Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Bakandamiyar Alhaji Mamman Shata  




 

Alhaji Mamman shata yayi wakarsa ta Bakandamiya har sau biyu. Ta farko ce wadda yayi lokacinda Alhaji Adamu Salihu yayi hira da shi a gidan Rediyo-Telbijin na Kaduna. Ta biyun ita ce wadda aka dauka a faifan garmaho. An had duka wakokin biyu cikin wannan littfafi, sai dai a wakarsa ta biyu an rage was baitoci.

Alo-alo Mai ganga ya gode.
yaran mai ganga sun gode.
Kai mutane kowa yake addini,
kun san baya kamar manzon Allah.
Kowa ka gani na sabon Allah,
ko wanene ke kafirci, kun san
babu kamar Fir'auna. To ashe haka
duk wanda ke yin waka, yara bai
yi kamar shata ba.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Idan kuma kayi musu sanya
mugani, kodagainaayi wakar.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
yaran mai ganga sun gode.
Abinda yasa haji Mamman shata
yake tausayin marokan birni,
yake tausan ku marokan kauye
yaki na karewa, ya kuke kera
makamai tima-tima?
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Ga kuma hauka ya kare, 'yan uwanmu
sun fada dawa saran turu.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Allah ya Allah don Allah,
ya Ahadun don girman Zati, Allah ya yarda.
Gwauron giwa mai ban tsoro na Habu dan Ibrahim,
kyarkyece mai wawar kora dan yaro.
Zaki mai ta'adin karfi dan Iro.
kowa ya san kowa Katsinawan Dikko
ku da Kanawan Dabo, da mutanen Zazzau.
Hada da Jasawa namu, Filanin Yola.
Shata tafi Gwambe kai ne, balle Bauchin Yakubu
Mamman shiga Barno ni ne, sun san ni
Shata ne, sai kaka?
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Idan na fara Bakandamiya ji nake
kamar Malami gwanin tamsiri amma,
Malami gwanin aja baki ya fasa
ba tare da jin tsoro ba.
Don ba'a gwaninta da tsoro Malam
mai tsoro bashi gwaninta ko wanene,
kuma ko dan wa- Allah kau
ko wanene, to-to-to. Alo-alo mai
ganga ya gode yaran mai
ganga sun gode.
Matsoraci bashi zama gwani ko wanene
ka zama kamar ni filin waka,
sararin waka ban tsoro ba in na
fito
Shata ne- kun san shi, ya san ku
sai kaka? Yeh!
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Gurnanin Damisa karen gida ke gudu
karen ko na wanene dan kusun uwa,
wane aura. To-to-to.
Alo-alo mai ganga ya gode
aran mai ganga sun gode.
Allah ya yarda har yau ni keyi
kuko baku samo chanjina ba,
balle in zauna wai har ince zan huta
ku taya mani ku 'ya'yana.
Har yau dai ni keyi Allah ya yarda.
Yardar Allah ta fi ta kovva na Habu
dan Ibrahim-kyarkece mai wawar
kora dan yaro, to-to-to.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Naje Kazaure naje Daura sannan
na gangara hanya in gaida Jambo.
Shehu kunu sai yada.
Alo-alo mai ganga ya gode
Yaron mai ganga sun gode,
Mai tumaki mai Jakai kanon dabo birni
mai mata mai mota, birnin gari mai Dala
da Gwauron dutse, Kanon Dabo birni.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Allah ya yarda har yau ni keyi
kuko baku samo chanjina ba,
balle in zauna wai har ince zan huta
in dai samu in saurara,
ku rika mu gani ‘ya’yana
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.
Kowa yayi gida nai birni in dai
aka ce birni ya zauna,
rannan aka ce ya koma kauye
yayi gida ya zauna-zaman duniya
zaman duniya tasa ya dai-dai ta,
fadawa mutane na kowa ya rasa Shata
yayi asarar waka, kowa ya rasa ni bai-sha
waka ba ko wanene ko dan wa, Allah kau.
Alo-alo mai ganga ya gode
yaran mai ganga sun gode.

 

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka mhashim@gumel.com

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.