi sarki Muhammadu ya dauki matakin nada shugaba a cikinsu. Nan ne wani kanin sarkin mai suna Adamu na Tsohon Birni ya sami daukaka, aka nada shi sarki, wanda ya zamanto mukaminsa na tsawon shekaru talatin (1719-1749), ko da shike muna iya tuna cewa Muhammadu mai kota ne yayi sarauta daga 1777 zuwa 1804, a yayin da ya zama sarkin farko da Mai Borno ya nada a yadda tarihi ya nuna. Kuma dama shine ya yi sarautar Tumbi tun asali, wannan shiyasa har kwanan gobe akwai zumunci da ma’amala tsakanin jama’ar Tumbi da kuma mutanen Gumel.

Bugu da kari kuma, kafin nasara (Yan mulkin mallaka) su raba iyaka tsakanin kasar Nijar da Nijeriya a watan june 1898, duka gundumomin da ke kimanin mil ishirin daga garin Gumel, na biyan diyarsu (haraji) ga masu sarautar Gumel a wancan zamanin. Kazalika kuma, har ila yau, mazauna garuruwa da dama a cikin Nijar wadanda suka hada da Maloua, Dingas, More da Damagum suna ci gaba da ma’amala da jama’an Gumel, ta fannin ziyarce-ziyarce a lokacin bukukuwa da kuma makamanninsu.

Tarihi dai ya nuna cewa Muhammadu Mai Tumbi, sarkin Gumel na takwas, ne ya kafa garin Gumel domin irin kwazon da ya nuna a lokacin da yake sarauta. Mai Tunbi yayi shekaru tara a Tumbi kafin ya zo ya yi shidda a Gumel, a cikin garin Gumel na yanzu ya rubuta wasikar murabus zuwa ga Shehun Borno a shekarar ta 1843, inda ya ambaci cewa shi dai ya manyanta kuma yana neman izini ya sauka daga karagar mulki. Nan ne ya mika wa dansa, watau Cheri karagar mulki.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.