|
RAYUWAR ALHAJI
MAMMAN SHATA
Alhaji Dr. Mamman shata Katsina a halm da ake ciki yanzu
ya zamewa makada da mawakan Hausa Dutse baka daukuwa saida
gammo, mutsu-mutsu gobe jar kasa, ruwan dare mai gama duniya,
ya buga da mazajen farko gashi yana bugawa da mazajen yanzu.
Abinda marokinsa ke fada ke nan kafm ya fara wakarsa ta Bakandamiya.
Babu wata kasa a duniya da zata bugi kirji ita kadai tace
ta sami ci gaba a rana guda. Su kansu kasashen da suka ci
gaba irin su Amirka, Tarayyar Soviet, China, Birtaniya da
Japan da Jamus sun yi amfani ne da kyawawan al'adunsu wajen
gina tushen ci gaban da suka samu. Mawaka da makadan wadannan
kasashe da suka ci gaba sun bada gudummawa mai yawan gaske
ta fuskar irin tasu fasahar wajen ciyar da kasashen nasu gaba.
Farfesa Dandatti Abdulkadir, kafm ya zama shugabanjami'ar
Bayero dake Kano a Nijeriya, ya rubuta makalarsa ne kan rayuwa
da wakokin Alhaji Mamman shata sannan ya gabatar wa shaihunan
Malaman Amirka don su tabbatar masa da samun digirinsa na
uku (Ph. D). Wannan yunkuri na Abdulkadir Dandatti ya tabbatar
da cewa shaharar da Alhaji Mamman Shata yayi, ba a Nijeriya
kawai ta tsaya ba harma da wadansu manyan kasashen duniya.
Cikakken sunan Shata shine Muhammadu. Sunan Mamman lakani
ne irin wanda kakanni kan radawa jikokinsu tun suna yara.
Ita kuwa kalmar "Shata". lakani ne wanda ake kiransa
da shi lokacin da yak-e cinikin goro. Baba Magaji Salamu Musawa,
wanda a lokacin shine ubangidan Alhaji Mamman shata, shi ya
rada masa sunan "Shata". A lokacin da Alhaji Mamman
shata ke saida goro, ba'a san wata aba wai ita bakar goro
ba, goron kawai ake sayarwa hamsin-hamsin, kuma a kan saida
guda-guda. Cinikin baka na kasa goro ana sayarwa da guda-guda
ai sai kananan 'yan goro* inji Alhaji Mamman shata. A wancan
lokacin da Alhaji Mamman shata ke saida goro baya kirgawa,
sai dai ya kwasa ya baiwa mai saye dai-dai kudinsa, shi yasa
ake ce masa -shata- wato mai saida goro babu ce a shata fill,
amma wadda ake amfani da ita wajen sunan Alhaji mamman hata
ita ce ta diban abu a bayar kamar ba'a so.
Kafin zuwan turawa kasar Hausa, al'ummar Hausawa na da addininsu
na lusulunci, akwai kuma kadan dake bin addinin gargajiya
da ake kiransu laguzawa. Ba'a san hikimar rubuta sunayen yara
da shekarunsu a ajiye don arihi ba kamar yadda yanzu ake yi.
Wannan shi yasa ba'a san cikakkiyar hekarar da za'a ce an
haifi Alhaji Mamman shata ba.Amma a shekarar da ya kai iyara
gidan rediyon Amirka cikin 1989, yace shekarunsa 65 a wancan
lokaci, an uma yi hassashen cewar an haife shi cikin 1926.
|
|