Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Tarishin Ya'Ke Ya'Ken Gumel 


 

Tarishi dai yanuna cewa babu wane dalili da ke jawo yawan 'kaurace-'kaurace kamar ya'ke-ya'ke, Mutanin Gumel (Mangawa) sunyi fama da ya'ke-ya'ken tsaron gida, tundaga inda suka fara kaura daga Ngazargamu, yazuwa inda aka kafa garin Gumel na yanzu. Ya'ke-ya'ke ke sawa idan jama'ar wata gundumar suka ga alamar cewa za'a mamayesu, sai su kauracewa guri. Jama'ar Gumel sun tabka ire-iren waddannan fa'dace-fa'dacen, da dama kafin su kafa garin Gumel, da kuma bayan sun kafa zango a Gumel. Gumel tana daya daga cikin garuruwan da basu nuna amincewarsu da mulkin Hausa-Borno, ko na Sokoto ba, ko da shike Barno ta mallaki Gumel da farko, mulkin Borno bai taka kara ya karya ba, domin masarautar Gumel ta balle daga 'kar'kashin Borno ta yi tsayuwarta ta kanta a 1837.

Tarihin yake-yaken Gumel ya faro ne tun daga karni na goma sha takwas, zamanin sarki Kalgo (1804-1811) wanda ya dinga kare garin Gumel, daga hannun mayakan Kano da kuma Machina har sai lokacinda wani bawan sarkin Machina ya sami fili ya soke shi da makami ya masa raunin da ya karasa shi har lahira.

Saboda kwadayin samun fa'Da'Da 'Kasa, da 'Yancin kai, wanda jama'ar Gumel suka fara nunawa tun fil azal, yasa sun kutsa kai wanjen ya'Ke wanda ake kira da "karo daya tsakanin kyai da dutse", suka fara yakar garuruwa wanda har ya sa ratar mil tamanin ne kawai ya raba su da shiga cikin garin Kano.

A wani fage da Gumel ta taimakawa Kano za a iya samun karin haske irin kwazon jaruman Gumel a ya'ke-ya'ken da suka goyi bayan kungiyar Yusuf a tsakaninsu da askarawan Tukur na yakin (1893-1895).

Wata yar gajeruwar jawabi da Gwadabe ya zayyana, ta ambaci irin kwarewa, jarunta, da kuma tsarin askarawan Mangawa, tun lokacin da suka soma fa'Dace-fa'Dacen su a mazaunin su na farko a Dogoma. A cikin wannan jawabin Gwadabe ya kwatanta irin shirin Mangawa da na askarawan Shehun Borno, inda shi shugaban askarawan ke bada umurni, kuma yake tafiyadda fasalin hare-haren askarawan sa baki 'Daya. Da farko Shiga cikin mayakan Mangawa an takaita shi tsakanin yan sarauta kawai, ko da shike irin wannan daukar na saukaka samun maya'ka, yana kuma toshe armashin samun kwararrun askarawa. Bisa wata yar tarzoma a shekara ta 1852 Mai Muhammadu Cheri ya fa'da'da daukar askarawa, ya bu'Da kofar dauka ga duk mai niyyar shiga, ya kuma sau'ka'ka wa wasu kwararrun maya'ka ko da basu da jinin sarauta zasu iya shiga kwamban askarawan.

A zamanin sarki Dan Auwa (1811-1828). Gumel ta yi nasara a yake-yake da makwabtanta da dama. A wani farmaki da yakai wa Hadejia, ya sami galabar kutsawa har yazuwa garin Kaugama, da Turmi. Daganan ya hada kai da sarkin Kano Dabo wanda yin hakan ya kasance masa alheri. A wani harin ba zato ba tsammani da yakaiwa Ringim, saboda karfin kariya daga mayakan Ringim, harin ya fi karfin Dan Auwa, sai ya janye maya'kansa suka koma garin Matoya can wajejen arewa maso gabacin garin Sule Tankarkar. Bayan wata yar gajeruwar hutu sai suka fusata suka kutsa har saida suka kore mayakan Kano din domin irin lahani da raunuka da suka ji musu. Bayan mutuwar Dan Auwa, ba a yi wani babban ya'ki ba, sai dai wasu yan tashe-tashen hankali da aka samu tsakanin Gumel da garuruwan Zinder da kuma Hadejia da kuma Kano, wanda bayan sune hadejia a sheka ta 1872 ta sami cin galaba kan mayakan Gumel din a Zaburam. A wannan harin ne aka kasha Sarkin Gumel Abdullahi, abinda ya kawo sanadin karshen ya'ke-ya'ke tsakanin Gumel da Hadejia wadda ya'ki ci ya'ki cinyewa, har wajen misalin shekaru hamsin.

Banda haka kuma, Gumel ta sha wuya a hanun makwabtanta daga arewa musamman ma daga hannun sarki Ibrahim na Damagaram. Can daga baya dai ta wajejen 1872-1896 mayakan Damagaram din suka dinga cin zalin mayakan Gumel din akai-akai wanda kuma shine sanadin raguwan yawan al'uman Gumel. Bugu da kari kuma, yayin da sarki Rabeh ya dinga matsawa Gumel shi ne ya sa sarki Ahmadau na Gumel wanda ya yi sarauta tsakanin 1896-1915 ya damu har ya je ya nemi mafaka da tsaro a hannun Lord Lugard a 1903 wanda bayansa ne al'umarsa suka dinga dawowa gida domin ci gaba da fatauci da kuma rayuwarsu cikin lumana.


 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.